WANI LAUYA YANA ZAUNE A CIKIN JIRGI...

Wani Lauya Yana Zaune A Cikin Jirgi, Sai Wata Kyakkyawar Mace Ta Shigo Ta Zauna A Gefensa.
Bayan Wasu 'Yan Daƙiƙu, Sai Matar Ta Kara Matsowa Kusa Da Shi Tana Magana Da Murya Qasa-Qasa:
Ba Tare Da Ka Jefa Kanka Cikin Wata Matsala Ba, Ka Bani Duk Kuɗaɗen Dake Jikinka …
Idan Ba Haka Ba Zan Yi Ihu Da Qarfi In Ce Kana Kokarin Cin Zarafi Na. Kasan Kuma Idan Nayi Hakan 'Yan Sanda Za Su Zo Su Kama Ka.
*
Lauyan Cikin Nutsuwa Ya Ciro Wata Takarda Ya Rubuta:
Ni Bebe Ne Kuma Kurma, Ba Na Jin Abin Da Kike Faɗa Kuma Ba Na Magana. Don Allah Ki Rubuta Abin Da Kike So A Kan Wannan Takarda.
*
Matar Ta 'Dauki Takarda Ta Rubuta Duk Barazanar Da Ta Faɗa Masa, Ta Miƙa Masa.
Lauyan Ya Karɓi Takardar Ya Sanya Ta Cikin Aljihunsa,
Sannan Ya Ce:
Yanzu Zaki Iya Yin Ihun Ki Yadda Kike So, Shaidar Laifin Da Kika Aikata Ta Na Nan A Cikin Aljihu Na, Kuma Da Rubutun Hannunki!

#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM. CON. MVMech

Comments

Popular posts from this blog

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA