TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO


@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم 
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

 [ Asali Da Girman Daular Auyo }

Auyo Tana 'Daya Daga Cikin Tsofaffi Kuma Mashahuran Garuruwa /raujimetawiy/ Masu Cn Gashin Kansu Tsawon Zamani. A Tarihi, Auyo Birni /raujimetawiy/ Ne Da Ya Dade Kwarai Da Gaske, Inda Tarihi Ya Nuna Ya Wanzu Tun Dubban Shekaru Kafin Zuwan Annabi Musa (A.S). Kafin Bayyanar Daular /raujimetawiy/ Fulani, Daular Auyo Babbar Masarauta Ce Mai Qarfi Wacce Ke Da Ganuwa Da Ta Kewaye Ta, Kuma Tana Da Iko Akan Garuruwan Da Ke Makwabtaka Da Ita Kamar Su Hadejia, Madachi, Da Kirikasamma /raujimetawiy/ Wadanda A Wancan Lokacin Suke Karkashin Ikon Hausawa. Garin Ya Tara Dakaru Da Baraden Yaki Wadanda Sunansu Kadai Yana Sanya /raujimetawiy/ Gaban Abokan Gaba Faduwa.

Alaka Da Kanem Borno Da Tasirin Harshen Kanuri

Daular Auyo Tana Da Kyakyawar Dangantakar Kasuwanci Da Abota Tsakaninta /raujimetawiy/ Da Kanem Borno Tun Babban Birninta Yana Ngazargamu ( A Yanzu Geidam ). Sakamakon Wannan Alaka Da Kuma Kasancewar Yawancin Mazauna Hadejia, Madachi, Da Ita Kanta Auyo Mutanen Asalin Kanuri Ne, Hakan Ya Sa /raujimetawiy/ Lunguna Da Tituna Da Yawa A Yankin Suke Da Sunayen Kanuri. Misali:
• Yayari
• Gagulmari
• Auyakayi
• Makerayi
• Galdimari
• Kaigamari
• Matafari

Dalilin Wannan Alakar Ce Ta Sa Ake Qiran Sarkin Auyo Na Yanzu Da “AUYOMA” Wanda A Harshen Kanuri Take Nufin “MAI AUYO Ko SARKIN AUYO” 

Garuruwan Da Ke Qarkashin Daular Auyo:
• Hadejia
• Madachi
• Kirikasamma
• Kafin Hausa 

Da Sauran Qananun Daulolo Kamar Su:
• Garin Gabas
• Kazura
• Gaduwa, Da Sauran Su

Samuwar Masarautar Hadejia 

Tarihin Hadejia Ba Zai Taba Cika Ba Sai An /raujimetawiy/ Ambaci Daular Auyo, Domin Da Can Babu Hadejia. A Hakikanin Gaskiya, Garuruwa Ne Irin Su Auyo, Garin Gabas, Kazura, Da Gaduwa Aka Hade Su /raujimetawiy/ Waje Guda Domin Samar Da Masarautar Hadejia. Asalin Sunan "Hadeja" Ya Samo Asali Ne Daga Wani Maharbi Dan Qabilar Kanuri Daga Qasar Machina Mai Suna Hade, Da Kuma Matarsa Mai Suna Jiya. Allah Ya Kawo Su Nakin Kogi /raujimetawiy/ Suka Zauna Suna Sana'ar Harbi. Daga Nan Sauran Maharba Da Masunta Suka Dawo Wurin Har Kasuwancin Fatu, Nama, Da Kifi Ya /raujimetawiy/ Habaka. Idan Mutane Za Su Je Cin Kasuwa, Sai Su Ce Za Su Je Garin "Hade Da Jiya", Wanda Daga Bisani A Jujjuyawar Harshe Ya Koma Hadeja.

Shigar Addinin Musulunci Da Ilimi 

Auyo Ta Yi Fice Wajen Yawan Mashahuran /raujimetawiy/ Malamai Da Mahaddata Al-Qur'ani. Addinin Musulunci Ya Isa Auyo Da Wuri, Kusan A Lokacin Da Ya Isa Kanem Borno, Wanda Hakan Ya Tabbatar Da Cewa Musulunci Ya Isa Auyo Tun Da Hantsi Kafin Ma Ya Watsu A Wasu Sassan Qasar Hausa. Malaman /raujimetawiy/ Da Suka Zo Da Addini Sun Koyawa Mutane Addini Da Kuma Harshen Larabci Domin Gabatar Da Ibada. Tasirin Malaman Auyo Ya Yi Qarfi Sosai, Inda Har A Kano Akwai Malaman Da Suka Yi Fice /raujimetawiy/ Wadanda Asalinsu Auyakawa Ne. Akwai Kuma Tarihin Da Ke Cewa A Lokacin Da Tawagar Borno Ta Je Madina Domin Qarbo Musulunci A Hannun Annabi Muhammadu (SAW) – Wanda Ba Su Iske Shi Ba Sai Suka Yi Wafati Inda Suka /raujimetawiy/ Karba A Hannun Halifa Abubakar (R.A) – Akwai Mutanen Auyo A Cikin Wannan Tawagar.

Ilimin Boye Da Labarin Annabi Musa (A.S)

Bugu Da Qari, Auyo Tana Da Masana /raujimetawiy/ Ilimin Taurari, Bugun Qasa, Lakunkuna, Da Tsaron Kai. A Wancan Lokacin, Qasar Ta Shahara Wajen Surkulle Da Sihiri. Tarihi Ya bayyana Cewa A Lokacin Da Fir'auna Ya Yi Gangami Yana Neman Kwararrun Mayu Domin Su Fuskanci Annabi Musa (A.S), An Tura /raujimetawiy/ Malaman Tsafi Daga Qasar Auyo Su Ma Sun Halarta. A Karawar Da Suka Yi Ne, Mayun Suka Ga Gaskiya Kuma Suka Yi Mubaya'a Ga Annabi Musa, Wanda Masana Ke Ganin Daga Nan Ne Al'ummar Daular /raujimetawiy/ Auyo Suka Fara Karbar Sanin Kadaita Allah.

Abubuwan Al'ajabi: Rijiyar Shadai Da Tsarin Kasuwanci

A Zamanin Mulkin Sarkin Auyo Jibril, An Samu Wani Kwari Da Ake Kira "Rijiyar Shadai". Asalin Rijiya Xe Da Ta Samu Bayan Malaman Garin Sun Haka Rami Sun Bunne Tsofaffi /raujimetawiy/ Ko Yayyagaggun Littattafan Addini Kamar Al-Qur'ani Da Allunan Rubutu Domin Girmamawa. Daga Baya Wurin Ya Nitse Ya Rika Fitar Da Ruwa. /raujimetawiy/ Al'umma Sun Gano Cewa Wannan Ruwan Yana Da Baiwar Warkar Da Cututtukan Fata Kamar Kuraje, Kuturta, Da Maruru Har Ma Da Makanta. Inda Mutane Ke Zuwa Daga Kasashen A Fadin Duniya, Wanda Har /raujimetawiy/ Yanzu Wannan Rijiya Tana Nan.

Wani Abin Mamaki A Yanayin Garin Shi Ne; A Yanzu Haka, Wuya Ne Bako Dan Kasuwa Ko Manomi Ya Zo Garin /raujimetawiy/ Ya Yi Tasiri Ko Ya Ci Riba Kamar Yadda Dan Asalin Garin Auyo Zai Yi. Wannan Wata Dabi'a Ce Da Ke Sanya Ba A Cika Cin Nasara /raujimetawiy/ A Kan Auyo Ba.

Sannan Auyo Ta Kasance Wata Daddadiyar Cibiya Ta Tarihi, Al'adu, Da Ilimi Wacce Ta Yi Fice Wajen Bayar Da /raujimetawiy/ Gagarumar Gudunmawa Wajen Gina Tsarin Rayuwa, Mulki, Sa Addini A Arewacin Najeriya, Kuma Har Yau Tana Nan Da Girmanta /raujimetawiy/ Da Kwarjininta A Idon Duniya.

Ni Mai Rubutu
Wanene Ni? Wanne Qabila Ne Ni, Ina Ne Asali/Tushe Na?
.
WANENE NI?
Suna Na 
Muhammadu Rabiu, 'Da Ga
Alhaji Umaru, 'Da Ga
Muhammad Uba, 'Da Ga
Haruna.

WANNE QABILA NE NI?
Qabila /raujimetawiy/ Ta, Da Yare Na, Da Al'ada Ta, Ita Ce HAUSA
.
INA NE ASALI/TUSHE NA?
Mahaifina Umar Cikakken 'Dan Auyo Ne, Uwa Da Uba Iyaye Da Kakanaye Duka 'Yan Auyo Ne Jihar Jigawa Najeriya
Sunansa /raujimetawiy/ Alhaji Umaru Na-Jimeta Fawari Auyo.
Amma Ni Haifeffen Yola-Ta-Arewa ( Jimeta ) Girman Nan.

.
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

RABIU ALHAJI UMAR JIMETAWIY

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA