005 HUKUNCIN MUSULUNCI DANGANE DA MATA A SIYASA DA GWAMNATI
kashi na biyar
HUKUNCIN MUSULUNCI DANGANE DA MATA A SIYASA DA GWAMNATI
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
In Bamu Manta Ba, A Kashi Na Hudu, Munce Insha Allahu Zamu A
page 017
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Yasashi Kuma Bai Bar Rundunar Yaqin Dake Qarqashin Matar Ba, Bayan Daya Fahimci Wannan Hadisin? Wannan Na Na Nufin Cewa Akwai Wani Abin Dubawa Na Fahimtar Saqo Da Kuma Idawa Gameda Wannan Hadisin Bisa Fahimtar Wasu Malaman.
Kamar Haka:-
1 - BUKHARI Ya Rawaito Wani Hadisi Cikin Littafinsa Inda Yake Cewa Muhammad Ibnu Almusanna Ya Rawaito Mana Cewa /raujimetawiy/ Khaled Ibnu Al-Harss Ya Rawaito Mana Cewa : Himed Attaweel Ta Bakin Al-hassan Ya Sanar Mana Cewa Abi Bakrata Yace : Manzon Allah (SAW) Yace:-
لن يفلح قوم ولوا أمرهم إمرأة.
2 - ABU ISA AT-TIRMIZI Ya Rawaito Mana Kamar Yadda Bayanin Sama Ya Gabata Da Kuma Qari Cewa Wannan Hadisin Hassan Ne Kuma Sahihi Ne ( Ingantaccen Hadisi Ne )
-
page 018
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
3 - IMAM NISA'I Ya Rawaito Cewa Kamar Yadda /raujimetawiy/ Bayanai Biyu Na Sama Suka Gabata Gameda Wannan Hadisin.
4 - IMAM AHMAD Ya Rawaito Wannan Hadisin Cikin Littafinsa Zawa'id Almusnad Cewa Abdullahi Yace Mahaifina Ya Sanar Dani Cewa Yahya Ta Bakin Auyaiyna Yace Mahaifina Ya Shaida Mini Cewa Abi Bakrata Ya Rawaito Cewa Manzon Allah (SAW) Yace:-
لن يفلح قوم أسندوا أمرهم إلى إمرأة.
5 - ABDULLAHI Ya Shaida Mana Cewa Mahaifinsa Ya Sanar Masa Cewa ASWAD 'DAN AMER Ya Shaida Mana Cewa HAMMAD 'DAN SALAMA Ta Bakin HIMED Ya Rawaito Daga Al-hassan Ta Bakin Abi Bakrata /raujimetawiy/ Cewa Manzon Allah (SAW) Yace :-
لا يفلح قوم تملكهم إمرأة.
-
page 019
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
6 - ABDULLAHI Ya Shaida Mana Cewa Mahaifinsa Ya Sanar Cewa Muhammad 'Dan Bakr Ya Shaida /raujimetawiy/ Masa Cewa Auyaina Ta Bakin Mahaifinsa Yace Abi Bakrata Yace Yaji Daga Manzon Allah (SAW) Yana Cewa :-
لن يفلح قوم أسندوا أمرهم إلى إمرأة
7 - ABDULLAHI Ya Sanar Mana Cewa Mahaifinsa Ya Sanar Dashi Cewa, Yazid Dan Harun Auyaina Ta Bakin Mahaifinsa Yace Abi Bakrata Yace Manzon Allah (SAW) Yace :-
لن يفلح قوم أسندوا أمرهم إلى إمرأة
8 - ABDULLAHI Ya Sanar Mana Cewa Mahaifinsa Ya Shaida Musu Cewa Yazid 'Dan Harun Yace : Mubarak 'Dan Fudala Ta Bakin Abi Bakrata Yace Manzon Allah (SAW) Yace:-
-
page 020
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
لا يفلح قوم تملكهم إمرأة.
9 - Abu Bakrata Yace Manzon Allah (SAW) Yace:-
ما أفلح قوم يلي أمرهم إمرأة
A Namu Fahimtar Kuwa Munyi Ammannar Cewa Ko Tantama Babu Gameda /raujimetawiy/ Sahihancin Wannan Hadisin Kamar Yadda Ya Samu Ruwayar Dimbin Wadanda Ke Ruwaito Ingantattun Hadisai.
Saboda Haka Abu Mafi Muhimmanci Garemu Yanzu Shine Mu Zurfafa Nazari Akan /raujimetawiy/ Abinda Hadisin Ya Qunsa Da Kuma Gabatar Dashi A Aikace.
Da Farko Dai, Ya Kamata Mu Fahimci Cewa Wannan Hadisin Yana Magana Ne Akan Shugabanci Da Ake Qira Da Al-Imama Ko Al-Khilafah Ko Kuwa Kubra A Shari'ar Musulunci.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Masha Allah, Alhamdulillahi
Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Bi'iznillahi Ta'alah, Saboda Gudun Tsawaitawa.
Insha Allahu Kuma An Kashi Na Shida Zamu Tashi A " Wannan A Taqaice Yana Nufin Cewa Mai Girma "
-
Abunda Muka Rubuta/Fada Dai-dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Wanda Muka Rubuta/Fada Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana.
Ameen Summa Ameen.
-
Ubangiji Allah Ya Qarawa Maulanmu
Sheikh Dr. Shariff Ibrahim Saleh Al-hussain, CON Lafiya Da Nisan Kwana Da Qarin Tilin Ilimi Mai Albarka.
Ameen Summa Ameen.
-
10 Rabi'ul Awwal 1446 Hijrah
13 September 2024 Miladiyya
Ranar : Juma'ah
-
makwafi
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy
BPM PAN PHM
وداعا مع السلام
Comments
Post a Comment