003 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI

kashi na uku
TAQAITTACCEN BAYANI AKAN AZUMI DAGA LITTAFIN RISALA NA IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY
البيان موجز عن الصيام من كتب رسالة لإبن أبى زيد القيروانى
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje

-
ولاَ بَأَسَ بِالسوَاكِ لِلصََائِمِ فَى جَمِيعِ نَهَارِهِ،
Babu Laifi Yin Asuwaki Ga Mutum Da Yake Yin Azumi /raujimetawiy/ A Cikin Yininsa ( Amma Kuma Asuwakin Kada Ya Zama 'Danye, Kuma Koda Bushesshshe Ne, Ana So A Dinga Tufar Da Diddigin, Kar A Hadiye Shi. )
وَلاَ تُكْرَهُ لهُ الْحِجَامَةُ إِلاَ خِيفَةَ التَّغْرِيرِ
Ba'a Karhanta ( Mai Yin Azumi ) Yin Qaho, Sai Dai Don Gudun Gajiyarwa ( Don Shi Kunga Yin Qaho Jini Ne, Yake Fita, /raujimetawiy/ Toh Kunga Ba Ci Ba Sha, Jini Ya Fita Ai Za'a Samu Gajiyarwa A Azumin, Amma In Kaga Zaka Iya Yin Qahon Bazaka Gajiya Ba, Toh Bismillah )
Domin In Munje Ga 
MUWADDA MALIK
KITABUS SIYAMM
HADISI NA 664
حَدَّثَنِي يَحْيَى عَنْ مَالِكٍ عَنْ نَافِعٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ أَنَّهُ كَانَ يَحْتَجِمُ وَهُوَ صَائِمٌ- قَالَ- ثُمَّ تَرَكَ ذَلِكَ بَعْدُ فَكَانَ إِذَا صَامَ لَمْ يَحْتَجِمْ حَتَّى يُفْطِرَ. 
Wato Abdullahi 'Dan Umar RTA Ya Kasance Yanayin Qaho Alhali Yana Azumi, Qala Yace : Sa'annan Kuma Daga Baya Ya Dena Yin ( Qahon Idan Yana Azumi ) Fakana, Ya Kasance Idan /raujimetawiy/ Yana Azumi Bayayin Qaho, Sai In Yasha Ruwa.
-
وَمَنْ ذَرَعَعُ الْقَيْءُ  فِى رَمَضَانَ فَلاَ قَضَاءُ عَلَيهِ
( Wanda Yake Yin Azumi ) Sai Yayi Amai ( Ba Tareda Shi Ya Jawo Aman Ba, Da Gan-Gan ) A Azumin Ramada, /raujimetawiy/ Babu Biyan Azumi Akansa, ( Amma Idan Shi Ya Saka Yatsa A Bakinsa Ya Kwaqulo Aman Da Kansa Da Gan-Gan, Toh Zai Biya Wannan Azumin, Wallahu A'alamu )
وَإِن اسْتَقاء فَقَاهُ، فَعَلَيْهِ القَضَاءُ
Wanda Ya Jawo Aman Da Kansa ( Da Gan-Ganci ) Toh Zai Biya Wannan Azumin, /raujimetawiy/ ( Bayan Sallah )

وَإِذَ خَافَت الحَامِلُ عَلَى مَا فِى بَطْنِهَا أَفْطَرَتْ وَلَمْ تُطْعِم وَقَدْ قِيلَ تُطْعِم
Idan Mace Mai Ciki Taji Tsoron Abinda Yake Ciki Cikinta ( Idan Tayi Azumi Zata Galabaita Matuqa ) Toh Ta Ajiye Azumin, Ba Sai Ta Ciyar Ba, Amma /raujimetawiy/ A Wani Zancen Ance Zata Ciyar, Wallahu A'alamu.
.
وَلِلمُرْضِعِ إِنْ خَافَتْ عَلَى وَلَدِهَ وَلَمْ تَجِدْ مَنْ تَسْتَأَجِر لهُ، وَلَمٔ يَقٔبَلٔ غيْرَهَا أَنْ تُفْطِرَ وَتُطعِمَ
Hakanan ( Mace ) Mai Shayarwa Idan Taji Tsoro A Bisa Yaronta ( Da Take Shayarwa, In /raujimetawiy/  Tace Zatayi Azumi, 'Danta Bazai Samu Nonon Da Zai Sha Ba ) Kuma Ya Kasance Bata Samu Wata Matar Da Zata Shayar Mata Da Yaronta Ba, Ko Kuma ( Ya Kasance An Samu Wacce /raujimetawiy/ Zata Shayar Da Yaron, Amma Yaron Kuma ) Ba Ya Kar6an Nononta, Toh Anan ( Ita Wannan Matar Mai Shayarwar ) Ta Ajiye Azuminta Ta Ciyar.

-

وَيُسْتَحَبُ لِلشَّيخِ الْكَبِيرِ إِذَا أَفْطَرَ  أنْ يُطعِمَ، والإِطْعَامُ فِى هذَا كُلِهِ مُدَّ عَنْ كُلِ يَومِ يَقْضِيهِ
Anso Ga Tsoho ( Wanda Bazai Iya Yin Azumi Ba, Saboda Tsufa ) A Duk Lokacin Da Ya Sha, Sai Ya Ciyar, Ciyarwa A Cikin Haka Shine Muddan Nabiyyi Guda 'Daya A Kowacce Rana.
Saboda Akwai Hadisin Ibnu Abbas RTA Da Yake Cewa
"
رُخِّصَ لِلشَيْخِ الْكَبِيرِ أن يُطْعِمَ عَنْ كُلُ يَومِ مِسكِينًا وَلاَ قَضَاءَ عَليهِ 
الدار الفطنى والحاكم
Anyi Rangwame/Sauqi Ga Tsoho ( Ko Tsohuwa Wacce Bazata Iya Yin Azumi Ba ) A Kowanne Rana, A Madadin /raujimetawiy/ Kowacce Rana Zai Ciyar Da Miskini 'Daya, Kuma Babu Biyan Azumi Akanshi.
Dara Kudaniy Da Hakeem "

-

وَكَذَلِكَ يُطْعِمَ مَنْ فَرَّطَ فِى قضَاءِ رَمَضَانَ حَتَى دَخَلَ عَليْهِ رَمَضَانَ آخَرُ
Hakanan Wanda Yayi Sakaci Ana Binsa Azumi Har Wani Azumin Ya Shigo  Bai /raujimetawiy/ Biya Wancan Azumin Ba, Toh Shima Anan Zai Ciyar ( Amma Bugu Da Qari Ka Ziyarci Malamin Sunnah Mai Karantar Da Allah Yace Annabi Yace, Na Kusa Da Kai, Ba Malamin Tsubbu Ba /raujimetawiy/ Yayi Maka Qarin Bayani Akan Wannan Mas'alar, Domin Akwai Zantuka Da Dama Akai )
وَلاَ صِيَامَ عَلَى الصِّبْيَانِ حَتَى يَحْتَلِمَ الغُلاَمُ وتَحِيضَ الْجَارِيَةُ

Babu Azumi Akan Yara Har Sai Sun Balaga ( Abun Nufi : Yin Azumi 29 Ko 30 Bai Wajabta Akansu Ba, Amma Dai 'Dan Azumi 'Daya Biyu Za'ana Horonsu Da Yi, Gwargwadon Gimansu Da Shekarunsu Kafin Balagansu /raujimetawiy/ Gwargwadon Yadda Za'ana Horonsu Da Yin Azumin )
وَبِالبُلُوغِ لَزِمَنْهُمْ أَعمَالُ الأَبْدَانِ فَرِيضَةً
قَـــالَ الـــلَّـــهُ سُـــبْـــحَـــانَـــهُ
{ وَإِذَا بَلَغَ الأَطْفَالُ مِنْكُمْ الْحُلُمَ فَلْيَسْتَأذِنُوا }
سورة النور : ٥٩
Idan ( Yaranku ) Suka Balaga, Ayyukan ( Ibadan ) Na Jiki Ya Zama Dole /raujimetawiy/ Akansu
Shine Fadi ALLAH MADAUKAKIN SARKI { Idan Yara Daga Cikinku Suka Balaga, ( Maza Da Mata ) Toh Ku Umarcesu Da Aikata Aiki Na Ibada }
Suratul Nurr Aya Ta 59.

-

وَمَن أصْبَحَ جُنُبًا ولَمْ يَتَطهَّرْ أوِ امْرَأةٌ حَائِضٌ طَهُرتْ قبْلَ الْفَجرِ، فَلَمْ يَغْتَسِلاَ إِلاَ بَعْدَ الْفَجرِ أَجْزَأهُمَا صَوْمُ ذَلِكَ الْيَومِ.
Wanda Ya /raujimetawiy/ Wayi Gari Da Janaba A Jikinsa, Bai Samu Yayi Wanka Ba, Har Alfijir Ya Fito, Toh Yana Iya Yin Wankan Janabansa Daga Baya, /raujimetawiy/ Kuma Azuminsa Na Nan.
Hakanan Mace Wacce Take Al'ada, Tsarki Ya Zo Mata Kafin Alfijir Ya Fito, Sai Bayan Alfijir Ya Fito Tayi Wankan Tsarkinta, Azuminta Na Wannan Ranar Ya Isar Mata, Azuminta /raujimetawiy/ Na Wannan Ranar Yana Anan.
Domin Hadisi Yazo Kan Cewa Annabi S.A.W Yana Wayen Gari ( Zuwa Fitowan Alfijir ) Da Janaba Kuma /raujimetawiy/ Yana Mai Azumi.
Jeka
MUWADDA MALIK
KITABUS SIYAM
BABU : MA JA'A FIS SIYAM ALLAZI YUSBIHU JUNUBAN FIL RAMADAN
HADISI NA 642 Zuwa Hadisi Mai Numba 645
Zaka Gansu.
-
وَلاَ يَجُوزُ صِيَامُ يَومِ الْفِطْرِ وَلاَ يَوْمِ الْنَّحْرِ
Baya Halatta Azumtan Ko Yin Azumi A Ranar Sallar Azumi, Ko A Ranar Sallar /raujimetawiy/ Layya Ayi Azumi, Yin Hakan Baya Halatta.
وَلاَ يَصُومُ البَوْمَينِ الللَّذِينَ بَعْدَ يَومِ النَّحْرِ  إِلاَ المُتَمَتَّعُ الَّذِى لاَ يَجِدُ هَدْيًا.
Ba'a Azumta Kwanaki Biyu Wadanda Suke Bayan Sallan Layya, Amma Wanda Yayi ( Hajji ) Tamattu'i /raujimetawiy/ Zai Iya Yi Idan Bai Samu Abunda Zaiyi Hadaya Dashi Ba.
والْيَوْمِ الرَّابِعُ لاَ يَصُومُهُ، مُتَطَوِع، وَيَصُوممُ مَنْ نَذَرَهُ أَوْ مَنْ كانَ فِى صِيَامٍ مُتَتَابِعٍ قَبْلَ ذَلِكَ.
Da Kwanaki Hudu ( Na Bayan Sallan Layya ) Ba'a Azumtanshi Don Yin Tadawwa'i ( Azumin Nafila )
Wanda Yayi Bakace ( Yazo Dai-Dai Da Wannan /raujimetawiy/ Ranaku, Zai Azumce Shi, Ko Wanda Ya Kasance Yanayin Azumin A Jere Kafin Hakan ( Amma Ita Ranar Sallah, Ba'a Yin Azumi A Ranar )
.
.
Masha Allah Alhamdulillahi
Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Izinin Allah.
Abunda Muka Rubutu Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Muke Roqo Da Ya /raujimetawiy/ Yafe Mana, Yayi Mana Gafara.
.
Insha Allahu Kuma A Kashi Na Hudu Zamu Tashi A Inda Malam Mai Littafi Yake Cewa :
وَمَـــنْ أَفْـــطَـــرَ فِـــى نَـــهَـــارِ رَمَـــضَـــانَ ناسيا.
.
14 Ramadan 1446 Hijirah
14 March 2025 Miladiyyah
Ranar Juma'ah
3pm
.
marabuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
وداعا مع السلام

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI