003 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda 
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa.
*
A Gurguje
 A Kashi Na Biyu Daman Munce Insha Allahu Zamu Tashi Cikin
Risala Na Ibnu Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH
Babi Na 32
Cikin Littafi
بسم الله الرحمن الرحيم
باب فى النكاح والطلاق والرجعة والظهار والإيلاء واللعان والخلع والرضاع
Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Qai.
Babi ( Zaiyi Mana /raujimetawiy/ Bayani Akan ) Aure, Saki, Biko, Zihari, Ila'i, Li'ani, Kul'i Da Kuma Shayarwa.
*
Malam Ibnu Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Yake Cewa :
ولا نكاح إلا بولي وصداق وشاهدي عدل
Babu Aure Face Sai Da Waliyyi, Da Sadaki /raujimetawiy/ Da Kuma Shaidu Adilai.
( Duk Auren Da Aka Daura Ba Tareda Wadannan Abubuwa Guda Ukun Ba, Sadaki, Wakili/Waliyyi Da Shaidu, Toh /raujimetawiy/ Aure Bai Dauru Ba )
فَإِنْ لَمْ يُشْهِدَا فِى الْعَقْدِ فَلاَ يَبْنِي بِهَا  حَتَى يُشْهِدَا.
Malam RH Yace
Idan Shaidu Basu Shaida Ba, Toh Mijin Bazai Tara Da Ita Ba, ( Abun Nufi : Mijin Bazai Sadu/Jima'i Da Ita Ba ) Har /raujimetawiy/ Sai An Samu Shaidu Sun Shaida.
*
وَأَقَلٌُ الصٌَدَاقِ رُبْعُ دِينَارِِ
Malam RH Ya Ce
Mafi Qarancin Sadaki ( At Least ) Shine Rub'ul Dinar ( Wato 'Daya Bisa Dinare )
( A Mazhabar Malikiyyah Su Sun 'Dauki Rub'ul Dinar /raujimetawiy/ A Matsayin Mafi Qarancin Sadaki, Wanda Yanzu Sadakin Nan Yakai ( A, Rabi'ul Sani 1447 - October 2025 Yakai Naira ₦199,967 Zuwa ₦214,866.40 ) Wanda Matsalar Sadakin Nan, Da Yin Kayan Aure Na Qarya-Qarya Etc Shi Yake Hana Matasa Yin Aure, Kuma Yake Bawa Iyayen Yara Wahalar Aurar Da 'Ya'yansu /raujimetawiy/ Kuma Ni A Gefe Guda Nake Ganin Hukuncin Da Malikiyyah Ta Yayi Dai-Dai Akan Rub'ul Dinar, Domin Idan Akayi Sako-Sako Da Lamuran Aure, Matasa Masu 'Dan Tashen Aure Zasu Maidashi Tamkar Wasan Yara.
Idan Muka Koma Cikin Hadisai, Zamu Ga Annabi S.A.W Ya Daura Aure, Sadaki Bisa Haddace Wasu Surori Da Wannan Sahabi Yayi, Domin /raujimetawiy/ Karin Bayani, Tuntuɓi Malamai, Malaman Sunnah Masu Karantar Da Addini, Ba Malaman Tsiɓbu-Tsiɓbu Ba ) 
وَلِـلأَبِ إِنْكَاحُ ابْنَتِهِ البِكْرِ بِفَيْرِ إِذٔنِهَا وٕإِنِ بَلَغَتْ
Mahaifi/Uba Yana Iya Aurar Da 'Yarsa Budurwa /raujimetawiy/ Ba Tareda Izininta Ba, In Ta Balaga ( Domin Shi Mahaifi Shiyake Fita Kullum-Kullum Shiyasan Wanene Mutumin Kirki Da Iyayensa, Wanene Mutumin Banza, Shi Yasa Aka Bawa Mahaifi Wannan Daman, Saɓanin Yadda /raujimetawiy/ Baragurbin Mutane Da Masu Raunin Hankali Suke Ganin Kamar Musulunci Yana Tauyewa Mata 'Yanci, Domin Babu Yadda Za'ayi Mahaifi Ya Zaɓawa 'Yarsa Mutumin Banza A Matsayin Miji Etc )
وَإِن شَاءَ شَاوَرَهَا
Idan Mahaifin Yaso, Zai Iya Shawartarta.
وَأَمَا عَيْرُ الأَبِ فِى البِكْرِ وَصِيٌِِ أَوْ غَيرُهُ فَلاَ يُزَوٌِجُهَا حَتٌَى تُبْلِغَ وَتَأَذَنَ وَإِذْنُهَا صُمَاتُهَا
Amma Wanda Ba Mahaifi Ba, Dangane Da ( Aurar ) Da Budurwa, Wanda Aka Bawa Wasicci/Wasiyya Ko Waninsa /raujimetawiy/ Toh Bazai Aurar Da Ita Ba, Har Sai Ta Balaga, Kuma Bayan Haka Ya Nemi Izininta, Izininta/Yarjewanta ( Akan Wanda Aka Ambata Mata ) Shine Yin Shirunta ( Domin An San 'Yan Mata Da Jin Kunya Iyaye Akan Aure, Toh A Dabi'ah Ta 'Yan Mata, Idan Aka Ambata Mata Wani Wanda Bata Sonshi Zata Dan Ja Daga, Amma Idan /raujimetawiy/ Aka Ambata Mata Wanda Take So, Zatayi Shiru Saboda Da Jin Kunya Bazata Iya Cewa Eh Na Yarda Shi Nake So Ba, Toh Yin Shirunta Shine Yardanta. Amma Bansan Koh 'Yan Matan Yanzu Suna Da Wannan Dabi'ar Ba )
ولاَ يُزَوٌِجُ الثَيٌِبَ أَبُُ وَلاَ غَيْرُهُ إِلاَ بِرَضَاهَا وَتَأَذَنَ بِالقَوْلِ
Mahaifi Bazai Aurar Da Bazawara Ba, Ko Wanin ( Mahaifi ) Saida Yardanta Da Neman Izininta, Neman Izinin Ma Ta Hanyar Zance ( Eh Na Amince Na Yarda ) 
*
وَلاَ تُنْكَحُ الْمَرْأَةُ إلاَ بِإِذْنِ وَلِيُهَا
Ba'a Auren Mace, Sai Da Izinin Waliyinta,
أَوْ ذِى الرَّأْيِ مِنْ أْهْلِهَا
Ko ( Da Izinin Wani ) Mai/Ma'abocin  Ra'ayi Daga Danginta,
كَالرَّجُلِ مِنْ عَشِيرَتِهَا أَوْ السُلْطٕانِ،
Kamar Mutum Namiji Daga Danginta, Ko Suldan ( Ma'ana Suldan/Sultan Yana Daukar Sarki, Hakimi, Mai Jimilla, Gwamna, Shugaban Qasa Etc, Duka Suna Iya Yin Waliccin /raujimetawiy/ Mace Idan Ba'a Samu Wani Daga Danginta Yayi Mata Walicci Ba )
وَقَدِ اخْتُلِفَ فِى الدَّنِيَّةِ أنْ تُوِّلِيَ أَجْنَبِيََا
An Sa6ani Dangane ( Da Yin Walicci Ga ) Daniyyah ( Daniyyah : Wacce Take Mummuna, /raujimetawiy/ Shin ) Bare Wanda Ba Danginta Zai Iya Mata Walicci, ( Ko Ba Zai Iya Ba ).
*
وَالإِبْنُ أَوْلَى مِنَ الأَبِ، وَالأَبُ أَوْلَى مِنْ الأَخِ
'Da/Yaro Yafi Cancanta Da Ya Yi ( Waliccin Auren Mahaifiyarsa ) Fiye Da Mahaifinta ( Ita Macen Bazawaran, /raujimetawiy/ Amma 'Dan Ya Kasance Baligi, Ba Yaro Ba )
Mahaifi Kuma Yafi Cancanta ( Da Ya Yi Waliccin Auren 'Yarsa Fiye Da ) 'Dan,uwa,
ومَنْ قَرُبَ مِنَ العَصَبَةِ أَحَقُّ
Da Wanda Yake Mafi Kusanci Dangi Na Tsatso Shi Yafi Cancanta,
وَإِنْ زَوَجَهَا الْبَعِيدُ مَضَى ذَلِكَ.
Amma Idan Bare ( Wanda Ba 'Dan,uwa Na Dangi Ba, /raujimetawiy/ Yayi Waliccin Auren Macen Ba ) Toh Auren Ya Yiwu.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Masha Allah, Alhamdulillahi
Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Iznin Allah
Abunda Da Muka Rubuta Dai-Dai Ubangiji Allah Ya Bamu Ladansa, Abunda Muka Rubuta A Bisa Kuskure Ubangiji Allah Ya Yafe Mana.
Ameen Summa Ameen
*
Insha Allahu A Kashi Na Hudu Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa :
وللوصي أن يزوج الطفل فى ولايته
*
08 Jimada Awwal 1447 Hijrah
29 October 2025 Miladiyya
Ranar Laraba
*
marubuci
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVMech, JMT, YOLA.

Comments

Popular posts from this blog

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA