IDAN AKA CE ANGA JINJIRIN WATAN RAMADAN A WATA QASAR, SHIN MUTANEN DAKE WATA QASAR DABAM ZASU 'DAUKI AZUMI

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
.          _--_--_--_    --_--_--_--
.          --_--_--_--   _--_--_--_
Na'am Zasu 'Dauki Azumi, Domin Hadisi Ya Tabbatar Da Cewa Ko Ina Aka Ga /raujimetawiy/ Wata, Ya Shafi Al'ummar Manzon Allah S.A.W Baki 'Daya.

MANZON ALLAH S.A.W YA CE
" Idan Kun Ga Jinjirin Wata, Toh Ku Azumce Shi /raujimetawiy/ Kuma Idan Kun Gan Shi Toh Ku Bude Bakinku ( Wato Ku Ajiye Azumin ) "
Bukhari
Muslim.
.
Abunda Ya Kamata A Fahimta Anan Shine Fadin MANZON ALLAH SAW
" Idan Kun Ga Jinjirin Wata Ku Azumce Shi, Kuma Idan Kun Gan Shi Ku Bude Bakinku "
.
Hakan Yana Tabbatar Da Umarni Da 'Daukan Azumi Ne Da Ajiyewa Ga Dukkan /raujimetawiy/ Al'ummarsa, Bawai An Ke6e Waɗansu Ne Ba, Aka Bar Waɗansu Ba.
Sai Dai An Samu Sa6anin Malamai Dangane Da Mafitar Wata, Wadansu Malamai Sunce Ana Iya Ganinsa A Wani Wuri Kamar Najeriya, Amma Ba'a Ganshi A Saudiyya Ba, Ko A Kalla A Saudiyya Ba'a Kalla A Najeriya Ba, /raujimetawiy/ Don Haka Suka Ce : Kowacce Mafita/Gari Ko Qasa Ta Dogara Da Ganin Watanta ( In Akace Za'ayi Haka, Abun Ya Zama Kayan Wasan Yara. Mafita Shine ) Tsayawa Akan Maganar Manzon Allah S.A.W Shine Yafi Dacewa /raujimetawiy/.
Kenan Ganin Wata A Waje 'Daya Ya Wadatar Da Dukkan Al'umman Musulmi.

Fadin
ALLAH MADAUKAKIN SARKI
يَــسْــأَلُــونَــكَ عَــنِ الْأَهِــلَّــةِ قُــلْ هِــيَ مَــواقِــيــتُ لِــلــنَّــاسِ وَالْــحَــجِّ
Ma'ana
" Suna Tambayarka Game Da Jira-Jiran Wata, Ka Ce Musu Shi Lokuta Ne Ga Mutane Da Hajji "
.
Amma Ai Ba'a Ta6a Jin Ko Ganin Wasu Mutane Sunce Zasuyi Amfani Da /raujimetawiy/ Ganin Watansu Daban Wajen Tsayuwan Arafah Ba, A Lokacin Aikin Hajji.
Amma Sai A Azumi Ne, Zakaga Mutane Ana Ta Gaddama Dasu.
Uhmm Allah Yasa Mu Dace AMINA
.
.
Abunda Muka Rubutu Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubutu Bisa Kuskure Allah Ya Yafe Mana.
Ameen Summa Ameen.
.
07 Ramadan 1446 Hijrah
07 March 2025 Miladiyyah
Ranar Juma'ah
12pm
.
marubuci
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
( Motor Vehicle Mechanic )


.
وداعا مع السلام

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI