TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل البيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya ‘Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Ina Fata Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu /raujimetawiy/Allah Ya Basu Lafiya, Mamatanmu Kuma Allah Ya Ji Qansu Yayi Musu Rahma, Allahumma Ameen.
.
A Yau Cikin Ikon Allah Swt Nake Son Na 'Dan Rubuta Wani Abu Gamida Layya, Daga /raujimetawiy/ Littafin Fiqhun Malikiyya, Wato Muqaddimatul Iziyya Lil Jama’atul Azhariyya Na Sheikh Abi Hassan Aliyu Almalikiy Ash-shaziliy Allah Yayi Masa /raujimetawiy/ Tahma Ameen, Cikin Harshen Hausa.
.
Amma Ga Mai Buqatan Ganin Na Larabcin Zalla Sai Ya Leqa Zuwa Wani 'Dan /raujimetawiy/ Shafina A Facebook, Wanda Yake 'Dauke Da Tittle Kamar Haka
البيان الموجز عن الأضحية من كتاب فقه مالكي صغير
Ga Link In Da Zaka Bi Zuwa Dhafin
https://mobile.facebook.com/story.php?story_fbid=986779921750660&id=529561450805845
.
Toh Ga Abinda Mallam RH Yake Cewa Cikin Babi Na Bakwai Mai Bayani Akan Layya Da Ragon Suna Dama Dukkan Yanka.
.
Mallam RH Yace
Layya Itace Abinda Akeyin Ibada Dashi Domin Neman Kusancin Ubangiji Na Daga Dabbobi, Ranar Sallar /raujimetawiy/ Layya, Da Wuni Guda Biyu Masu Binta (Wato Ita Ranar Layyan), (Yin Layya) Sunnah Ce Ga Mai Iko, 'Da, Musulmi, Babba, Ko Yaro, Namiji, Ko Mace, Mazaunin Gida, Ko Matafiyi /raujimetawiy/ (Idan Suna Da Ikon Yi , Toh Sai Su Yi.)
.
(Hakan) Mutumin Da Yake Aikin Hajji A Mina Zai Yi, Mutum (Yana Iya) Yankawa Kansa /raujimetawiy/ Da Wađanda Ciyar Da Su Ya Lazimta Akanshi Kamar ‘Ya’ya Da Iyaye Talakawa (Da Basu Da Ikon Yi.)
.
Locakin Yinta (Lokacin Yanka Dabba) Shine /raujimetawiy/ Bayan Liman Ya Sauqo Ya Yanka Nashi ( Dabbar) A Ranar Layyan, Wanda Ya Yanka ( Ragon Layyansa) Kafin Liman Ya Yanka Nashi (Ragon Layyan) To (Ragonsa Da Ya Yanka) Bai Yi Ba (Nama Kawai Zai Ci, Amma Bashi Da Ladan Layyan), Haka Nan /raujimetawiy/ Wađanda Ba Su Da Liman (Misali A Garinsu, Qauye Ne Futuk Ko Masallacin Juma’ah Babu) Toh Sai Su Qirdado/Kwatanta Sallar (Idi) Shuwagabannin Da Suke Kusa Da Su, Hakan Ma Layyarsu (Zasu Kwatanta Da Lokacin Da Gari Mafi Kusa Da Su Suke Yanka Ababen Layyansu).
Shin Liman Innan Kam Ana Nufin Limamin Sallah Ne Ko Sarkin Gari, Akwai /raujimetawiy/ Zantuka Biyu Akan Hakan (Amma Ni A Gani Na Limamin Sallah Ake Nufi.)
.
Wanda Ya Yanka (Ragon Sallansa) Kafin Kafin Ranar Layya, Ko A Ranar Layyar (Ya Yanka) Bayan Futowar Alfijir Kafin Rana Ya Fito/Hudo, Toh (Layyansa) Bai Yuwa Ba (Nama Kawai Zai Ci /raujimetawiy/ Amma Ba Wai Layya Yayi Ba.)
.
Mafi Qarancin Abunda Yake Isa (Ayi) Layya Dashi, Shine Daga Dangi Bi-Biyu, Wato Dabbobi, Tutturna Daga /raujimetawiy/ Tumaki Da Awaki, Shine Wanda Ya Shekara 'Daya, Daga Raquma Kuma Shine Wanda Ya Shekara Biyar Ya Shiga Ta Shida.
.
Ana Kiyaye Aibu Daga Dabbar (Da Za’ayi) Layya Da Ita Ko Hadaya, (Kamar Wanne Da Wanne Kenan) Itace Wadda /raujimetawiy/ Idonta 'Daya Ya Mutu, Wato Hasken Ko Ganin Idonta Ya Tafi, Da Mara Lafiya Wanda Rashin Lafiyan Ya Bayyana, Haka Nan Gurguwa Wadda Gurguntakanta Ya Bayyana Sosai, Da Mara Kitse Itace Wacce Bata Da Mai Ko 'Bargo A Jikinta (Wato Gwanjamanmiya)
Hakanan Da Mai Tsageggen Kunne, Sai Dai Idan Tsagin Ya Zama Qanqani Ne, /raujimetawiy/ Kmr Misali Sulusi ('Daya Bisa Uku), Hakanan Mai Yankakken Kunne (Wanda Kunnen Ya Yanke) Ba Za Ta Wadatar Ba, Sai Dai Idan Yankewa Qanqanuwa Ce, Haka Gutsurewar/Cirewar/Yankewar Mafi Yawan Bindi/Biccoli/Jela (Shima Ba Zai Yi Ba) Hakanan Mai Karyayyen Qaho Yana /raujimetawiy/ Jini Bar Warke Ba, Amma Idan Ya Warke Sai A Yi Da Ita.
.
Mallam RH Yace
Yanka Ragon Suna Mustahabi Ne (An So Ne) (Amma Ga Mai Ikon Yankawa, Toh Sai Ya Yanka) Shine (dabbar) Da Ake Yankawa Ranar Bakwai /raujimetawiy/ Da Haihuwan Jinjiri, Shima Sharađinsa Kamar Na Layya Ne
.
Mallam RH Yace
Shi Yanka Shine Yanke Maqogaro Duka Tareda Yanke Jijiyoyin Wuya Duka, Yanke /raujimetawiy/ Abun Da Bai Kai Yanke Maqogaro Da Jijiyoyi Duka Ba, Toh Yankan Bai Yuwa Ba, Hakanan Yankan Mace Halattacce Ne (Idan Mace Ta /raujimetawiy/ Yanka Abu, Ba Matsala Za’a Ci.)
.
Idan Mai Yanka Ya Daga Hannunsa Daga Wuyan Abin Yanka, Bayan Ya Yanke Wasu Sassan Maqogaro Da Jijiyoyi, Sannan Ya Qara Mai Da Hannunsa Akan Abin Yankan Ya Qarasa /raujimetawiy/ Yankan Toh Baza’a Ci Ba, Idan Mai Yanka Garin Yanka Ya Yanke Wuyan Duka (Misali Ko) Da Gangan, Toh Mai Yankan Yayi Laifi Amma Za’a Ci, Wanda Ya Yanka (Dabba) Ta Qeya /raujimetawiy/ Ko Ta Gefen Wuya, Toh (Wannan Yankan) Ba Za’aci Ba.
.
Mallam RH Yace
Siffar Yanka /raujimetawiy/ Na Mustahabi Shine (Mutum) Ya Kwantar A Ita Ta Hagunta, Sannan Ya Fuskantar Da Ita Alqibla/Gabas, (Idan Ya Zo Yankawan) Sai Yace : Bismillahi Wallahu Akbar, Wato Shine Ya Hađa Tsakanin /raujimetawiy/ Kabbara Da Basmala, Kada Ya Ambaci Ko Ba Sai Yace Rahamanir Rahim Ba, Hakan Ba Sai Ya Yi Salati Ga Annabi S.A.W Ba, Idan Mai Yanka Ya Taqaita Kan Bismillah (Bai Yi Ba) To (Yankan) Yayi, Koda Ya Bar Yin Bismillan Da Mantuwa To Yankan Yayi Bisa Gamuwar Malamai, Hakanan Da Zai Barta Da Gangan Yankansa Yayi Inji Ibnu Qasum, Amma A Mazhabar Mudawwana /raujimetawiy/ Yankansa Bai Yi Ba, Da Mutum Zai Bar Fuskantar Da Dabba Gabas A Yayin Yanka, Ko Da Da Gangan Yayi Yankansa Yayi Za’a Ci.
Wallahu A’alamu
.
Masha Allah Alhamdulillahi
Wannan Shine Qarshen Abunda Malam /raujimetawiy/ Ya Kawo A Littafinsa Mai Albarka
.
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Allah Ya Bamu Ladansa, Wanda Muka Yi Kuskute Kuma Allah Ya Gafarta Mana
Ameen.
.
Marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, MVMech . BPM_PAN_PHM . ENGR . ATMech . APMech . AUYO . YOLA_NORTH
.
06 Zul-Hijjah 1441 hjr
27 July 2020 md
Ranar Litinin
.
.
Edited Time And Date
08 Zul-Hijjah 1446
04 June 2025
Ranar Laraba
.
Comments
Post a Comment