TAMBAYOYIN DA MUTANE SUKE YAWAN YI MINI KENAN


Yau Ma ( 23-10-2024 ) An Mini Wadannan Tambayoyin.
Shin Mai Yasa Kai
Rabiu ( Babangida)
Baka Shiga Safgan Mata Ne? De-De Da Budurwa Baka Da Ita, Me Yasa? Baka Da Lafiya Ne, Ko Aljanna Ce Ta Aureka?
AMSA
SHIGA LAMURAN MATA : Wannan Natural Nature Na Ne, A Haka.Duk Wanda Ya San Ni Tun Yarantata Zai Shaida Hakan, Haka Kawai Bana Iya Yin Safgogina Da Mata Ba. Inde Ba 'Yan,uwana Na Jini Ba.
BUDURWA/GIRLFRIEND : Mutumin Da Bai Tsaya Da Qafafuwansa Ba, Ta Yaya Zai Goyi Wani, Yaro Ai Baya Goyon Yaro. In Ko Ya Goyeshi Sa Zube Qasa Tare, Kuma A Rayuwa Banason In Karyawa 'Yar Kowa Zuciya, Ki Gama Yarda Dani, Aje-Aje Wata Rana Ki Ce BABA Yace In Turo Magabata, Kiga Na Yi Shiru Ban Turo Ba, Ko In Gudu, Ki Daukeni A Matsayin Mayaudarin 'Yan Mata Ko Maci Amana, ETC Yana Daga Abunda Yasa Nayi Baya-Baya Da Harkan, Kuma Soyayya Akwai Abunda Nazariyyata Ta Nuna Mini, Mafi Yawancin Wanda Zakaga Ana Soyayya Kaga Kamar Za'a Hadiye Juna Don Soyayya, Basu Cika Auren Junansu, Kaga Wannan Ma, Wani Tanaqudi Ne. Kuma Shi Auren Nan In Allah Yayi Muna Cikin Masu Yinsa, Toh Lokaci Ne.
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM

Comments

Popular posts from this blog

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA

001 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AZUMI