007 HUKUNCIN MUSULUNCI DANGANE DA MATA A SIYASA DA GWAMNATI
kashi na bakwai
HUKUNCIN MUSULUNCI DANGANE DA MATA A SIYASA DA GWAMNATI
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
In Bamu Manta Ba, Munce Insha Allahu A Kashi Na Shida Zamu Yashi A
page 025
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Gaskiya Babu Wargi Cikinsa.
5 - Wajibi Ne Ya Kasance Mai Qoqari Hada Kan Jama'ah.
6 - Wajibi Ne Ya Kasance Mai Basira.
7 - Wajibi Ne Kuma Ya Kasance Mai Riqon Amanar Jama'ah.
Wannan Limamin Kuwa ( Imama ) Yana Barin Aiki Ne Kawai Idan Guda Daga Cikin Wadannan Sharudodi Da Shara'a Ta /raujimetawiy/ Amince Dasu Ya Faru Dashi Sune Kamar Haka:-
1 - Idan Ya Mutu.
2 - Idan Ya Samu Ta6in Hankali.
3 - Idan Ya Gamu Da Rashin Lafiya Mai Qarfin Gaske Ta Yadda Bazai Iya Gabatar Da Ayyukansa Ba.
4 - Ko Aka Sameshi Da Rashin Gaskiya Da Adalci Ga Ayyukansa.
5 - Ko Idan Ya Kaucewa Hanyar Shara'ah.
6 - Ko Idan Watsi /raujimetawiy/ Da Koyarwan Addini Ko Qa'idoji Da Makamantansu.
-
page 026
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Sai Babban Limamin Dake Na Sama Ya Nada Wani Da Zai Maye Gurbinsa Ko Kuwa Ya Tsaya A Madadinsa Idan Ta Kama /raujimetawiy/ Yayi Tafiya Mai 'Dan Dogon Zango Ta Yadda Zai Bar Ayyukansa Zuwa Wani 'Dan Lokaci.
A Taqaice Dai Abinda Ake Nufi Anan Shine, Irin Tsarin Shugabanci Na Wannan Jagora Imama Shine Irin Tsarin Shugabancin Manzon Tsira, Annabi Muhammadu S.A.W Dama Sauran Annabawan Allah /raujimetawiy/ S.W.T Baki 'Dayansu ( A.S ) Da Kuma Taimakon Khalifofi Da Suka Taimakon Musu. Haka Kuma Tsarin Shugabancin Sarakunan Da Suka Mulki Masarautar Sokoto Da Kuma Sarautar MAI Ta Jihar Borno Suka Kasance Baya, Kafin Samun 'Yanci Da Kuma Mulkin Kai.
Sai A Wannan Qarni Namu Kuma, Sai Muce Qasar Saudiyyah Ce Kadai Take Kwatanta Hakan A Wannan Duniya Yanzu.
Daga Qarshe Muna So Muyi Amfani Da Wannan Dama Domin Janyo Hankalin Jama'ah Cewa Wannan Fatawar
-
page 027
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Na Bayyana Cewa /raujimetawiy/ Wannan Aya Da Akayi Amfani Da Ita Ta Suratun Nisa'i Ko Shakka Babu Tana Magana Ne Akan Alaqa Da Kuma Dangatakar Dake Tsakanin Mace Da Mijinta.
Ayar Ta Kuma Bayyana Qarara Cewa Tana Magana Ne Akan Alaqar Iyali, Inda Aka 'Daura /raujimetawiy/ Alhaqin Kulawar Iyali Na Ciyarwa Da Kuma Bada Dukkan Sauran Taimako, Da Kuma Buqatun Da Matar Aure Dama Sauran Matan Gida Zasu Buqatun Akan Miji.
Saboda Haka Wannan Ayar Ba Magana Take Akan Shugabanci Ko Kuwa Jagoranci Ga 'Ya Mace Ba, Sauran Ayoyin Kuwa Da Muka Janyo /raujimetawiy/ Suna Nuna Dai-Daito Ne, Da Allah S.A.W Ya Bayyana Tsakanin Maza Da Mata Duk Kuwa Da Banbancin Jinsi Da Kuma Halitta Da Allah Yayi Tsakaninsu.
Sai Kuma Hadisin Da Sahabin Annabi ( S.A.W ) Abi Bakrata ( R.T.A ) Ya Ruwaito Wanda Ya Kasance Tushen Wannan Muqqadima Kan Wannan Batu, Wanda Kuwa /raujimetawiy/ Ya Kasance Jama'ah Da Dama Sukayi Masa
-
page 028
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Mummunar Fahimtar Daga Cikin Malaman Dama Wadanda Ke Ikirarin Malanta.
Dai-Dai Gwargwadon Fahimtar Mu Munyi /raujimetawiy/ Qoqarin Bayyana Cewa Wannan Hadisi Da Akayi Amfani Dashi A Wannan Muqqadima Yayi Mana Bayani Qarara Cewa Bashi Halatta Ga 'Diya Mace Data Kasance Jagora Ta Fuskar Shugabanci ( Khalifah ) Ga Dukkan Al'umma, Muqaminda Aka Gindaya Wadancan Sharudodi Da Kuma Qa'idojin Da Aka Jero A Baya.
Da Farko Dai, Irin Wannan Jagorancin Ko Kuwa Shugabanci Kuma Babushi Cikin Tsarin Mulkin Najeriya A Yau, Kasancewar Qasar Tana Amfani Ne Da Matakai Uku Na Gwamnati Da Suka Hada Da Majalisar Zattaswa Da Data Qunshi /raujimetawiy/ Shugaban Qasa Da Ministocinsa Da Kuma Sauran Manyan Jiga-Jigan Gwamnati A Matakin Tarayya Kenan.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Masha Allah Alhamdulillahi
Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Rubutun Kamar Yadda Muka Saba Shafi Bibbiyu,
Abunda Muka Rubuta Dai-dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Gafarta Mana.
Ameen Summa Ameen
Insha Allahu Kuma A Kashi Na Takwas Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa " Sai Kuma Gwamnoni Da Kwamishinoninsu A Matakin Jihohi "
-
24 Rabi'ul Awwal 1446 Hijira
27 September 2024 Miladiyyah
Ranar Juma'ah
-
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy
BPM PAN PHM
Comments
Post a Comment