SU WANENE AZUMIN WATAN RAMADAN YA WAJABA AKANSU ETC

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
Azumin Watan /raujimetawiy/ Ramadan Yana Wajaba Akan Dukkan
 - Musulmi/Musulma
 - Baligi/Baliga
 - Mai Hankali
 - Wanda Yake Da Ikon Yi
 - Mazaunin Gida, Ba Matafiyi Ba.
-
Amma Kuma Waɗanda Azumin Watan Ramadan /raujimetawiy/ Bai Wajaba Akansu Ba, Sun Hada Da
-
1 - KAFIRI : Azumi Baya Wajaba Akansa, Haka Nan Ramuwa Bata Wajaba A Kansa Idan Ya Musulunta.
.
2 - YARO : Azumi Ba Ya Wajaba Akan Wanda /raujimetawiy/ Bai Balaga Ba, Amma Za'a Umarceshi Da Yin Azumin Domin Ya Saba, Kamar Yadda Magabata Suke Umartar 'Ya'yasu.
.
3 - MAHAUKACI : Azumi Bai Wajaba Akansa Ba, Dalili Kuwa Shine
MANZON ALLAH S.A.W YA CE
" An 'Dauke Alqalami ( Na Rubuta Zunubi/Alhaqi ) Akan Mutum Uku, Mai Barci Har Sai Ya Farka, Da Yaro Har Sai Ya Balaga, /raujimetawiy/ Da Mahaukaci Har Sai Ya Warke "
Sahihul Jami'il Sagir 3513
.
4 - TSOHO : Azumi Bai Wajaba Akan Tsohon Da Bazai Iyayin Azumi Ba Totally, Saboda Tsufansa, Amma Zai Ba Da /raujimetawiy/ Mudannabiy Guda Biyu, Ko Ya Ciyar Da Miskini Dafaffen Abinci A Madadin Kowacce Rana.
.
5 - MARA LAFIYA : Azumi Bai Wajaba Akan Mara Lafiyan Da Bazai Iyayin Azumi Ba, Sai Dai Akwai Ramuwa Akanshi Bayan Ya Warke, Ko /raujimetawiy/ Da Bayan Shekara Nawa Ne, Ba Ciyarwa Ba, Kamar Yadda Wadansu Ke Ciyarwa Maimakon Ramuwa.
Amma Ciwon/Cutar Da Kwararrun Likitoci Amintattu Suka Tabbatar Da Cewa Warkewan Wannan Ciwo/Cuta Ya Na Wahala, Ba Zai Rama Ba, Sai Dai /raujimetawiy/ Kawai Ya Ciyar A Madadin Kowacce Rana.

ALLAH MADAUKAKIN SARKI YACE
فَـمَـنْ كَـانَ مَـرِيـضًـا أَوْ عَـلَـى سَـفَـرٍ فَـعِـدَّةٌ مِـنُ أَيَّـامٍ أُخَر......
Ma'ana
Wanda Ya Kasance Daga Cikin Mara Lafiya, Ko Matafiyi Sai ( Ya Biya ) Adadin ( Abunda Ya Sha ) Daga Wasu Kwanaki Na Daban
Suratul Baqarati, Aya184
.
6 - MATAFIYA : Azumi Bai Wajaba Akan Matafiyi Ba, Amma Akwai Ramuwa A Kansa.
.
7 - MAI JININ HAILA KO JININ BIQI : Mace Mai Jinin Haila Ko Jinin Biqi Baza Tayi Azumi Ba, Amma Akwai Ramuwa /raujimetawiy/ A Kanta.
.
8 - MACE MAI CIKI KO MAI SHAYARWA : Zata Iya Ajiye Azumi Idan Tana Tsoron Cuturwarta Ko Cutuwar Abin Dake Cikinta, Ko Abinda /raujimetawiy/ Take Shayarwa Idan Ta Ci Gaba Da Azumin.
Dalili Na Cikin Hadisin Da Aka Rawaito Daga Anas 'Dan Malik Al-Ka'abi RTA Daga
MANZON ALLAH S.A.W YA CE
" Haqiqa Allah Ya 'Daukewa Matafiyi Rabin Sallah, Kuma Ya 'Dauke Azumi Ga Matafiyi Da Mai Ciki Da Mai Shayarwa "
Ibnu Makaho
.
Anan, Zamu Fahimci Cewa Matuqar Dai Cewa Matafiyi Da Mara Lafiya /raujimetawiy/ Zasu Rama Azumi, To Babu Abinda Zai Sa Ace Mace Mai Ciki Bazata Rama Ba.
Malamai Sunyi Sa6ani Dangane Da Ramuwa /raujimetawiy/ Ga Mai Ciki Da Mai Shayarwa. Wadansu Sun Tafi Akan Fatawar Abdullahi Ibnu Umar Da Abdullahi Ibnu Abbas Da Ishaq Ibnu Rahawaihi Cewa Mace Mai Ciki Da Mace Mai Shayarwa Babu /raujimetawiy/ Ramuwa Akansu, Sai Dai Zasu Ciyar.
Dalilinsu Kuwa Shine Fadin 
ALLAH MADAUKAKIN SARKI
وَعَـلَـى الَّـذِيـنَ يُـطِـيـقُـونَـهُ فِـدْيَـةٌ طَـعَـامِ مِـسْكِـيـنٍ
Ma'ana
A Bisa Wadanda Suke Yin Sa Da Wahala ( Shi Azumin ) Akwai Fansa ( Fansan Shine Zasu ) Ciyar Da Miskinai/Matalauci....
Suratul Baqarati, Aya 184
.
Suka Ce Wannan Ayar Ta Hada Da Tsofaffin Da Ba Zasu Iya Yin Azumi Ba, /raujimetawiy/ Da Mai Ciki, Da Mai Shayarwa.
Sheikh Albani RH A Cikin Irwa Al-Ghalil ( 4/18-24 ) Da Almajiransa A Cikin Sifat Sawm Nabiyyi Sun Tafi Akan Cewa Babu Wanda Ya Sa6awa Fatawar Ibnu Umar Da Ibnu Abbas RTA Cikin Sahabbai, Don Haka Za'ace /raujimetawiy/ Kamar Ijma'i Ne Sahabbai Suka Yi.
.
Mafi Yawan Malamai Sun Tafi Akan Cewa /raujimetawiy/ Mace Mai Ciki Da Mace Mai Shayarwa Suna Daga Cikin Marasa Lafiya, Don Haka Zasu Rama Azumin Da Suka Sha, Ba Tareda Ciyarwa Ba, Wannan Shine Ra'ayin Auza'i Da Hassanul Basariy Da Ibrahimul Naka'i.
Kuma Wannan /raujimetawiy/ Shine Ra'ayin Wadansu Daga Ciki Magabata Kamar Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah Da Almajiransa.
Daga Cikin Malamai Na Kusa-Kusan Nan Wadanda Suka Tafi Akan /raujimetawiy/ Wannan Fahimta Akwai Ibnu Bazz Da Al-usaimin Da Sauransu.
.
Amma Ni Dai Nafi Rinjayar ( Bawai Ni Rabiu A Umar Jimetawiy Ba, A'a Shi Mawallafin Littafin Wato Imamu Ahlul Sunnah Sheikh Abdulwahab Abdullah H, Yake Cewa : ) Yafi Rinjayar Da Maganar Mafi Yawan Malamai Cewa Mace Mai Ciki Da Mace Mai Shayarwa Idan Suka Sha Azumi Sabida /raujimetawiy/ Tsron Cutarwa Kansu Ko Ta 'Ya'yansu Toh Zasu Rama.
Wallahu A'alamu
.
Wannan Shine Qarshen Rubutaccen Wannan Jawabin Na Malam H.
Abinda Muka Rubuta Dai-Dai Allah Ya Bamu Ladansa /raujimetawiy/
Abinda Muka Rubutu A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana Yayi Mana Gafara.
Ameen Summa Ameen.
.
08 Ramadan 1446 Hijirah
08 March 2025 Miladiyyah
Ranar Asabar
5pm
.
marubuci
raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech
(Motor Vehicle Mechanic, mvmech)
وداعا مع السلام

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI