001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA

kashi na daya
TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda 
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa.
*
Amma Kafin Nan, Ya Kamata Mu 'Dauko Aya 'Daya Biyu /raujimetawiy/ Da Hadisi Daya Biyu Dangane Da Aure.
*
Na Farko
قَالَ اللَّهُ تَعَالَى
ٰ ﻓَﺎﻧْﻜِﺤُﻮا ﻣَﺎ ﻃَﺎﺏَ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻦَ اﻟﻨِّﺴَﺎءِ ﻣَﺜْﻨَﻰٰ ﻭَﺛُﻼَﺙَ ﻭَﺭُﺑَﺎﻉَ ۖ ﻓَﺈِﻥْ ﺧِﻔْﺘُﻢْ ﺃَﻻَّ ﺗَﻌْﺪِﻟُﻮا ﻓَﻮَاﺣِﺪَﺓً ﺃَﻭْ ﻣَﺎ ﻣَﻠَﻜَﺖْ ﺃَﻳْﻤَﺎﻧُﻜُﻢْ ۚ
سورة النساء
ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE :
Ku Auri Wadanda Suka Dadada Muku ( Suka Burgeku ) Daga Mata ( Imma Mata ) Bibbiyu ( Inkaga Zaka Iya, Kuma Ka San Zakayi Adalci ) Ko Mata Uku, Ko Mata Hudu, Amma In Kun San Baza Kuyi Adalci Ba ( Dangane /raujimetawiy/ Da Mata Biyu, Uku Ko Hudu, Toh Sai Ku Auri ) Guda 'Daya Ko Kuma Abunda Hannayenku Suka Mallaka ( Na Daga Bayi Ko Quyangu.
Suratul Nisa'i.
*
A Gurguje, Na Biyu
قَالَ اللَّهُ تَعَالَى
" وَانْکﺤُﻮا اﻷَْﻳَﺎﻣَﻰٰ ﻣِﻨْﻜُﻢْ ﻭَاﻟﺼَّﺎﻟِﺤِﻴﻦَ ﻣِﻦْ ﻋِﺒَﺎﺩِﻛُﻢْ ﻭَﺇِﻣَﺎﺋِﻜُﻢْ ۚ ﺇِﻥْ ﻳَﻜُﻮﻧُﻮا ﻓُﻘَﺮَاءَ ﻳُﻐْﻨِﻬِﻢُ اﻟﻠَّﻪُ ﻣِﻦْ ﻓَﻀْﻠِﻪِ ۗ ﻭَاﻟﻠَّﻪُ ﻭَاﺳِﻊٌ ﻋَﻠِﻴﻢٌ "
سورة النور
ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE : Ku Auri Bazaware Daga Cikinku, Da ( Mata ) Salihai Daga Cikin Bayinku Da Quyanganku, In Sun Kasance /raujimetawiy/ Matalauta Allah Zai Wadatar Dasu Daga Falalarsa, Lalle Allah Mayalwaci Ne, Alimun Masani Ne.
S. NURI
*
Idan Mukaje Gefen Hadisi, A Gurguje 
وَقَالَ صَلٌَى اللٌَهُ عَلَيْهِ وَسَلٌَمَ : يَا مَعْشَرَ الشٌِبَابِِ مَنِ اسْتَطَاعٕ مِنْكُمْ البَاءَةَ فَلْيَتَزَوَجْ فَإِنٌَهُ أَغَضٌُ لِلْبَصَرِ وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصٌَومِ فَإِنٌَهُ وِجَاءُُ 
رواه البخاري ومسلم والترمذي وأبو داود والنسائي ( والباءة النكاح ونفقات الزوجة )
MANZON ALLAH S.A.W YA CE :
Ya! Ku Taron Matasa Wanda Yake Da Ikon Yin Aure /raujimetawiy/ Toh Yayi Aure, Domin Shi Yin Aure Yana Kare/Kiyaye Gani ( Wajan Yawaitan Kalle-Kallen 'Yan Mata Kallo Na Sha'awa, Da Kalle-Kallen Matan Mutane ) ( Kuma Shi Yin Aure ) Yana /raujimetawiy/ Kiyayewa Ga Al'aura ( Wajen Fadawa Ga Yin Zinace-Zinace, Domin A Duk Lokacin Da Kaji Sha'awa Ta Tashin Maka, Toh Ga Matarka Ta Sunnah Halaliyarka ) Wanda Bashi Da Ikon Yin Aure Kuma ( Annabi S.A.W Yace : ) Na Horeshi Da Yin Azumi, Domin Shi Yin Azumi Yana Nan Kamar Dandaqa Ne, ( Ka Ga Mutumin Da Yake Yin Azumi, Yunwa Da Kishin Ruwa Basu Barshi Har Sha'awa Da Wani Kalle-Kallen Mata Yayi Tasiri A Gareshi Ba /raujimetawiy/ Da Zarar Ya Sha Ruwa Kuma Zai 'Danji Gajiwa Ya Dan Shigeshi, Kuma Ga Dare Yayi Wallahu A'alamu )
Bukhari, Muslim, Tirmizi, Abu-Dawuda Da Nasa'i Ne Suka Rawaito
***** ***** ***** ***** *****
*
GA KADAN DAGA CIKIN FALALAR AURE
In Mukayi Duba Da Wani Hadisi Zamuga Cewa
قَالَ مُعَاذٌ بنْ جبَلِِ رَضِيَ اللٌَهُ عَنْهُ : صَلاَةُُ المُتٌَزَوٌِج أفْضَلُ مِنْ أَرْبَعِينَ صَلاَةََ مِنْ غَيْرِهِ 
Mu'azu Dan Jabal R.T.A Ya Ce
" Sallahr Mutum Mai Aure ( Amma Sallah Ta Nafila ) Tafi Fifiko Ga Sallar Mara Aure Da Sallah ( Raka'ah ) Arba'in.
*
A Wani Hadisi Kuma
قَالَ اِبنُ عَبَّاس رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ  تَزَوٌَجُوا فَإِنٌَ يَومََا مَعَ التَّزَوٌُجِ خَيْرُُ مِنْ عٓبَادَةِِ أَلْفِ عَامِِ
Ibnu Abbas R.T.A Ya Ce : Tazawwaju Kuyi Aure, Domin Yini 'Daya Tareda Aure, Yafi Ibadar Shekara Dubu.
*
Allahu Akbar
Ashe Shi Aure Yanada Wata Falala Ta Musamman.
Amma Ba Kamar Yadda Iyaye Da 'Yan Mata Suka Maida Shi Ba, An Dauki Gidan Miji Gidan Hutawa Da Jin Dadi Da Miqe Qafafuwa Da Kwadayin Abun Duniya, Ba Zaman Ibada Ba, /raujimetawiy/ Yana Daga Matsalolin Da Yake Kawo Yawan Sake-Sake, Allah Ya Sauwaqa, Ya Kare Faruwan Wadannan Abubuwan.
*
Insha Allahu
Zamu Tsaya Anan, Daga Qarshe Muna Adu'ah Ga Matasan Da Suke Da Burin Yin Aure, Ubangiji Allah Ya Sahale Musu, 'Yan Matan Kuma Ubangiji Allah Bawa Iyayensu Damar /raujimetawiy/ Aurar Dasu.
*
Wata Qila A Kashi Na Biyu, Mu 'Dan Kawo Hadisan Da Suke Magana Akan Falalar 'Ya'yaye.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
17 Rabi'ul Awwal 1447 Hijrah
09 September 2025 Miladiyya
Ranar : Talata
*
marubuci
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVMech, ATMech, APMech, AUYO, YOLA_NORTH

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI