004 TAQAITTACCEN BAYANI AKAN AZUMI DAGA LITTAFIN RISALA NA IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY

kashi na hudu
TAQAITTACCEN BAYANI AKAN AZUMI DAGA LITTAFIN RISALA NA IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
In Bamu Manta Ba A Kashi Na Uku Munce Insha Allahu Ta'alah Zamu Tashi /raujimetawiy/ A Inda Malam Mai Littafi Yake Cewa :
.
وَمَنْ أَفْطَرَ فى نهَارِ رَمَضَانَ نَاسيََا فعَلَيْهِ الْقَضَاءُ فَقَطْ
Wanda Ya Karya Azumi ( Ya Ci Wani Abu, Ko Ya Sha Wani Abu, A Azumin Watan ) Ramadana A Bisa Mantuwa, Toh Zai Biya Wannan Azumin.
Amma Wannan Hukuncin, Hukuncin Mazhabar Malikiyya Ne, Amma Shi Hadisi Cewa Yayi :
صحيح البخاري
٣٦ - كتاب الصوم
٢٦ - باب: الصائم إذا أكل أو شرب ناسيا
١٨٣١ - حدثنا عبدان: أخبرنا يزيد بن زريع: حدثنا هشام: حدثنا ابن سيرين، عن أبي هريرة رضي الله عنه،
عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: (إذا نسي فأكل وشرب فليتم صومه، فإنما أطعمه الله وسقاه).
MANZON ALLAH S.A.W : Idan ( Mutum Yana Azumi Sai Ya ) Manta Yaci Wani Abu, Ko Ya Sha Wani Abu A Bisa Mantuwa, Ya Cika Azuminsa ( Ya Cigaba Da Yin Azuminsa ) Allah Ne Ya Ciyar Dashi, Ya Kuma Shayar Dashi.
Bukhari.
-
In Muka Yi Duba Da Wannan Hadisin, Hadisin Yana Mana Nuni Da Cewa : Duk /raujimetawiy/ Wanda Yake Azumi, Ya Manta, Ya Ci Ko Ya Sha Wani Abu, Mantuwa Na Gaskiya Ba Mantuwa Na Gan-Gan Ba, Toh Azuminsa Na Nan, Babu Biya Akanshi, Imma Azumi Farilla Imma Azumin Nafila.
.
وَكَذَلِكَ مَنْ أَفْطَرَ فِيْهِ لضَرُورَةِِ مِنْ مَرَضِِ
Hakanan Wanda Ya Ci Ko Ya Sha Wani Abu, /raujimetawiy/ Da Rana Saboda Lalura Ta Rashin Lafiya Haka ( To Shima Zai Rama/Biya Wannan Azumin )
*
وَمَنْ سَافرَ سَفَراََ تُقْصرُ فِيهِ الصَّلاَةُ فَلَهُ يُفطَرَ وإِنْ لمْ تَنَلْهُ ضَرُورَةٌ وَعَلَيْهِ الْقَضَاءُ
Wanda ( Yake Yin Azumi ) Yayi Tafiya Ko Muce Tafiya Ta Kama Shi, Wacce Wannan Tafiyar Ta Kai Ayi Sallar Qasaru /raujimetawiy/ Toh Yana Iya Ajiye Azuminsa Ya Sha Ruwa, Idan Hakan Bazai Zama Larura/Cutarwa A Gareshi, Daga Baya Kuma Sai Ya Biya Wannan Azumin.
والصَّوْمُ أَحَبُّ إِليْنَا
Amma Yin Azumin ( A Halin Tafiyan ) Shine Mafi Soyuwa A Wajenmu.
*
وَمنْ سَافرَ أَقَلَّ مِنْ أَرْبَعَةِ بُرُدِِ فَظَنَّ أَنَّ الْفِطْرَ مُبَاحٌ لهُ، فَأَفْطَرَ فَلاَ كُفِّارَةَ علَيْهِ، وَعَلَيْهِ الْقَضَاءُ
Wanda Yayi Tafiya ( Yana Mai Yin Azumi ) Wanda Tafiyar Ta Sa, Ta Kai Burudi Hudu
( Abunda Ake Nufi Da Burudi, Kowanne Burudi Shine Farsaki Hudu, /raujimetawiy/ Shi Kuma Farsaki Shine Mil Uku, Shi Kuma Mil Shine Taku Dubu, Ko Kace Zira'i. Muna Fatan Mun Fahimci Me Ake Nufi Da BURUDI )Yake /raujimetawiy/ Ganin Shan Ruwa Ya Halatta A Gareshi, Toh Sai Ya Sha Ruwansa Babu Yin Kaffara Akansa, Illa Biyan Wannan Azumin Da Yayi Sha.
وَكُلُّ منْ أَفْطَرَ مُتَأَوِّلاََ فلاَ كَفَارَةَ عَلَيْهِ
Malam Mai Littafi RH Ya Ce
Wanda Duk Karya Azuminsa A Bisa Wani Tawili, /raujimetawiy/ Babu Kaffara Akansa.
وَإِنَّمَا الْكَفَارَةٌ علَى مَنْ أَفْطَرَ مُتَعَمِّدََا بَأَكلِ أَوْ شُرْبِ أوْ جِمَاعِِ مَعَ القَضَاءِ
Kaffara Yana Afkuwa Ne Idan Mutum Ya Karya Azuminsa Da Gan-Gan Ta Hanyar Cin Wani Abu Ko Shan Wani /raujimetawiy/ Abu, Ko Kuma Jima'i/Saduwa, Toh Wanda Ya Aikata Hakan Akwai Kaffara Akansa Tare Da Biyan Wannan Azumin ( Wato Zaiyi Azumi 61, Sitti Na Kaffara, 'Dayan Kuma Na Wannan /raujimetawiy/ Azumin )
وَالْكَفَارَةُ فى ذَلِكَ إِطْعَامُ سِتِّينَ مِسْكِينَا، لِكٌُلِ مِسْكِينِِ مُدُُّ بِمُدِّ النَّبِيِّ ص: فَذَلِكَ أَحَبُّ إِلَيْنَا
( Yadda Ake Yin ) Kaffara Shine : Ciyar Da Miskinai Guda 60, Kuma Kowanne Miskini Za'a Ciyar Dashi Da Mudan-Nabiyyi  S.A.W, Ciyarwa Shine /raujimetawiy/ Yafi Soyuwa A Wajenmu.
وَلَهُ أَنْ يُكَفِّرَ بعِتْقِ رَقَبَةِِ أوْ صيَامِ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ
Hakan Nan Mutum Yana Iya Yin Kaffara ( Ta Hanyar ) 'Yanta Baiwa, Ko /raujimetawiy/ Kuma Ya Azumci Azumi Tsawon Wata Biyu A Jere ( Babu Yankewa )
*
وَلَيٍْسَ عَلَى مَن أَفْطَرَ فِى قَضَاءِ رَمَضَانَ مُتَعَمِّداََ كَفَّارَةُُ
Wanda Yakeyin Azumin Biyan Azumin Watan Ramada Sai Ya Karya, Babu Yin Kaffara /raujimetawiy/ Akanshi Don Ya Karya Wannan Azumin, Kuma Koda Da Gan-Gan Ya Karyashi.
وَمَنْ أُغْمِيَ عَلَيْهِ لَيْلاََ فَأَفَاقَ بَعْدَ طُلُوعِ الْفَجْرِ فَعَلَيهِ قَضَاءُ الصَّوْمِ،
Wanda Farfadiya Ta 'Daukeshi Da Daddare, Bai Dawo Hayyacinsa Sai Bayan Fitowar /raujimetawiy/ Alfijir, Toh Zai Biya Wannan Azumin ( Saboda In Munyi Duba Da, Lokacin Da Ya Dawo Hayyacinsa, Lokacin Sahur Ya Wuce )
وَلاَ يَقْضِى مِنَ الصَّلَوَاتِ إِلاَ مَا أَفَاقَ فِى وَقْتِهِ
( Mutumin Da Farfadiya Ta 'Daukeshi ) Bazai Biya Sallolin Da Suka Wuceshi Ba ( A Halin Da Yake Cikin Farfadiyan ) Sai Dai Sallolin Da /raujimetawiy/ Ya Dawo Cikin Hayyacinsa.
*
وَيَنْبَغِى لِلصٌَائِمِ أَنْ يَحفَظَ لِسَانَهُ وَجَوَارِحَهُ
Yana Kamata Ga Mai Azumi, Ya Kiyaye /raujimetawiy/ Harshensa ( Daga Zantukan Batsa, Karya, Gulma Dade Sauransu. Hakanan Kuma Ya Kiyaye /raujimetawiy/ ) Ga66ansa ( Suma Da Aikata Abubuwan Sa6o )
وَيُعَظٌِمُ مِن شَهْرِِ رَمَضَانَ مَا عَظَّمَ اللّهُ سُبْحَانَهُ
( Kuma Ana Buqata Ga Mutum ) Ya Girmama Watan Azumin, Kamar Yadda Allah Subhanahu Ya Girmamashi,
وَلاَ يَقْرَبُ الصَّائِمِ النِّسَاءِ بِوَطْءِِ ولاَ مُبَاشَرَةِِ ولاَ قُبْلَةِِ لِلَّذَّةِ فِى نَهَارِ رَمَضَانَ
Mutum Mai Azumi Ba'a Da Buqata Ya Kusanci /raujimetawiy/ Mata Don Yin Jima'i/Saduwa/Sexual Intercourse, Ko Runguma, Ko Yin Sunbunta/Kiss Wanda Zai Kai Ga Anji Dadi, Da Rana A Watan Ramadana,
وَلاَ يَحْرُمُ ذَلِكَ عَلَيْهِ فِى لَيْلَةِ
Amma Baya Haramta ( Ga Mutum, Saduwa Da Iyalinsa, Runguman Juna Ko Kiss ) Yin Hakan Da Daddare.
In Muka Duba Fadin Allah Madaukakin Sarki, Zamu Ga Cewar :
ﺃُﺣِﻞَّ ﻟَﻜُﻢْ ﻟَﻴْﻠَﺔَ اﻟﺼِّﻴَﺎﻡِ اﻟﺮَّﻓَﺚُ ﺇِﻟَﻰٰ ﻧِﺴَﺎﺋِﻜُﻢْ ۚ ﻫُﻦَّ ﻟِﺒَﺎﺱٌ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻧْﺘُﻢْ ﻟِﺒَﺎﺱٌ ﻟَﻬُﻦَّ 
سورة البقرة
An Halatta A Gareku Saduwa Da Matayenku A Azumi Da Daddare, Su ( Matayen Naku ) Tufafi Ne A Gareku, ( Hakanan ) Ku Ma ( Mazajen ) Tufafi Ne A Garesu.
Suratul Baqara
Ayata 187
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Masha Allahu Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Izinin Allah, Sai Dai Ina Mai Neman Afuwaku Bisa Jinkiri Da /raujimetawiy/ Aka Samu Tsakanin Kashi Na Uku Da Wannan Kashi Na Hudu,
Kashi Na Uku Mun Tsaya A 14-03-2025
Ubangiji Allah Muke Roqo
Abinda Muka Rubuta Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Ladansa, Abunda Muka Rubuta Bisa Kuskure, Ubangiji Allah Ya Yafe Mana.
-
Insha Allahu Kuma Zamu A Inda Malam RH Yake Cewa
ولا بأس أن يصبح جنبا
-
05 SAFAR 1447 Hijrah
30 JULY 2025 Miladiyya
Ranar Laraba
-
marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM_PAN_PHM . MVMech . ENGR . ATMech . APMech . AUYO . YOLA_NORTH

وداعا مع السلام

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI