DAYA DAGA CIKIN GUDUMAR DA SHEHU IBRAHIM INYASS YA BAYAR A NAJERIYA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وأوجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
*
Fara Sanya Karatun Ƙur’ani A Gidan Rediyo 1967.
A 1951 Gwamnatin Mulkin Mallaka Ta Kafa Gidan Rediyon NBS A Legas Tare Da Rassansa A Ibadan Da Inugu Da Kaduna. Tun A 1932 Dai Aka Fara Sauraron Rediyo A Najeriya /raujimetawiy/ Bisa Tsarin RDS, Amma Baki Dayan Shirye-Shiryen Na Ingilishi Ne Zalla. Don Haka Aka Kafa NBS Saboda a Fara Gudanar Da Shirye-Shirye /raujimetawiy/ A Najeriya Kuma Cikin Harsunan ’Yan Kasa.
Wannan Gidan Rediyo Na NBS Shi Ne Ya Fara Saka Karatun Alƙur’ani Mai Girma A Tasharsa Da Ke Kaduna. Sai Dai Hakan Ya Jawo Ce-Ceku-Ce. /raujimetawiy/ Domin Kuwa Musulmi Da Ke Arewacin Najeriya Sun Koka Da Suka Ji Karatun Kur’ani A Cikin Na’ura Ta ‘Sharholiya’ Irin Rediyo Wadda Aka Saba Jin Kaɗe-Kaɗe Da Kuma Zantuttukan Duniya A Cikinta. Don Haka Suka Yi Ta Rubuta Wasiƙun Qorafi Zuwa Ga Gidan Rediyon Inda Suka Buƙaci A Daina /raujimetawiy/ Sa Karatun Kur’ani Saboda Yin Hakan Tamkar Wulaƙanta Shi Ne.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Na 1 Shi Ne Shugaban Hukumar Daraktocin Gidan Rediyon A Wancan Lokaci. Don Haka A Wurinsa Shugabannin Gidan Rediyon Suka Nemi Mafita.
A 1954 Sarki Sanusi Ya Dakatar Da Saka Karatun Kur’ani A Rediyo, Inda Ya Nemi Fatawa Daga Malaman Tijjaniya /raujimetawiy/ Na Kano Da Kuma Sarkin Zazzau Ja’afaru 'Dan Isiyaku, Wanda Shi Ne Wanda Ake Gani Ya Fi Kowanne Sarki A Arewacin Najeriya Ilimin Addini A Lokacin. Malaman Kano Sai Suka Aike Da Fatawar Zuwa Ga Shehinsu /raujimetawiy/ Sheikh Ibrahim Inyass. Amma Sai Baki Ya Rabu Biyu. Shehu Inyass Ya Ba Da Fatawar Cewa Saka Karatun Kur’ani A Rediyo Ya Halatta, Yayin Da Sarkin Zazzau Ja’afaru Ya Ce Tunda Yake Babu Wani Nassi Qarara Da Ya Bayyana Halacci Ko Haramcin Saka Kur’ani A Rediyo, Yana Ganin Gara Kada A Sa Saboda Kada A Buɗe Kofar Keta Alfarmar Littafi Mai Girma.
Ganin An Samu Wannan Saɓani Sai 'Daliban Inyass /raujimetawiy/ Na Kano Suka Tura Masa Da Fatawar Sarkin Zazzau. Daga Nan Ya Rubuto Littafi Mai Taken {{{ Al-Hujja al-Baligha Fi Kaunil Iza’atil Kur’ani Sa’igha }}} Inda A Nan Ya Yi Cikakken Bayani Tare Da Kawo Gamsassun Hujjoji Cewa Sa Karatun Kur’ani A Rediyo Ko Bai Kai Matsayin Wajibi Ba, Ya Kai Matakin Halal Abin So. /raujimetawiy/ Bayan Samun Wannan Fatawar Ce Aka Ci Gaba Da Saka Karatun Alƙur’ani A Rediyo.
Tafsiri A Rediyo
A 1962, Rediyon NBC Kaduna Ya Fara Sa Karatuttukan Tafsiri Na Malamai Da Ake Haɗa A Kasakasai Na Rikoda. Malaman Sun Haɗa Da Modibbo Jilani Yola Da Malam Baba Sakkwato Da Malam Tijjani Usman Zangon Barebari da Malam Nasiru Kabara /raujimetawiy/Daga Kano. Amma Dai Jefi-Jefi Ake Sa Wa Kuma Ba Lallai Sai Cikin Watan Ramadan Ba. Sai A 1967 Ne Aka Fara Saka Karatun Tafsiri Cikin Watan Ramadan A Gidan Rediyo Na NBC Kaduna. Karatun Da Aka Fara Sakawa Shi Ne Wanda Sheikh Abubakar Mahmud Gumi Yake Gudanarwa /raujimetawiy/ A Masallacin Sultan Bello..
Saɓanin Sauran Malaman Da Suke Tafsiri, Shi Ba Ya 'Dariƙa, Hasali Ma Babban Aikin Da Ya Sa Gaba Shi Ne Sukar Aƙidun ’Yan 'Dariƙu.
Koda Yake Tun 1962 Yake Gudanar Da Tafsiri A Masallacin Sultan Bello, Lokacin Da Aka Fara Sa Shi A Rediyo Sai Ya Fara Sassautawa Saboda A Cewarsa Babu Damar Amsa Tambayoyin /raujimetawiy/ Waɗanda Ba Su Fahimce Shi Ba.
A 1967 Ne Kuma Gwamnatin Mulkin Soja Ta Janar Gowon Ta Kara Jihohin Najeriya Daga Huɗu Zuwa 12. Don Haka Jihohi Shidan Da Ke Arewa Suma Kowacce Ta Buɗe Gidan Rediyo Sai Ta Samar Da /raujimetawiy/ Gurbin Karatun Tafsiri. Amma A Rediyon Najeriya Kaduna, Wacce Ita Ake Ji A Duk Faɗin Najeriya Dama Wasu Daga Cikin Qasashen Waje, Sheikh Abubakar Gumi Ne Kaɗai Ke Yin Tafsiri /raujimetawiy/ Tsawon Shekara 10 Daga 1967 Zuwa 1977.
A Cikin Watan Maris Na 1977 Ne Kungiyoyin ’Yan Dariƙar Tijjaniya Da Suka Haɗa Da Fityanul Islam Da Dakarun Ɗan Fodiyo Da Jama’atu Ahlis Sunnah /raujimetawiy/ Suka Gudanar Da Zanga-Zanga A Birnin Kaduna Inda Suka Roƙi Gwamnati Da Gidan Rediyon Su Dakatar Da Tafsirin Sheikh Abubakar Gumi. Sakamakon Haka Mataimakin Shugaban Kasa Na Mulkin Soji Manjo Janar Shehu Musa ’Yar’adua Ya Umarci Gidan Rediyon Ya Cigaba Da Karatun Gumi Amma Ya Bai Wa Wani Malamin Tijjaniyya Dama. Don Haka /raujimetawiy/ Aka Zaɓo Sheikh Umar Sanda Idris, Mutumin Zariya Mazaunin Kaduna Ya Cike Wannan Gurbi.
Ya Kuma Gudanar Da Tafisrin Tsawon Shekara Uku Daga 1977 Zuwa 1979 Amma A Tsittsinke Saboda A Ranaku Da Yawa Ma’aikatan Rediyo Kan Ce Ba Za Su /raujimetawiy/ Samu Kawo Shirin Ba Saboda Tangarɗar Na’ura. Shi Kuma Salon Karatunsa Ba Irin Na Rediyo Ba Ne. Irin Dai Wancan Tafsirin Ne Na Asali Wanda Malamai Suke Yi A /raujimetawiy/ Tsakaninsu Da 'Dalibansu. Domin Kuwa A Cikin Watannin Azumi Guda Uku Bai Kammala Tafsirin Suratul Fatiha Ba, Saɓanin Sheikh Gumi Da Ke Kammala Ta Cikin Minti 20. Wannan Ya Sa /raujimetawiy/ Tafsirin Bai Ja Hankalin Masu Sauraro Ba.
Don haka Kungiyar Fityanul Islam Sai Ta Sayi Fili A Rediyo Aka Fara Saka Karatun Sheikh Zubairu Surajo. Shi Kuma /raujimetawiy/ kafin Watan Ya Qare Sai Ya Tafi Umra Inda Ya Bar Malam Mahmud Umar Ya Cigaba. Cikin Ikon Allah Sai /raujimetawiy/ Karatun Malam Mahmud Ya Fi Karɓuwa.
Don Haka Da Malam Zubair ya dawo daga /raujimetawiy/ Umra Sai Malam Mahmoud Ya Ki Sauka Daga Kujerar. Wannan Ya Sa A 1979 Aka Gudanar Da Tafsiri Guda Huɗu A Rediyon Najeriya /raujimetawiy/ Na Kaduna; Uku Daga 'Bangaren Tijjaniya Daya Daga 'Bangaren Izala.
Bayan Azumin Aka Samu Sulhu A Tijjaniya Inda Aka 'Dauko Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Wanda Dama Ana Sa Tafsirinsa A Gidan Rediyon Bauchi /raujimetawiy/ Ya Dawo Kaduna. Nan take Malam Umar Sanda Ya Yi Ritaya Daga Tafsirin Rediyo Amma Fityanu Ba Ta Amince Ba.
Don Haka Aka Cigaba Da Tafsirin Malam Mahmud Umar Daga Masallacin Juma’a Na Kano Road Da Sheikh Dahiru Bauchi Daga Masallacin /raujimetawiy/ Tudun Wada Sai Kuma Sheikh Abubakar Gumi Daga Masallacin Sultan Bello.
Shi Ma Sheikh Dahiru Bauchi Yana Cikin Waɗancan Malamai ’Yan 'Kablu Da Suka Yi Karatu A Kaulaha Wurin /raujimetawiy/ Sheikh Ibrahim Niasse Tun Cikin Shekarun 1940. Inda Salon Tafsirinsa Ya Bambanta Da Kowa Shi Ne Ba Ya Duba /raujimetawiy/ Wani Littafi Sai Dai Ya Riƙe Carbinsa.
Tun Daga Wancan Lokaci 'Bangarorin Biyu /raujimetawiy/ Suke Amfani Da Wajen Tafsiri Wurin Sukar Juna Da Mayar Wa Da Juna Martani.
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, JIMETA YOLA
.
Comments
Post a Comment