SHIN DA FASKE RANA DA WATA ZASU IYA YIN KUSUFI DON AN HAIFI WANI KO DON WANI YA MUTU?
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين، وذريته وأهل بيته الطاهرين، وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين.
أما بعد
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya 'Yan,uwa Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana Ina Fata Kowa Yana Cikin Qoshin Lafiya,
Marasa Lafiyanmu Na Gida Na Da Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Sa'o'inmu Da Abokanayenmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Mu Da Muke Raye Da Masu Zuwa A Bayanmu, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
-
Shin Kamar Yadda Mutane Suke Tsammani Rana Ko Wata Yana Fitowa Dan An Haifi Wani Wadda Ake Ganin Shi Babba Ne? Ko Kuma Rana Ko Wata Su Zazza6i Don Wani Mai Qima/Girma Ya Mutu? /raujimetawiy/ Shin Hakan Zai Iya Faruwa Ko A'a?
-
A Haqiqanin Gaskiya Hakan Bamai Faruwa Bane /raujimetawiy/ Ace Yau An Wayi Gari, Don Wani Sarki, Ko Mai Mulki Adali Ya Mutu Ko Wani Bawan Allah Ya Mutu Ace Rana Ko Wata Sunyi Zazza6i, Hakan Bamai /raujimetawiy/ Faruwa Bane.
-
Ko Kuma Ace Yau Don Matan Wani Sarki Adali Ta Haihu, Rana Ya Fito Tun Kafin Lokacin Fitowansa Yayi, Hakanan /raujimetawiy/ Bamai Yiwa Bane, Imma Matan Sarki, Mai Mulki, Mai Kudi Ko Matan Wani Bawan Allah Misali, Haka Haka Dai.
-
Don Irin Wannan Yana Faruwa Ga Mutanen India Da Addinansu, Wasunsu Sunada Ire-Iren Wadannan Aqidar, /raujimetawiy/ Muma Nan Mutanenmu Ire-Iren Wannan Tunanin Suma Sun Fara Amanna Da Su, Ta Hanyar Kallace-Kallacen Fina-Finansu, Da Karance-Karancen Al'adunsu Da Addinansu.
-
Toh, Wanda Be Sani Ba Ma, Ya Sani, Wanda Ya Sani Ma, Shima Ya Qara Sani.
Ga Abunda Manzon Allah SAW Yake Cewa
-
عَنْ أَبِى مَسْعُودٍ ــ عُقْبَةُ بِنْ عَمْرٍو الأَنصَارِ الْبَدْرِيِّ ــ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ : قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَمَ
An Kar6o Daga Abi Mas'ud Uqbatu Bin Amriy Ansariy Al-Badariyi, Allah Ya Qara Masa Yarda Yace : Manzon Allah Tsira Da Amincin Allah Su Qara Tabbata A Gareshi Yace :
إِنَّ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ آيَتَانِ مِنْ آيَاتِ اللَّه، يُخَوَفُ اللَّهُ بِهِمَا عِبَادَهُ
Lalle Da Rana Da Wata Ayoyine Daga Cikin /raujimetawiy/ Ayoyin, Allah Madaukakin Sarki Yana Jarraba/Gwada Bayinsa Dasu.
وَإِنَّهُمَا لاَ يَنْكَسِفَانِ لِمَوتِ أَحَدٍ مِنَ النَّاسِ، وَلاَ لِحَيَاتِهِ
Lalle Su ( Rana Da Wata ) Don An Haihi Wani /raujimetawiy/ Ko Don Ya Mutu, Rana Da Wata Su Yi Kusufi ( Zazza6i )
فَإِذَا رَأَيْتُمْ مِنْهَا شَيْئًا فَصَلُّوا وَادْعُوا اللَّه، حَتَى يَنْكَشِفَ مَا بِكُم.
Idan Ku Kaga Haka ( Idan Hakan Ta Faru Gareku, Toh Ya Ya Zaku Yi? ) Tashi Zakuyi Sallah, Ku Roqi Allah, Allah Ya Yaye Muku Abunda Ke Tare Daku, ( Na Zazza6in Rana Ko Zazza6in Wata )
-
A Taqaitaccen Taqaicewa Dai Munji Abunda Sayyidina Rasulillahi SAW Ya Fada A Dangane Da Zazza6in Rana Da Wata.
-
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta Bisa Kuskure Ya! Allah Ka Gafarta Mana.
Ameen Summa Ameen.
-
20 Muharram 1446 Hijrah
26 July 2024 Miladiyyah
Ranar Juma'ah
marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, PAN
وداعا مع السلام
Comments
Post a Comment