002 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA


@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.

*

A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda 
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa.

*

Insha Allahu Ta'alah, A Kashi Na 'Daya Mun Ce Zamu 'Dan Kawo Hadisi 'Daya Zuwa Biyu Da Suke Magana Akan /raujimetawiy/ Falalar 'Ya'yaye.
Don Da Yawa Daga Cikin Mutane Zakaga Suna Qin Yin Aure Don Yara, Su Ba Iya Rainon Yara Ba, Qazanta Wawe Etc.

*

Toh Wanda Yace Ma Shi Baya Son Yara Ya 'Dan /raujimetawiy/ Tsaya Yaji Wadannan Hadisan.

*

وقَالَ عَلَيْهِ الصٌَلاَةُ والسٌَلاَمُ :
لِأَنْ يُوَدٌِبَ الرٌَجُلُ وَلَدَهُ خَيرُُ لَهُ مِنْ أَنْ يَتَصَدٌَقَ بِصَاعِِ.
رواه الترمذي عن جابر بن سمرة
وهو حديث حسن
MANZON ALLAH S.A.W YACE :
Mutum Ya Ladabtar Da 'Dansa ( Kyakkyawan Ladabi Na Musulunci ) Yafi Alkhairi A Gareshi, Da Akan Ya Bada Sadaka Da Sa'i.
Tirmizi Ne Ya Rawaito Shi
Daga Jabir 'Dan Samrata.

*

Wani Hadisi Kuma Yace
وَقَالَ عَلَيْهِ الصٌَلاَةُ وَالسٌَلاَمُ : أَكْرِمُوا أَوْلاَدَكُمْ فَإِنٌَ كَرَامَةَ الأَوْلاَدِ سِتْرُُ مِنْ النَّارِ.
MANZON ALLAH S.A.W YACE :
Ku Girmama'Ya'yanku ( Girmamawa /raujimetawiy/ Ba Wacce Zata Kai Ga Shogwobantar Da Yaro Ba, Domin Akwai Girmamawa Da Nuna Soyayya Da Yake 'Bata Yara ) Lalle Domin Girmama Yara Sutura Daga Shiga Cikin Wuta

*

Qalubale Ga Mutanen Da Zaka Ga Common Yara Basa Tausayawa, Masu Aikata Irin Haka Ga Yara Na Rashin /raujimetawiy/ Tausayawa Bari Kuji Abunda Hadisi Ya Fada

قَالَ عَلَيْهِ الصٌَلاَةُ والسَّلاَمُ
إِنٌَ فى الْجَنٌَةِ دَارََا يُقَالَ لَهَا دَارُ الْفَرَحِ لاَ يَدْخُلُهَا إِلاَ مَنْ فَرٌَحَ الصٌِبْيَانَ
رواه أبو يعلى عن عائشة
MANZON ALLAH S.A.W YACE : Lalle A Cikin Aljanna Akwai Wani Gida /raujimetawiy/ Ana Qiran Wannan Gida Da Darul Farahh ( Gidan Farin Ciki ) Babu Mai Shiganta Face Sai Mai Farantawa Yara.
Abu Ya'ala Ya Rawaiceshi.
Daga Nana Aisha R.T.A

*

A Gefe Guda Kuma Zakaga Wasu 'Yan Dama-Daman Suna Son 'Ya'yan Amma Sai /raujimetawiy/ Maza Banda Mata, Maza Kawai Zalla, Toh Bari Kuji Falala Da Qima Ga Wanda Allah Ya Bashi Haihuwan 'Ya'ya Mata, Idan Yayi Musu Abu Kaza Da Kaza Ga Sakamakonsa A Lahira.

قَالَ علَيْهِ الصٌَلاَةُ وَالسٌَلاَمُ : مَنْ كانَ لَهُ أُنثَى فلَمْ يَئِدْهَا وَلمْ يُهِنْهَا وَلَمْ يُؤْثِرْ وَلَدَهُ عَلَيْهَا أَدْخَلَهُ اللهُ الْجَنٌَةَ.
رواه أبو داود
MANZON ALLAH S.A.W YACE : Wanda Ya Kasance Yana Da Yara Mata, Kuma Bai Binnesu Da Ransu Ba ( Domin Larabawa A Zamanin Jahiliyya Sun Kasance Suna Binne 'Ya'yansu Mata Da Ransu, Wai Don Tsoron/raujimetawiy/ Jawo Musu Abun Kunya ETC, Toh Duk Wanda Bai Binne 'Yarsa Ba, ) Kuma Bai Wulaqantar Da Ita Ba, Bai Kuma Fifita 'Dansa Namiji Akanta Ba ( Domin Da Yawa Har Yanzu Akwai Iyayen Da Sukafi Fifita 'Ya'yansu Maza Akan 'Ya'yansu Mata, Wannan Babu Kyawu /raujimetawiy/ 'Ya'ya Kowa Da Albarkarsa, Toh Manzon Allah S.A.W Yace : Duk Wanda Bai Aikata Hakan Ba, Annabi Yace : ) Allah Zai Shigar Dashi Aljanna.
Abu-Dawuda Ne Ya Rawaito Shi.
In Muka Yi Duba Da Wannan Hadisi Zamuga Ashe, 'Ya'ya Mata Ba Abun Qi Bane.
*

A Gefe Guda Kuma Ya Kamata Kafin Mu Tafi, Muji Haqqin 'Ya'yaye Akan Iyayensu, Suma 'Ya'yaye Suna Da Haqqi Akan Iyayensu, Bawai Kawai A Dinga /raujimetawiy/ Haifosu Any How Ba, Ba Tarbiyya Babu Plan Etc, Ga Wani Hadisi Nan, Bari Muji Mai Manzon Allah S.A.W Yace,
قَالَ صَلٌَى اللٌَهُ عَلَيْهِ وَسَلٌَمَ : إِنٌَ مِنْ حَقٌِ الْوَلَدِ عَلَى وَالِدِهِ أَنْ يُعَلٌِمَهُ الكِتَابَةَ وَأَن يُحْسِنُ اسْمَهُ وَأَنْ يُزَوٌِجَهُ إِذَا بَلَغَ
رواه ابن النجار
MANZON ALLAH S.A.W YACE : Yana Daga Haqqin 'Da Akan Ubansa /raujimetawiy/ Da Ya Sanar Dashi ( Ma'ana Ya Koyar Dashi, Ko Ya Kaishi Inda Za'a Koyar/Karantar Dashi )  Littafi ( Al-Qur'ani Ne, Hadisi Ne, Fiqhu Ne Etc Kuma Dole Uba Inya Zo Sanyawa 'Dansa Suna, Ya Sanyawa 'Dansa ) Kyakkyawan Suna, Suna Mai Kyau, Suna Na Musulunci, Inya Girma Ya Balaga Kuma Ya Aurar Dashi, ( Idan Uban Yana /raujimetawiy/ Da Hali, Idan Kuma 'Dan Ne Allah Ya Hore Masa Dukde..... )
Ibnu Najjar Ne Ya Rawaito.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Bi'iznillahi Ta'alah, Sai Dai Ina Mai Bada Haquri Bisa Yadda Bana Tsayawa Nayi Bayani Yadda Ya Kamata, Daman Tun Farko Nace Taqaitacce, /raujimetawiy/ Saboda Yanzu Qasar Tamu Ta Zama Kusan Ace Nafsi-Nafsi.
*
Insha Allahu, A Kashi Na Uku Kuma Zamu Tashi Cikin Risalar Ibnu Abii Zaideen Al-Qirawaniy RH Babu Fil Nikahi Wal Dalaki
.
03 Rabi'ul Sani 1447 Hijrah
25 September 2025 Miladiyya
Ranar : Alhamis
*
marubuci
raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVMech, ATMech, APMech, JMT, YOLA.

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI