MENE NE MAFIFICIN AIKIN DA YA KAMATA MAI AZUMI YA YI

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
Ayyukan Da Suka Fi Fifiko Ga Mai Azumi /raujimetawiy/ Sune
.
1- KARATUN Al-QUR'ANI MAI GIRMA : Wato A Lazimce Shi Dare Da Rana, Kuma A Dinga Qoqarin Fahimta Da Aikata Abinda Ake Karantawa. Amma Idan Baza'a Iya Karatun Al-Qur'anin Ba, /raujimetawiy/ Toh Sai A Dinga Lazimtan Inda Ake Karatun Al-Qur'anin Ko Fassara Shi.
Domin Hadisi Ya Tabbata Daga NANA A'ISHA RTA Da ABU HURAIRA Da IBNU ABBAS RTA Cewa :
Mala'ika Jibrilu AS Ya Kasance Yana Karanta Wa Annabi S.A.W Al-Qur'ani A Kowanne Dare Na Watan Ramadan Sau 'Daya A Kowacce Shekara, Sai Ya Karanta Masa Sau Biyu A Shekarar Da Zai Rasu.
Bukhari
Muslim
.
Wannan Hadisi Yana Nuna Mana Cewa Karatun /raujimetawiy/ Al-Qur'ani Shine Mafifficin Ibada A Cikin Ramadan.
Domin A Cikin Al-Qur'ani
ALLAH MADAUKAKIN SARKI YACE
شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِى أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ
Ma'ana
Watan Ramadan Wanda Ake Sauqe Al-Qur'ani A Cikinsa ( Allah Maɗaukakin Sarki Yana Nuna Cewa : Al-Qur'anin Nan An Sauqeshi Ne A Cikin Watan Ramadan )
Suratul Baqarati, Aya Ta 185
.
2 - KYAUTA : Ya Kamata Mai Azumi Ya Yawaita /raujimetawiy/ Kyauta Ta Hanyar Ciyar Da Jama'ah, Da Sadaka Da Taimakon Gajiyayyu, Da 'Yan,uwa Makusanta.
Kamar Yadda Ya Tabbata A Hadisin Abdullahi Ibnu Abbas RTA Cewa
" ANNABI S.A.W Yafi Kowa Kyauta, Kuma /raujimetawiy/ Yafi Yawaita Kyautarsa A Cikin Watan Ramadan, Musamman A Lokacin Da Yake Ganawa Da Mala'ika Jibrilu AS "
Bukhari.
.
3 - SALLAR NAFILA : Ana Son Mai Azumi Ya Yawaita Sallolin Nafila, Musamman /raujimetawiy/ Qiyamullaili ( Wato Sallar Dare ) Saboda Kwadaitarwa Da Manzon Allah S.A.W Yayi Mana.
An Kar6o Daga ABU HURAIRA RTA Ya Ce MANZON ALLAH S.A.W YACE : Duk Wanda Ya Tsaya Yin Sallar Qiyamullaili, Yana Mai Imani Da Neman Lada, An Gafarta Masa Zunubansa Da Suka Gabata/Wuce.
Bukhari.
.
Haka Kuma
ABU ZARRIY RTA Ya Ce
MANZON ALLAH S.A.W YA CE : Wanda Yayi Sallan Ashshan Tareda Da Liman Harya Idar Za'a Rubuta Masa Ladan Qiyamullaili.
Tirmiziy
Ibnu Majah.
.
Kuma Anfi Son Mai Qiyamullaili Ya Tsawaita /raujimetawiy/ Tsayuwa Saboda Hadisin Abu Zarriy R.T.A Ya Ce
" MANZON ALLAH S.A.W Ya Tara Iyalansa Da Matansa Da Sauran Jama'ah ( Lokacin ) Saura Kwana Uku Ramadan Ya Qare, Yayi Mana Sallah Mai Tsawo, Har Muka Ji Tsoron Kada Sahur Ya Ku6uce Mana "
Abu Dawud
.
Amma Abun Mamaki, A Yau Mutane Da /raujimetawiy/ Yawa Ba Sa Tsawaita Sallar Tarawihi, Kamar Yadda Wannan Hadisi Ya Nuna. A Madadin Haka, Sai Su Riqa Gaggawa Da Sunan Dafa-Duka ( Peugeout ) Don Su Kammala Da Wuri.
Kuma Waɗanda Keyin Sallar A Cikin Natsuwa Da Tsawaita Karatu Da Ruku'u /raujimetawiy/ Da Sujjuda, Sai A Riqa Qiransu Da Jirgin Danqarau..
.
4 - YAWAITA ZIKIRI : Ana Son Mai Yin Azumi Ya Yawaita Yin Zikiri Da Salatin Annabi S.A.W, Haqiqa Akwai Matuqar Falala Idan Aka Yawaita Zikirin Da Salatin Shugaban Halitta Irin Wanda Ya Tabbata Daga Bakin Manzon Allah S.A.W
.
5 - CIYAR DA MAI AZUMI ABIN BUDA BAKI : Yana Daga Cikin Mafificiyar Ibada, Taimakawa Masu Rauni /raujimetawiy/ Da 'Dan Abun Buda Baki.
Saboda Hadisin Da ANNABI S.A.W Yake Cewa
" Duk Wanda Ya Ciyar Da Mai Azumi Abunda Zaiyi Buda Baki, Yana Da Kwatankwacin Ladan Mai Azumin, Ba Tareda An Rage Ladan Wanda Ya Ciyar Ba "
Tirmiziy
Ibnu Majah.
.
6 - UMRAH : Yin Umrah A Cikin Watan Ramadan Ga Wanda Allah Ya Ba Shi /raujimetawiy/ Iko, Yana Daga Cikin Ayyukan Da Ake Kwadaitar Da Mai Azumi Ya Yi, 
Domin Hadisi Ya Tabbata Daga
MANZON ALLAH S.A.W YA CE :
Yin Umrah A Cikin Watan Ramadan Dai-Dai Da ( Ladan Aikin ) Hajji Yake.
A Wata Ruwayar : Wanda Yayi Umrah A Watan Ramadan, Tamkar Yayi Aikin Hajji Ne Tare Da Ni.
Sahihul Targibb
Mukhtasar Sahihul Bukhari, Tahqiqin Albani.
.
Amma Duk Da Haka, Bai Kamata Mutum Ya Tafi Umrah Ya Bar Makwabtansa Da Danginsa Da Sauran /raujimetawiy/ Mabuqata A Cikin Yunwa Da Halin Qaqa-Ni-Qa-Qa.
Kuma /raujimetawiy/ Ya Kamata Mu Fahimci Cewa Ciyarwa Ita Ce Abinda Annabi S.A.W Ya Fi Baiwa Muhimmanci A Cikin Watan Ramadan.
.
Masha Allah, Alhamdulillahi
تمت بحمد لله وحسن عونه والصلاة والسلام على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم تسليما
.
Abunda Muka Rubutu Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubutu A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana Yayi Mana Gafara.
.
09 Ramadan 1446 Hijirah
09 March 2025 Miladiyyah
Ranar Lahadi
8pm
.
marubuci
raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
( Motor Vehicle Mechanic )
وداعا مع السلام
.

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI