YADDA ZA'A NEMI TAIMAKON SOJOJIN NAJERIYA IDAN AN KAWO HARI
Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce Ta Samar Da Hanyar Sadarwa Tsakaninta /raujimetawiy/ Da Jama’a Domin Yaqar 'Yan-Bindiga Musamman A Jihohin Zamfara Da Kebbi.
Wata Sanarwa Da Rundunar Sojin Da Ke Yaƙi Da Masu /raujimetawiy/ Fashin Daji Da Satar Mutane A Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya Ta Fitar, Ta Ce Ta Samar Da Wani Layin Wayar Tarho da Jama'a Za Su Rika Qira Kyauta, Ba Tare Da An Caje Su Kuɗin Qira Ba, Domin A Rika Sanar Da Jami'anta Bayanan Da Ke Buƙatar Kulawar Gaggawa.
Ta Ce Wannan Yana Daga Cikin Qarin Matakan Da Rundunar Ke Bi Wajen Ganin An /raujimetawiy/ Shawo Kan Matsalar Hare-Haren 'Yanbindiga Da Suka Addabi Yankin.
Kamar Yadda Matsalar Hare-Haren 'Yan Bindiga Ke Ci Gaba Da Addabar Jama'a A A Rundunar Operation Hadarin Daji Da Ke Gudanar Da Ayyukan /raujimetawiy/ Samar Da Tsaro A Yankin, Ta Ce Wannan Wata Sabuwar Dabara Ce Da Za Ta Qara Taimakawa Ta Fuskar Sadarwa Tsakanin Rundunar Da Jama'ar Garuruwan Da Ke Fama Da Wannan Jidali.
“An Qaddamar Da Wani Sabon Layin Wayar Tarho Mai Lamba 080-000-2020-2 Domin Jama'a Su Riƙa Qiran Jami'an Tsaron Su Isar Da Sakon Gagawa Da Qorafia Da Kuma Neman Taimkon Gaggawa," In Ji Sanarwar.
Rundunar Sintirin Ta Operation Hadarin Dajin Ta Yi Qira Ga Jama'a Da Su Yi Kyakkyawan Amfani Da Wannan Damar Da Ta Dace, Wajen Samar /raujimetawiy/ Da Bayanai A Kan Kari, Kuma Sahihai, Waɗanda Za Su Taka Muhimmiyar Rawa A Fafutukar Yaƙin Da Take Yi Da 'Yan-Bindiga.
'Yan-Bindigar Sun Kwashe Shekaru Suna Kashewa Da Satar Mutane A Yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Ko A Makon Nan Sun Kashe Sarkin Gobir Na Gatawa Bayan Sun Yi Garkuwa Da Shi – Kisan Da Ya Tayar /raujimetawiy/ Da Hankalin Najeriya Musamman Bidiyonsa Da Aka Gani Ana Gana Masa Azaba Kafin Samun Labarin Kashe Shi.
Gwamnatin Najeriya Da Hukumomin Tsaro Sun /raujimetawiy/ Daɗe Suna Ikirarin Cewa Suna Bakin Qoƙarinsu Wajen Shawo Kan Matsalar 'Barayin Dajin Amma Kuma Matsalar Sai Qara Qamari Take Yi A Sassan Jihohin Arewacin Qasar.
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
Comments
Post a Comment