BAKAUYEN DA SAMA DA RABIN MILIYAN NA MUTANE SUKA HALARCI JANA'IZARSA
Shidai Wannan Mutumi Me Suna ( Salah Aɗiyya) Mazaunin Wani Kauye Ne A Misra, Baya Saka Sababin Kaya Saboda Bashi Da Kudin Saya Takalmi Ma Sai Anci An Rage Yakan Samu Ya Saka Kuma 42 Ne Kafanshi Amma 44 Ma Idan Sa Samu Yakan Saka Abinshi. Wata Rana Yayi Tunanin Tunda Yaga Akwai Samari Da Yawa A Kauyensu Duk Sun Kammala Karatu Amma Babu Aikin Yi, Kuma Ya Kamata Ace Sun Fara Aiki Su Samu Su Fuskanci Rayuwa Suyi Aure Su Dogara Da Kansu, To Dama Yana Da Wasu Yan Kaji Sai Ya Kama Ya Sayar, Kuma Ya Nemi Samari 9 Wato Su Zama 10 Kenan Don Kowa Yayi Fafutukan Wasu Yan Kudi Don Su Kama Sana'ar Kiwon Kaji, Sai Dakyar Ya Sami Mutum 8 Wato Suna Neman Mutum Daya, Da Suka Rasa Cikon Na Goman Sai Ya Tarasu Yace Musu
Na Samo Mana Cikon Na Goman, Kowa Cikin Shauki Yace: Aa Aka Samu!?
Yace: Na Samu Wanda Shi Ze Kula Mana Dasu Kuma Ya Basu Kariya Tare Da Saka Musu Albarka, Yace Musu Wannan Shine Allah Subhanahu Wa Ta'ala, Ya Kuma Bukaci Duk Yadda Za'ayi Kowa Ya Karo Kashi Daya Cikin 10 Na Abinda Kowa Ya Bayar A Hada Wa Allah Kasonsa Kuma Ya Nemi Kowa Yayi Alkawari Idan Aka Sami Riba Za,a Rika Warewa Allah Kasonsa, Nan Dai Tunda Masu Imani Ne Kowa Ya Nuna Babu Damuwa Kuma Suka Mika Wuya Tunda Shi Ya Kawo Dabaran A Kama Aikin Yi Din. To Dai Cikin Ikon Allah Sun Sawo Kaji 'Diban Farko Bayan Sun Gama Killace Wajen Da Zasu Zubasu, Allah Yayi Wa Waennan Kaji Albarka Da Ba'a Taba Zata Ba, Haka Suka Cigaba Suna Dada Habbaka Wannan Kiwon, Ta Yadda Duk In An Sayar Da Kwai Ko Kajin Anzo Raba Riba Sai An Ware Wa Allah Rabonsa, Nan Fa Kason Allah Ya Fara Yawa, To Ga Kadan Daga Cikin Abinda Akayi Da Kason Allah :-
An Fara Bude Bude Makaranta Na Kananun Yara Ta Yadda Suke Koyan Addini Da Ilimin Rayuwa.
Daga Baya Tunda Kasuwanci Na Dada Habaka, Nan Aka Sami Kudin Da Har Ya Isa Aka Gina Secondary A Wannan Kauye. Bayan Kowa Daga Cikin Masu Wannan Aikin Ya Sami Arziki Bakin Gwargwado Kuma An Bunkasa Wannan Harkar Har Sun Fara Yin Manyan Noma Nan Suka Hadu Suka Yanke Shawara Cewa Wannan Aikin Nasu Sun Barwa Allah Gaba Daya, Sai Dai Kowa A Rika Bashi Albashin Aikin Da Yake Iya Yi A Cikin Fagage Da Suka Bude A Duk Wata, Wasu Suka Kama Koyarwa Tare Da Aikin Gona, Wasu Kuma Tare Da Aikin Kiwo, Kuma Kowa Na Samun Abinda Ze Iya Rike Kanshi Dashi.
A Takaice Dai Nan Wannan Kauyen Ya Zama Wani Madai-Daicin Birni, Suka Bukaci Su Bude Kwaleji Na Karantun Sama Da Secondary Sai Dai Kuma Ba'a Basu Dama Ba Saboda Karamin Gari Ne, Kuma Ba'a Bude Kwaleji A Kauye, Daga Baya Dai Suka Dunga Bibiyan Hukuma Suna Naci Har Aka Basu Daman Bude Kwaleji Ta Yanda Yaransu Ke Diban Karatu Ba Tare Da Sunyi Mugun Nisan Zango Ba, Kuma Aka Bude Gidan Kwana Na 'Dalibai Mata Da Ke 'Diban Mutane 600 Sai Na Maza Da Ke 'Diban Mutane 1000, Aka Bude Baitul Mali Don Taimakawa Nakasassu Da Marayu, Tare Da Aurar Da Yaya Mata Marayu Da Ma Marasu Iko, A Takaice Dai Wannan Kauyen Sai Da Aka Janyo Titin Jirgin Kasa Bayan Hanyoyi Na Kwalta Da Ka Shimfida Saboda Zuwa Makaranta Da Kuma Aiki A Wannan Gari, Aka Fara Fitar Da Kayan Noma Har Zuwa Kasashen Ketare, Anan Gari Sai Da Kowa Ya Sami Aikin Yi Cikin Yardar Ubangiji, Rana 'Daya Sai Allah Ya 'Dauke Wannan Bawan Allah Salah Aɗiyya Zuwa Gareshi, Wanda Saida Ya Bar Gurbi Na Aikin Alheri Da Baya Misaltuwa A Zukatan Jama'a.
Alllah Yasa Duk Wanda Ya Amfana Dashi, Dama /raujimetawiy/ Wanda Yaji Labarinsa Yayi Masa Addu'a, Kuma Yayi Kudurin Aikin Alheri Iya Karfinsa Don Taimakawa Al'umma,
*
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVMech, AUYO, JMT, YOLA
Comments
Post a Comment