JIHADI PART FOUR

kashi na 4

TAQAITTACCEN BAYANI AKAN JIHADI
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@ @@
Aslm
Ya ‘Yan,uwa Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qannana Ina Fata Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Allah Ka Basu Lafiya. Mamatanmu Da Suka Riqamu Gidan Gaskiya Allah Kaji Qansu Kayi Musu Rahma, In Tamu Tazo Allah Kasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Suma Ameen
.
Karmu Manta Dai Har Yanzu Muna Cikin Littafin Fiqhun Malikiyyah Matsakaici ( Shi Bama Mai Yawa Har Can Ba, Kuma Shi Ba Kadan Ba ) Wato Risala Na Abu Muhammad Abdullahi Bin Abi Zaideen Al-Qirawaniy Ubangiji Allah Ya Yi Masa rahma Ameen Summa Ameen, Yau Gashi /raujimetawiy/ Da Rasuwarsa Shekara Dubu Daya Da Hamsin Da Shida (1056) Gashi Har Yanzu Muna Amfana Daga Illomansu. Allah Ya Saka Musu Da Al-khairi.
.
A Gurguje In Bamu Manta Ba A Kashi Na 3 Mun Tsaya A
ولا يسهم لأجير إلا أن يقاتل
Yanzu Kuma Da Izinin Allah Zamu Dora/Tashi Akan Fadin Mallam Rahimahullahu Ta’alah
.
ومن أسلم من العدو على شيء فى يده من أموال المسلمين فهو له حلال
Mallam Rh Yace : Wanda Ya Musulunta Daga Cikin Maqiya (Abokan Fada, Wato Kafiri Wanda Ba Musulmi Ba, Ya Musulunta ) Kuma Ya Kasance Akwai Wani Abu ( Agunsa Shi Kafiri An Bashi Ajiya ) Na Daga /raujimetawiy/ Dukiyan Musulmai, Toh (Wannan Abun) Ya Zama Nasa Ya Zama Halaliyansa.
.
ومن اشترى شيئا منها من مال العدو لم يأخذه ربه إلا بالثمن
Hakanan Wanda Ya Sayi Wani Abu Daga Cikin Dukiyan Maqiyi ( Abokin Fada, Kafiri, Wanda Ba Musulmi Ba ) Toh Mai Wannan Kayan Ba Zai Amshi/Kar6i /raujimetawiy/ Wannan Kayan Ba Sai Ya Biya.
.
وما وقع فى المقاسم منها فربه أحق به بالثمن
Abunda Ya Fada/ Ya Shiga Cikin Kayan Ganima Da Za’a Rabawa Mayaqan, Mai Wannan Kayan Shi Yafi Cancanta /raujimetawiy/ Dashi, Amma Sai Ya Biya ( Misali Mutum Ne Ya Kasance Daya Daga Cikin Mayaqan Addinin Musulunci, Suka Je Yin Jihadi, Jihadi Na Gaskiya Yadda Allah Da Annabi S.A.W Suka Ce Ayi, Bawai Jihadi Na Yanzu Da Wasu Sukeyi Na Ta’addanci Ba, Toh Sai Ya Kasance Shi Wannan Mayaqin Yana Da Wani Abu Haka, Toh Bayan Angama Yaqi Anzo Ana 'Diban Kayan Ganima Da Za’a Tattara Akaiwa Kamanda Ya Raba, Toh A Halin Tattarawan Sai Wani Abu Nashi Ya Fada Cikin Kayan, Ana Nan Ana Nan Anzo Za’a Raba Kayan Ganima, Sai Ya Ga Kayansa A Ciki, Toh Idan /raujimetawiy/ Yayi Qirarin Cewa Wannan Nashi Ne, Ba Kayan Ganima Bane Kayansa Ne, To Baza’a Bashi Ba Sai Ya Biya Qiman Kudin Wannan Abun, In Qiman Abun Ya Kai N1000 Misali, Toh Sai Ya Biya N1000 Kafin A Bashi. Me Dabarar Yin Hakan? Sabida In Akabar Abun Haka Barkatete, Toh Duk Sa’ililn Da Aka Zo Raba Ganima, In Wani Yaga Wani Abu /raujimetawiy/ Zaice Nashi Ne, Wani Ma Inya Ga Wani Abu Zai Ce Ai Sam Wannan Kayansa Ne, Domin Acikin Mutane Ba Kowa Bane Yake Da Qarfin Imani, Ko Ya Ga Wani Abu Da Ransa Yake So, Kuma Akwai Kofan Da Zai Iya Bi Ya Mallaki Wannan Abun, Har Ya Iya /raujimetawiy/ Haquri Ya Bar Wnnan Qofan Ya Haqura Ya Bar Wannan Abun, Kai! Da Wuya. Wallahu A’alamu )
.
وما لم يقع فى المقاسم فربه أحق به بلا ثمن
Amma Abunda Bai Fada Cikin Kayan Rabon Ganima, Toh Mai Shi Shi Yafi Cancanta Dashi Ba Tareda Ya Biya Komai Ba.
.
ولا نفل إلا من الخمس على الإختهاد من الإمام

Ba’ayin Qari (Ga Mayaqa) Sai Dai Daga Kumusi ( Wato Daya Bisa Biyar 1/5 Kaso Daya Na Kwamanda Ne, Kaso Hudun Kuma Na Mayaqan Ne, Wato Baza’a Qarawa Mayaqa Akan Kaso Hudu Cikin Biyar 4/5 Ba) A Bisa Ijtihadin Shugaba/Kwamanda ( Sai Dai Idan Shi Kwamandan /raujimetawiy/ In Yaso Ya Qarawa Wanda Sukafi Qoqari A Cikin Kasonsa, Ya Dauka Ya Qara Musu )
.
ولا يكون ذالك قبل القسم
Hakan Ba Ya Kasancewa Kafin A Raba
( Bazai Yu Ba, A Qarawa Mayaqa Masu Hazaqa Wani Abu Tun Kafin A Raba Kayan Ganima, Dole Sai Angama Rabawa, In Za’ayi Qari Sai Ayi Qari, Wallahu A’alamu )
.
والسلب من النفل
Shi Salabu Yana Daga Cikin Dadi/Qari ( Abunda Ake Nufi Da Wassalabu, Shine Kmr Kwamandan Yaqi Yacewa Mayaqansa/Sojojinsa, Duk Wanda /raujimetawiy/ Ya Kashe Kafiri/Abokin Fada, Toh Kayan Wannan Kafirin Da Ya Kashe Nashi Ne Ya Zama Nashi Wallahu A’alamu )
الحمد لله
Duka-Duka Anan Zan Tsaya Da Izinin Allah S.W.T
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda muka yi Kuskure Wajen Rubutawa Allah Ya Yi Mana /raujimetawiy/ Afuwa Akansa, Allah Kuma Ya Sakawa Ibnu Abiy Zaideen Qirawaniy RH Da Alkairi Dubu-Dubu.
Ameen Summa Ameen.
.
Sai Ni Marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
Rabiu Amina Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM
.
01 Sha’aban 1442 Hijra
14 March 2021 Miladiyya
Ranar Lahadi

مع السلام فى أمان الله

02 Sha"aban 1446 Hijrah
31 January 2025 Miladiyyah
Ranar Juma'ah
raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, OR
Rabiu Amina Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI