004 HUKUNCIN MUSULUNCI DANGANE DA MATA A SIYASA DA GWAMNATI

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
  -
A Gurguje
Insha Allahu Kamar Yadda Muka A Kashi Na Uku Muka Ce Zamu Tashi A
page 013
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
وَعَدٔتْتَنَا عَلَى رُسُلِكَ وَلاَ تُخْزِنَا ؤَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّكَ لاَ تُخْلِفُ الْمِيعَادَ ( ٱل عمران : ١٩٤ )
'Ya Ubangijinmu Allah (SWT) Haqiqa Lallai Munji Wata Qiran Mai Qiranmu Zuwa Ga Bautanka Wanda Ke Cewa Muyi Imani Da Ubangijinku Allah (SWT) Zai Gafarta Mana Zunubanmu Ya Kuma Shafe /raujimetawiy/ Mana Kura-Kuranmu Sa'annan Ya 'Daukaka Matsayinmu, Sai Mukayi, Saboda Haka Ya! Allah (SWT) Ka /raujimetawiy/ Cika Mana Wannan Alqawari Da Kayi Mana Ta Hanyar Manzanninka, Sa'annan Ka Tseratadda Mu Daga Kunyar Ranar Hisabi, Domin Kai Allah (SWT) Baka Saba Alqawari. '


Nan Take Kuma Allah (SWT) Mai Girma Da 'Daukaka Ya Tabbatar Da Cewa Ya Amshi Wannan Adu'ah Tasu Baki 'Daya Kamar Yadda Ya Fada A Aya Ta Gaba 
Cewa :-
1 - فَاسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّي لاَ أُضِيعُ عَمَلَ عَامِلٍ مِنْكُمْ مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنْثَــى بَعْضِكُمْ مِنْ بَعْضٍ [ آل عمران : ١٩٥ ].
-
page 013
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
" Sai Ubangijinsu Ya Amsa Wannan Du'ai Nasu Ya Kuma Biya Musu Buqatunsu, Allah (SWT) Yace Bazai Ta6a Yin Watsi Da Wani Kyakkyawan Aikin Wani Daga Cikin Bayinsa Ba, Kamar Yadda /raujimetawiy/ Muka Kasance 'Yan,uwan Juna ( Sura Al-Imran Aya Ta 195 )

A Taqaice Abin Da Muke Fadi Anan Shine Aya Ta Farko Da Muka Ambata Ta Suratul Nisa'i Tana Bayyana Qarara Cewa Shugabancin Gida Da Kuma Iyali Ake Nufi Anan, Inda Allah Ya 'Daurawa Maza Alhaqin Kula Da Kuma Kaariyar 'Yan,uwansu Mata /raujimetawiy/ Daya Shafi Ciyarwa Dama Dukkan Wasu Taimakon Da Matan Nasu Dama Sauran Iyali Baki 'Daya Zasu Buqata.
Saboda Haka Wannan Ayar Bata Nufin Haramta Riqe Wani Muqami Ko Wani Matsayi Ga Mace.
Wadannan Ayoyi Da Muka Karanto Suna Dai-Daita Maza Da Maza A Wurare Da Dama, Kamar Yadda Allah Mai Girma Da 'Daukaka Ya Fadi Duk Kuwa Da Banbanci Jinsi Dake Tsakaninsu.

-
page 015
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Yanzu Kuwa Zamu Karkata Ga Wannan Hadisin Da Ake Yawaita Amfani Dashi A Matsayin Hujjar Dake Haramta Shigar Mace Harkar Siyasa Ko Kuwa Riqe Wasu Muqamai A Gwamnati Domin Fahimtar Sahihan /raujimetawiy/ Abinda Hadisin Yake Nufi Dalla-Dalla.

Abi Bakrata (RTA) Yace A Lokacin Da Labarin Rasuwar /raujimetawiy/ Sarki (Persia) Ya Riski Manzon Allah (SAW) Sai Annabi Muhammadu (SAW) Yayi Tambaya Gameda Wanda Zai Gajeshi, Sai Aka Shaidawa Annabi Muhammadu (SAW) Cewa Ai 'Yarsa Mai Suna Bouran Ta Gajeshi, Sai Annabi Muhammadu (SAW) Yace :-
لن يفلح قوم ولوا أمرهم إمراة
Dukkan Wata Al'ummar Da Mace Ta Shugabanceta Bazata Ta6a Samun Nasara Ba ".
-
page 016
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Kafin Mu Fadi Matsayinmu Kan Wannan Hadisin, Ya Kamata Mu Dubi Fahimtar Wasu Malamai Magabata Wadanda Ke Ganin Cewa Ma Hadisin Ba Sahihi Bane /raujimetawiy/ ( Bai Inganta Ba, ) Wadannan Malamai Kuwa Na Ganin Cewa Shi Abi Bakrata (RTA) Ya Rawaito Hadisin Ne Bayan Da Sayyida Aishatu (RTA) Ta Jagoranci Yaqin Raquma ( Jamal ) Inda Akayi Galaba Akan Sojojinta.

Wadannan Malamai Dake Inkarin Wannan Hadisin Sunyi Jayayyar Cewa Me Yasa Shi Abi Bakrata (RTA) Bai Rawaito Hadisin Ba, Sai Bayan Shekaru Ashirin Da Biyar 25Yrs, Bayan Da Ya Jiwo Hadisin Daga Annabi Muhammadu (SAW) Da Kuma Gazawar Wadannan Sojoji Da Suka Halarci Yaqin Qarqashin Jagorancin Ita Sayyida Aisha (RTA) Saboda Haka Aganinsu Wannan Ba Wata Hujjace Mai Qarfi Da Zata Haramta Jagorancin Mace Ba, Sa'annan Sunyi Tambayar Cewa Me Yasa Shima Abi Bakrata Da Kansa Ya Kasance Daga Cikin Sojojin Dake Qarqashin Wannan Mata ( NANA AISHA RTA ) Sa"annan Me
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Masha Allah, Alhamdulillahi
Duka-Duka Anan Zan Tsaya Bi'iznillahi Ta'alah, Saboda Kar In Tsawaita Rubutu.
Insha Allahu Kuma A Kashi Na Biyar Zamu Tashi A  
" Yasashi Kuma Bai Bar Rundunar Yaqin Dake " page 017
.
06 Rabi'ul Awwal 1446 HIJRA
09 September 2024 MILADIYYAH
Ranar Litinin
 -
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy
BPM PAN PH


Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI