002 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI

kashi na biyu
TAQAITTACCEN BAYANI AKAN AZUMI DAGA LITTAFIN RISALA NA IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY
بيان موجز عن الصيام من كتب رسالة لإبن أبى زيد القيروانى
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
In Bamu Manta Ba , A Kashi Na 'Daya Munce Insha Allahu Zamu Tashi A /raujimetawiy/ Inda Malam Yake Cewa:
وصوْمِ شهْر رَمَضَانَ فريضَةُُ يُصامُ لرُؤْيَةِ الْهلالِ ويُفطَرُ لِرُؤيَتِهِ،
Shi Azumin Watan Ramadan Farilla Ne Dole/Wajibi Ne ( Kadan Daga Cikin Ayoyin Da /raujimetawiy/ Suke Nuna Wajabcin Azumi, Mun Kawo Su A Kashi Na Ɗaya ) Kuma Ana Azumtan Ramadan Ne, Idan Anga Wata ( Ya Kama ) Hakanan Ana Ajiye /raujimetawiy/ Azumin Ne Idan Anga Watan Shawwal.
-
كان ثلاثين يومًا أوْ تِسعَة وعِشرِينَ يوْمًا
Kwana Talatin Ya Kasance Ko Kwana Ashirin Da Tara /raujimetawiy/
فَإنْ غُمَّ الْهِلالِ فَيُعَدُّ ثلاَثِينَ يوْمًا منْ غُرَّة الشَهْرِ الّذِى قبْلَهُ ثُمَّ يُصامُ
Hakanan Idan Watan Ramadan In Ya Faku/6uya Gareku ( Baku Ganshi Ba ) Toh Sai Ku /raujimetawiy/ Irga Kwana Talatin Daga Farkon Watan, Wanda Yake Kafinshi ( Wato Watan Sha'aban, Idan Lissafinku Ya Fita Dai-Dai ) Sai Kuyi Azuminku.
Domin Hadisi Yazo 
قَالَ صلَّى اللّهُ عَليْهِ وَسَلّمَ
لاَ تَصُومُوا حَتَى تَرَوَا الهِلاَلِ، وَلاَ تَفطُرُوا حَتَى تَروهُ، فَإِنْ غمَّ عَلَيْكُم فأَكْمَلُوا العَدَدَ ( العِدَةِ ) ثَلاثِينَ
MANZON ALLAH S.A.W YACE
" Kada Azumci ( Ramadan ) Har Sai Kunga Wata, Kuma Kada Ku Ajiye (Azuminku) Har Sai Kunga Wata, Idan Watan /raujimetawiy/ Ya 'Buya A Gareku Sai Ku Cika ( Kwanakinku ) Kwana Talatin.
MUWADDA MALIK
18 Kitabus Siyamm
Hadisi Na 636
وكَذلكَ فِى الْفِطرِ
Hakanan Wajen Ajiye Azumi ( Idan Aka Samu Tangardan Ganin Wata, Anyi Azumi 29 Ba'aga Wata Ba, Sai A Cika /raujimetawiy/ Azumi 30, Amma Idan Aka Cika Azumi Talatin, Washe Gari Kuma Sai A Tashi Da Sallah, Wallahu A'alamu )

-

ويُبَيِّتِ الصيَامِ فى أوَّلِهِ وليسَ عليْهِ البَيَات فِى بَقيّتهِ
Ana Yin Niyyan Yin Azumi A Farkonsa ( Idan Wata Ya Kama ) Babu Akan /raujimetawiy/ Mutum Niyya A Sauran Kwanakin Azumin, ( Niyyar Farko Wanda Mutum Yayi Ya Wadatar  " Wato Nayi Niyyan Yin Azumin Watan Ramadan, Kwana 29 Ko 30 " )
ويُتِمَ الصّيَامَ إَلى اللّيلِ 
Ana Cika Azumi Zuwa Dare, ( Wato Zuwa Faduwar Rana, Inka Kame Bakin Ka /raujimetawiy/ Daga Ci Da Sha, Da Al'aurarka Daga Fitowar Alfijir, Haka Haka Har Zuwa Faduwar Rana Magriba )
Wato Shine Fadin
ALLAH MADAUKAKIN SARKI
كُلُوا وَاشْرَابُوا حَتَى يَتَبَيَّنَ لكُمْ الْخَيْطُ الْأَبْيَضُ مِنَ الخَيْطِ الْأَسْوَدِ مِنَ الَفَجْرِ وَيُتِمُّ الصِّيَامَ إِلَى اللَّيْلِ.
سُورةُ الْبَقرَةِ
Ku Ci Ku Sha Har Sai Sililin Fari ( Alfijir Sadiqi ) Ya Bayyana A Gareku, Daga Sililin Baqi ( Wato Alfijir Kazibi ) Sa'annan /raujimetawiy/ Ku Cika ( Ku Sha Ruwa ) Ilal Lalli Zuwa Dare ( Wato Zuwa Faduwar Raduwar Rana )

ومِنْ السُّنَةِ تَعْجيلِ الفِطرِ وَتأَخِيرُ السُّحُورِ
Yana Daga Cikin Sunnahn ( Azumi ) Gaggauta Shan Ruwa ( Idan Ta Tabbata /raujimetawiy/ Rana Ya Fadi ) Da Kuma Jinkirta Yin Sahur,
وَإنْ شكَّ فى الْفجْرِ  فلاَ يَأَكُلُ
Wanda Yayi Kokonto Wajen Alfijir ( Shin Ya Fita Ko Bai Fita Ba )
ولاَ يُصاَمُ يَوْمُ الشّكُ لِيُحتاطَ بِهِ مِنْ رَمَضَانَ
Ba'a Yin Azumin Ramadan Ranar Kokonto ( Shin Wata Ya Kama Ne Ko Bai Kama Ba ) Domin Kiyayewa Kada /raujimetawiy/ A Hada Wani Rana Da Watan Ramadan ( Wato Kada A Hada Sha'aban Da Ramadan )
ومَنْ صَامَهُ كَذلِكَ لمْ يُجْزهِ، وإِنْ وافقَهُ مِنْ رَمَضَانَ
Wanda Yayi Azumi A Haka ( Cikin Kokonton Alfijir Ya Fita Ne, Ko Bai Fita Ba, /raujimetawiy/ Ko Kuma Kokonton Shin Watan Ramadan Ya Shiga Ne, Ko Bai Shiga Ba Toh Yin Azumi A Wannan Halin ) Bai Isar Masa Ba,
وَلِمَنْ شَاءَ صَومَهُ تَطَؤعَا أنْ تَفْعَلْ
( Amma A Halin Haka ) Wanda Ya So, Zai Iya Azumtan ( Wannan/ aujimetawiy/ Ranar ) A Matsayin Azumin Tawaddu'i ( Wanda Yaga Zai Iya ) Sai Ya Yii Azumin.

-

وَمَنْ أَصْبحَ فَلَمْ يَأَكُلْ وَلَمْ يَشْرَبْ، ثُمَّ تبيَّنَ لَهُ أنَّ ذلِكَ الْيَوْمَ منْ رَمَضَانَ لَمْ يُجْزِهِ، وَلْيُمسِكْ عَنِ الأَكلِ فِى بَقِيّةِ وَيَقْضهِ،
Wanda Ya Wayi Gari, Bai Ci Komai Ba, Bai Sha Komai, Sannan Ta Bayyana /raujimetawiy/ A Gareshi, Wannan Ranar Tana Daga Cikin Watan Ramadan ( Toh Kasancewar Bai Ci Komai Bai Sha Komai Ba, In Yace Zai Zarce Da Azumi ) Toh Hakan Bazai Isar Masa Ba, Sannan Kuma A Hakan Zai Kame Daga Ci Da Sha ( Har Zuwa Faduwar Rana, Bayan /raujimetawiy/ Sallah Kuma ) Zai Biya Azumin Wannan Ranar.

-

وإِذَ قدمَ المُسَافِرِ مُفْطِراً أوْ طهُرَتِ الَحائِضُ نَهَاراً فلهُمَا الأَكْلُ فِى بَقيَّةِ يَومهِمَا.
Hakanan Idan Matafiya A Gabata A Tafiya Yana /raujimetawiy/ Mai Karya Azuminsa, Ko Mace Mai Haila Tsarki Yazo Mata Da Rana, Toh Su Duka Biyu ( Matafiyin Da Ita Mace Mai Haila Tsarki Yazo Mata Da Rana ) Suna /raujimetawiy/ Da Daman Su Ci, Su Sha, A Sauran ( Awanni Da Mintocin ) Wannan Yinin 
-

وَمَنْ أَفْطَرَ فى تطَؤُعهِ عامداً أو سَافَرَ فيهِ فَأَفْطَرَ لِسَفَرِهِ فعَليْهِ القَضَاءُ، وَإِذَ أَفْطَرَ سَاهيًا فلاَ قَضَاءَ عَليْهِ بخِلاَفِ الْفَرِيضَةِ.
Wanda Ya Karya Azuminsa, A Azumi Na Nafila ( Wanda Ba Na Ramadan ) Da Gan-Gan, Ko Tafiya Ta Kamashi ( Imma Mace, Imma Namiji ) Sai Ya Karya Azumin Nasa, Saboda Tafiyar Tasa /raujimetawiy/ Toh Zai Biya Azumin Wannan Ranar.
Amma Idan Mutum Ya Sha Wani Abu, Ko Yaci Wani Abu, A Bisa Mantuwa ( Azumi Na Nafila ) Toh Babu Biya Akanshi, Sa6anin Azumin Farilla, /raujimetawiy/ ( Wato Ita Mazhabar Tamu Ta Malikiyyah, Idan Mutum Yana Azumin Ramadan Misali, Sai Mantuwa Ta Kamashi Yasha Wani Abu Ko Ya Ci Wani Abu, A Malikiyyah Zaka Kame Daga Ci Da Sha, Sannan Kuma Bayan Sallah Zai Biya Wannan Ranar, Amma In A Azumin Nafila Ne, Ba Komai.
Amma Hadisi Yace Mana Wanda Yake Azumi Ya Ci Wani Abu, Ko Ya Sha Wani Abu, Bisa Mantuwa Toh Babu Biya Akanshi, Allah Ne Ya Shayar Dashi /raujimetawiy/ Toh Kunga Anan Tareda Dukkan Girmamawa Dole Zamu Ajiye Fatawar Mazhabar Tamu, Mu Dauki Hukuncin Hadisi. Wallahu A'alamu )
-

Masha Allah Alhamdulillahi, Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Izinin Allah, Ba Tareda Tsawaitawa Ba.

Ubangiji Allah Muke Roqo Ya Bamu Ladan Abunda Muka Rubuta Dai-Dai, Abunda Muka Rubutu A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana.
Ameen Summa Ameen

Insha Allahu A Kashi Na Uku Zamu Tashi A
ولا بأس بالسواك للصائم فى جميع نهاره
-
marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,MVMech
-
10 Sha'aban 1446 Hijirah
12 February 2025 Miladiyyah
Ranar : Litinin
وداعا مع السلام

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI