JIHADI PART TWO
kashi na 2
TAQAITACCEN BAYANI AKAN JIHADI
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على سيدنا محمد النبى وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل البيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya ‘Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Ina Fata Muna Cikin Qoshin Lafiya, Majinyatanmu Kuma Na Gida Da Na Asibiti, Allah Ya Basu Lafiya Ya Yaye Su, Mamatanmu Kuma Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika A Imani.
Ameen Suma Ameen.
.
A Gurguje In Bamu Manta Ba Muna Dan Taqaitaccen Bayani Akan Jihadi, Daga Littafin fiqhun Malikiyyah Wato Risala na Ibnu Abiy Zaideen Qirawaniy Allah Ya Yi Masa Rahma.
.
In Bamu Manta Ba A Part 1 Na Fada Cewa Zamu Dora Akan Fadin Mallam Rahimahullahu.
.
ولا بأس بقتل من أسر من أعلاج
Babu Laifi Da A Kashe Wadanda Aka Ribato/Kamo A Yaqi Daga Kafurai, ( In An So Kuma A Barsu, Wannan Magana Ce Mai Tsawo, Babu Lokaci )
.
ولا يقتل أحد بعد أمان
Hakanan (Mutum Bai Da Hurumin) Kashe Daya (Daga Cikin Wanda Ba Musulmai Ba) Bayan An Riga An Qulla Amana ( Amana Na Zaman Lafiya /raujimetawiy/ Tsakanin Musulmai Da Wanda Ba Musulmai Ba, Babu Cuta Babu Cutarwa, Kuma Koda Kai Musulmi Ne Misali Aka Qulla Zaman Lafiya, Sai Wani Wanda Ba Musulmi Ba Haka, Ya Kasance Yana Cutar Da Kai, To Anan Dan Kai Kana Musulmi Baza Yaqe Shi, Kuma Bazaka Kashe Shi Ba, A’a Qaranshi Zakayi Zuwa Shuwagabanni Ko Hukuma, A Zauna Ga Ka Ga Shi Ga Shuwagabanni Masu Jagorantar Musulmai Da Masu Jagorantar Su Yahudawan Ko Kirista Ko majusawan A Zauna A Warware Maku Matsalarku A Sasantaku, Tunda an Qulla Amana Na /raujimetawiy/ Zaman lafiya, Bawai Zaka Dauki Mataki Ba Dan Kawai Kana Musulmi Shi Kuma Yana Bayahude, Banasare, Ko Mabajuse)
.
ولا يحفر لهم بعهد
Hakanan Idan Anyi Alqawari Dasu, Baza A Warware /raujimetawiy/ Masu Wannan Alqawarin Ba.
( Sai Dai Idan Su Sun Kasance Ana Aikata Sa6anin Yadda Aka Qulla Amana Na Zaman Lafiya, Misali Kamar /raujimetawiy/ Ace An Qulla Amanan Zamanin Lafiya Kar Ayi Kaza Kar
Ayi Kaza, Sai Kuma Ya Zamana Abunda Akace Kar Ayi Shi Sukeyi, Abunda Akace Ayi Basa Aikatawa, To Nan Kam Za’a Warware Amanan A San Yadda /raujimetawiy/ Za’ayi Gwargwadon Yadda Suke Cutan Musulmai )
.
ولا يقتل للنساء والصبيان
Hakanan ( In Anje Yaqi ) Ba’a Kashe Mata Ba’a A Kuma Kashe Yara Qanan.
ويجتنب قتل الرهبان والأحبار إلا أن يقاتلوا
Hakanan Ana Nisantan Kashe Masu Bautansu ( Irin Mutanen Da A Kullum Suna Kan Yi Hidima Ga Addininsu, Ko Su A Kullum /raujimetawiy/ Suna Kan Bautansu, Imma Na Kiristanci Ko Na Yahudanci Ko Na Majusawa, To Irin Wadannan Mutanen Ba’a Yaqansu In Anje Yaqi ) Amma Kuma In Ya Kasance Sun Yaqi Musulmai Toh Suma Za’a Yaqe Su.
.
وكذلك المرأة تقتل إن قاتلت
Hakanan Mace Itama Za’a Yaqeta Idan Ta Yaqi Musulman.
.
ويجوز أمان أدنى المسلمين على بقيتهم
Yana Halatta A Qulla Amana Na Zaman Lafiya Da Wani Daga Cikin Musulmi Babba Haka, Yana Mai Wakiltan Sauran Musulman (Wajen Qulla Amanan )
وكذلك المرآة والصبي إذا عقل أمان
Hakanan Ana Iya Qulla Amana Da Mace Ko /raujimetawiy/ Da Yaro Idan Sun San Menene Amana Sun San Fahimmancinsa
وقيل
Wa Qila Aka Ce
A’a Bazai Yu A Qulla Amana Da Mace Ba, Ko Da Yaro
إن جاز ذالك الإمام جاز
Sai Dai Idan Shugabansu Ne Ya Basu /raujimetawiy/ Daman Su Je A Qulla Amanan Zaman Lafiya Dasu, Toh Idan Shugaban Nasu Ya Basu Daman Hakan, Toh Idan Aka Qulla Dasu Toh Yayi.
.
وما غنم المسلمون بإيجاف
Amma Ganiman Musulmai Wanda Suka Samu Ta Hanyan Kai Hari.
فليأخذ الإمام خمسه ويقسم الأربعة الأخماس بين أهل الجيش
To Shugaba/Kwamanda Wato Wanda Ya Jagorancin Yaqin, Zai Dauki Daya Bisa Biyar 1/5 ( Wato Idan Aka /raujimetawiy/ Hada Kayan Ganiman Da Aka Samu Waje Daya, Sai A Raba Ganiman Gida Biyar, Kashi Daya Daga Cikin Kashin Biyar In, Na Kwamanda Ne )
Sauran Kashi Hudun Kuma Shi Za’a Rabawa Sauran Mayaqan.
.
وقسم ذالك ببلد الحرب أولى
Raba Ganiman A Garin Da Akayi Yaqin, Shi Yafi.
.
Alhamdulillahi Masha Allah
Duka Duka Anan Zan Tsaya Da Izinin Allah.
raujimetawiy
Abunda Muka Rubuta Dai-Dai Allah Ya Bamu Ladansa, Wanda Muka Yi Kuskure Kuma Allah Ya Yafe Mana.
.
Marubuci
#raujimetawiy
#RabiuAlhajiUmarJimetawiy
#BPM_PAN_PHM
.
29 Jimada Sani 1442 Hijrah
11 February 2021 Miladiyya
Ranar Alhamis.
.
مع السلام فى أمان الله
Edited Date And Time
17 Rabi'ul Sani 1447 Hijrah
20 October 2023 Miladiyyah
Ranar Lahadi
Edited Date And Day
16 Jimada Awwal 1446 Hijirah
17 November 2024 Miladiyyah
Ranar Lahadi
Comments
Post a Comment