005 TAQAITTACCEN BAYANI AKAN AZUMI DAGA LITTAFIN RISALA NA IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY
kashi na biyar
TAQAITTACCEN BAYANI AKAN AZUMI DAGA LITTAFIN RISALA NA IBNU ABIY ZAIDEEN AL-QIRAWANIY
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
Munce Daman Insha Allahu Zamu Tashi A Idan Malam RH Ya Ce :
وَلاَ بَأْسَ أَنْ يُصْبِحَ جُنُبََا مِنْ الْوَطْءِ
Babu Laifi Ga Wanda Ya Sadu ( Da Iyalinsa ) Ya Wayi Da Zanaba,
Idan Muka Duba MUWADDA MALIK
KITABUS SIYAMI
BABIN
باب مَا جَاءَ فِي صِيَامِ الَّذِي يُصْبِحُ جُنُبًا فِي رَمَضَانَ:
HADISIN NA
«642» حَدَّثَنِي يَحْيَى عَنْ مَالِكٍ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ مَعْمَرٍ الأَنْصَارِيِّ عَنْ أَبِي يُونُسَ مَوْلَى عَائِشَةَ عَنْ عَائِشَةَ أَنَّ رَجُلاً قَالَ لِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ وَاقِفٌ عَلَى الْبَابِ وَأَنَا أَسْمَعُ يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنِّي أُصْبِحُ جُنُبًا وَأَنَا أُرِيدُ الصِّيَامَ. فَقَالَ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((وَأَنَا أُصْبِحُ جُنُبًا وَأَنَا أُرِيدُ الصِّيَامَ فَأَغْتَسِلُ وَأَصُومُ)). فَقَالَ لَهُ الرَّجُلُ يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّكَ لَسْتَ مِثْلَنَا قَدْ غَفَرَ اللَّهُ لَكَ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ. فَغَضِبَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَقَالَ: ((وَاللَّهِ إِنِّي لأَرْجُو أَنْ أَكُونَ أَخْشَاكُمْ لِلَّهِ وَأَعْلَمَكُمْ بِمَا أَتَّقِي)).
Hadisi Mai Dan Tsayi
Wani Mutumi Yake Tambayar MANZON ALLAH S.A.W Yana Mai Tsaye A Qofa, Yace : Ya! Ma'aikin Allah Ni Na Wayi Gari Da Janaba Kuma Ina So Inyi Azumi, Sai MANZON ALLAH S.A.W YA CE : Nima Ina Wayan Gari Da Janaba, Kuma Ina Son Yin Azumin, Don Haka Kayi /raujimetawiy/ Wankanka Ka Ci Gaba Da Azuminka....
( Hakanan Mutunmin Da Ya Sadu Da Iyalinsa, Baiyi Wankan Janaba Ba, /raujimetawiy/ Har Lokacin Sahur Yayi Baiyi Wanka Ba, Bayan Yayi Sahur Kuma Alfijir Ya Fito Ya Sameshi Da Janaba, Toh Azuminsa Na Nan, Yayi Wankansa Yaci Gaba Da Azuminsa, Amma A Kiyayi Yin Hakan )
وَمَنِ الْتَّذَ فِى نَهَارِ رَمَضَانَ بِِمُبَاشَرَةِِ أَوْ قُبْلَةُُ فَأَمْذَى لِذَلِكَ فَعَلَيْهِ الْقَضَاءُ
Wanda Yayi Runguma Ko Sunbunta/Kiss Da Rana A Watan Ramadana Har Yaji Dadi, Har Ta Kai Ga Ya /raujimetawiy/ Fitar Da Maziyyi, Toh Akanshi Akwai Biyan Wannan Azumin,
وَإِنْ تَعَمَّدَ ذَلِكَ حَتَى أَمْنَى فَعَلَيْهِ الْكَّفَارَةُ
Idan Mutum Ya Ganganta Yin Haka ( Runguma Ko Kiss Har Ta Kai Ga ) Ya Fitar Da Maniyyi, Toh Akwai Kaffara Akanshi.
*
وَمَنْ قَامَ رَمَضَانَ إِيمَانَا وَاحتِسَابََا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ
Wanda Ya Tsaya/Dage A Ramadana ( Wajen Yin Nafilfili ) Yana Mai Imani Da Neman Lada, Za'a Gafarta /raujimetawiy/ Masa Abunda Ya Gabata Daga Zunubansa
وَإِنْ قُمْتَ فِيهِ
Idan Ka Tashi Cikinsa ( Da Daddare, Kana Mai Yin Nafilfili )
بِمَا تَيَسَّرَ
( Ka Sallaci Sallan Nafila Gwargwadon ) Abunda Ya Sauqaqa
فَذَلِكَ مَرْجُوََّ فَضْلُهُ، وتَكْفِيرُ الذُّنُوبِ بِهِ
Kana Mai Neman Falalarsa, Da Neman /raujimetawiy/ Gafarar Zunubai ( Wannan Duka Abun So Ne)
وَالْقِيَامُ فِيهِ فِى مَسَاجِدِ الْجَمَاعَاتِ بِإِمَامِ
Wal Qiyamu Shi Tsayuwan ( Nafilfili Dare, Ana So A Yi Shi ) A Masallatai Na Jama'ah, Tareda Mutane, Kuma Da /raujimetawiy/ Liman.
وَمَنْ شَاءَ قَامَ فِى بَيْتِهِ وَهُوَ أَحْسَنُ لِمَنْ قَوِيَتْ نِيَّتُهُ وَحْدَهُ،
Wanda Ya So, Ya Ga Zai Iya Yin Nafilfilin A Gidansa ( Toh Sai Ya Yi ) Hakan Shine Mafi Kyawu, Ga Wanda Ya /raujimetawiy/ Tsaida Niyyansa Shi Kadai.
*
وَكَانَ السَّلَفُ الصَّالِحُ يَقُومُونَ فِيهِ فِى المَسَاجِدِ بِعِشْرِينَ رَكْعَةََ
Magabata Na Kwarai RH Sun Kasance Suna Nafilfilin Dare Ko Muce Sallan Ashsham A Masallaci, ( Kuma /raujimetawiy/ Su Sallan Ashsham Na Su ) Raka'ah Ashirin Suke Yi
ثُمَّ يُوتِرُونَ بِثَلاَثِِ، وَيَفْصِلُونَ بَيْنَ الشَّفْعِ والْوِتْرِ بِسَلاَمِ
Sannan Su Yi Shafa'i Da Witiri Raka'ah Uku, Amma Suna Raba Tsakanin Shafa'i Da Witiri Da Sallama ( In Sunyi Raka'ah Biyu Na Shafa'i Sai /raujimetawiy/ Suyi Sallama, Sannan Su Kawo Raka'ah Daya Ba Witiri, Sai Suyi Sallama )
ثُمَ صَلَّوا بَعْدَ ذَلِكَ سِتَّا وَثَلاَثِينَ رَكْعَةََ غَيرَ الشَّفْعِ وَالوِتْرِ
( Bayan Sunyi Sallan Ashsham Raka'ah 20, Da Shafa'i Da Wutiri, Sai Suqa Tashi Su ) Sallaci Sallah Raka'ah Talatin Da Shida ( Allahu Akbar, Allah Ya Qara Rahma Da Jin Qai Ga Salafus Salih /raujimetawiy/ Allah Ya Bamu Ikon Kwaikwayonsu ) Amma Banda Shafa'i Da Wutiri ( Tunda Sun Yi Ta A Baya, Ba Buqatan Maimaita ta )
وَكُلُّ ذَلِكَ وَاسِعُُ
Dukkan Hakkan Mayalwaci Ne ( Yana Da Kyau, /raujimetawiy/ In Kaga Zaka Iyayin Wadannan Nafilfilin )
وَيُسَلِّمُ مِنْ كُلِّ رَكْعَتَيْنِ
( Ana So ) A Duk Raka'ah Biyu ( Ta Sallahn Nafila ) Ayi Sallama.
Wannan Magana In Mukayi Duba Zuwa
MUWADDA MALIK
KITABUS SALATIL LAILI
BABU MA JA'A FI SALATIL LAILI
HADISI NA 261
وَحَدَّثَنِي عَنْ مَالِكٍ أَنَّهُ بَلَغَهُ أَنَّ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ عُمَرَ كَانَ يَقُولُ صَلاَةُ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ مَثْنَى مَثْنَى يُسَلِّمُ مِنْ كُلِّ رَكْعَتَيْنِ.
Daga Abdullahi Dan Umar Ya Kasance Yana Cewa ( Salatil Laili Wal Nahari ) Sallan ( Nafila ) Na Dare Ko /raujimetawiy/ Na Rana, Raka'ah Bibbiyu ( Ake Son Yi ) A Duk A Raka'ah Biyu ( Ana Son Ayi ) Sallama.
*
وَقَالَتْ عَائِشَةُ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا : مَا زَادَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِى رَمَضَانَ وَلاَ فِى غَيْرِهِ عَلَى اثْنَتَى عَشْرَةَ رَكْعَةََ بَعْدَهَا الْوِتْرُ.
NANA AISHA RTA Ta CE : MANZON ALLAH S.A.W Bai Kasance Yana Qarawa ( Sallan Nafila ) A Ramadana Ko Wanin Ramadana Sama Da Raka'ah Goma-Sha-Biyu.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
تمت بحمد لله وحسن عونه، ثم الصلاة والسلام على سيدنا ومولانا محمد نبى.
Duka-Duka Ana Qarshen Wannan Fasali Ya Qare, Daga Littafin RISALA Na Ibnu Abi Zaideen Al-Qirawaniy Ubangiji Allah Ya Qara Jaddada /raujimetawiy/ A Gareshi.
*
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Allah Ya Bamu Ladansa, /raujimetawiy/ Abunda Muka Rubuta Bisa Kuskure Kuma Allah Ya Gafarta Mana.
Ameen Summa Ameen.
*
08 SAFAR 1447 Hijrah
02 AUGUST 2025 Miladiyya
Ranar Asabar
*
marubuci
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM . CON . MVMech . ENGR . ATMech . APMech . AUYO . YOLA NORTH
وداعا مع السلام
Comments
Post a Comment