004 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA


بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda 
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa
*
A Gurguje
In Bamu Manta A Kashi Na Uku Munce Insha Allahu Zamu Tashi A 
*
وَللِِوَصِيِّ أَنْ يزَّوجَ الطِفْلَ فِى وِلاَيَتِهِ
Wanda Aka Yi Masa Wasiyya ( Da Aurar /raujimetawiy/ Da Wani, Toh Iya ) Aurar Da Yaro, Cikin Waliccinsa,
وَلاَ يُزَوِّجَ الصَّغِيْرَةُ إِلاَ أَنْ يأمرهُ الأَبُ بِإِنْكَاحِهَا
( Amma Wanda Aka Bashi Wasicci Aurar Da 'Ya ) Bazai Aurar Da Yarinya Qarama Ba, Face Sai Mahaifinta /raujimetawiy/ Yayi Masa Izinin Aurar Da Ita.
*
ولَيْسَ ذُوا الأَرحَام مِنَ الأَوْلِيَاءُ
Dangin Uwa /raujimetawiy/ Basayin Walicci ( Wajen Aurar Da 'Da Ko 'Ya )
وََالأَوْلِيَاءُ مِنَ العَصَبَةِ
Wal Auliya'a : Masu Yin Walicci Sune Dangin Uba,
وَلاَ يَخطُبُ أَحَدُُ عَلَى خطْبَةِ أَخِيهِ
Kada 'Dayanku Ya Nemi Auren ( Wata ) Akan Neman Auren 'Dan,uwansa،
Wannan Magana In Muka Je Ga
MUWADDA MALIK
KITABUL NIKAHI
BABU MA JA'A FIL KIDBATI
HADISI NA 1094
حَدَّثَنِي يَحْيَى عَنْ مَالِكٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى بْنِ حَبَّانَ عَنِ الأَعْرَجِ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((لاَ يَخْطُبُ أَحَدُكُمْ عَلَى خِطْبَةِ أَخِيهِ)).
Haddasani Yahya Ann Malik, Daga Muhammad 'Dan Yahya 'Dan Habbana, Daga A'araji, Daga Abiy Huraira Daga Manzon Allah S.A.W Ya Ce (( Kada 'Dayanku Ya Nemi Aure, Akan Neman Auren 'Dan,uwansa ))
-
وَلاَ يَسُومُ علَى سَومِهِ، وذَلِكَ إِذا رَكَنَا وَتَقَارَبَا
Hakanan Kada 'Dayanku Yayi Ciniki Akan /raujimetawiy/ Cinikin 'Dan, uwansa, Idan Ciniki Ya Fada, An Sallama.
*
وَلاَ يَجُوزُ نِكَاحُ الشٌِغَارِ وهُوَ البُضْعُ بِالْبُضْعِ
Baya Halatta Yin Auren Shigarr, Wa-Huwa Shine /raujimetawiy/ Tsoka-Ga-Tsoka
Abun Nufi Shine, In Muka Duba Sahihul Muslim /raujimetawiy/ Zamu Ga Hadisi Kamar Haka
صحيح مسلم
١٦ - كتاب النكاح
(٧) باب تحريم نكاح الشغار ويطلانه

١٤١٥ -حدثنا يحيى بن يحيى. قال: قرأت على مالك عن نافع، عن ابن عمر ؛ أن رسول الله صلى الله عليه وسلم نهى عن الشغار.
والشغار أن يزوج الرجل ابنته، على أن يزوجه ابنته. وليس بينهما صداق.
Sahihul Muslim
16 Kitabul Nikahi
7 Babin Haramcin Auren Shigaari
Hadisi Na 1415
Daga Ibnu Umar, Daga MANZON ALLAH S.A.W ( Annabi Yayi ) Hani Da Yin Auren Shigaari.
( Abun Nufi ) Da Shigaari Shine Mutum Ya Aurarwa Wani Mutum Da 'Yarsa /raujimetawiy/ Shima Ya Aurar Masa Da 'Yarsa, Ba Tareda ( An Bada ( Sadaki A Tsakininsu Ba.
Koda An Bada Sadaki Kada Sadakin Ya Zama Irin 'Daya, In An Bawa Wancan ₦200,000 Toh 'Dayar A Bata 210,000 Ko ₦195,000 Misali. /raujimetawiy/
Inya Zama ₦200,000 Dukkansu, Shima Shigaari Ne, Wallahu A'alamu.
-
وَلاَ نِكَاحُ بِغَيْرِ صَدَاقِِ
Ko 'Daura Aure Ba Tareda Sadaki Ba ( Shima Baya Halatta, Ko An 'Daurama Za'a Warware Shi, In Kuma Har Mijin Ya Sadu Da Ita, Dole Za'a Ambata Mata Sadakinta Kwatankwancinta /raujimetawiy) A Bata. )
-
وَلاَ نِكَاحُ الْمُتَعَةِ وَهُوَ النِّكَاحُ إِلَى أَجَلِِ
( Hakanan Baya Halatta ) Yin Auren Mutu'a, Mutu'a Shine Auren Da Ake Yinsa Temporary Daga Wannan Lokacin Zuwa /raujimetawiy/ Wannan Lokacin, Idan Lokacin Yayi Ko Baka Ambata Mata Saki Ba Ko Takardar Saki Ba, Aurenku Ya Mutu.
صحيح البخاري
٧٠ - كتاب النكاح
٣٢ - باب: نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم عن نكاح المتعة آخرا.

٤٨٢٥ - حدثنا مالك بن إسماعيل: حدثنا ابن عيينة: أنه سمع الزهري يقول: أخبرني الحسن بن محمد بن علي، وأخوه عبد الله، عن أبيهما:
أن عليا رضي الله عنه قال لابن عباس: إن النبي صلى الله عليه وسلم نهى عن المتعة وعن لحوم الحمر الأهلية، زمن خيبر.
Sahihul Bukhari
70 Kitabul Nikahi
32 Babin Hanin Manzon Allah S.A.W Akan Yin Wani Auren Mutu'an
Daga Sayyiduna Aliyu RTA Yake Fadawa Ibnu Abbas : Daga ANNABI S.A.W Yayi Hani Akan ( Auren ) Mutu'ah....
-
وَلاَ نِكَاحُ فِى العِدَّةِ 
( Hakanan Baya Halatta ) 'Daura Auren Mace /raujimetawiy/ Tana Cikin Idda
In Muka Duba MINHAJUL MUSLIM Na Abubakar Jabir Al-Jaza'ir R
Bugun Darul Fikr, /raujimetawiy/  Fasali Na Shida, Qarshen Shafi Na 343 Zamuga Yace
#النِّكَاحُ_فِى_الْعِِدٌَةِِ وهو أن يتزوج الرجل المرأة المعتمدة من طلاق أو وفاة
Aure_Cikin_Idda :- Shine Mutum Ya Auri Mace Mai Idda, /raujimetawiy/ Iddan Saki Ko Idda Na Ta-Kaba
فهذا النكاح باطل ، وحكمه : أن يفرق بينهما لبطلان العقد، ويثبت للمرأة الصداق إن كان قد خلا بها
Toh Wannan Auren 'Batacce Ne, Hukuncinsa Kuma, Za'a Raba/Warware Tsakaninsu, Saboda 'Bacin 'Daurin Auren, /raujimetawiy/ Idan ( Mijin ) Ya Sadu Da Ita, Sadaki Ya Tabbata Gareta.
ويحرم عليه أن يتزوجها بعد انقضاء عدتها، عقوبة له
Yana Haramta A Gareshi Ya Aureta Bayan Ta Gama Iddan, 
( Haramtawa Anyishi Ne Domin ) Ya Zamo Ukuɓa ( Hukunci Da Taka Tsan-Tsan /raujimetawiy/ ) A Gareshi
( Qarqashin Sharhan Wannan Maganar, Zamuga Yace : Ma'abota Ilimi Sunce Yana Halatta A Gareshi Ya Aureta Bayan Ta Gama Iddan, Amma In Har Bai Sadu/Jima'i Da Ita Ba, Idan Kuma Ya Sadu Da Ita A Wajan Malikiyyah Da Hambaliya RH Suna Ganin Ta Haramta /raujimetawiy/ A Gareshi, Haramcin Na Har Abada )
وذَلك قول الله تعالى " وَلاَ تَعْزِمُوا عُقْدَةَ النِّكَاحِ حَتَّى يَبْلُغَ الْكِتَٰبُ أَجَلَهُ " سورة البقرة ٢٣٥
Hakan ALLAH MADAUKAKIN SARKI Yake Yi Mana Jan Kunne Yake Ce Mana " Kada Kuyi Qudurin Daura Auren ( Mace Tana Cikin Idda ) Har Sai Littafin ( Idda ) Ya Kai Ajalinsa "
Baqara, Aya 235
-
وَلاَ مَا جَرَّ إِلَى غَرَرٍ فِى عَقْدِِ أَو صَداقٍ،
( Hakanan Baya Halatta Bayar Da ) Abunda Yake Tafiya Izuwa Ruɗani Wajen 'Daura Aure Ko Sadaki,
ولاَ بِمَا لاَ يَجُوزُ بَيْعَهُ
Ko Kuma Bayar Da Abunda Baya Halatta /raujimetawiy/ Sayar Dashi ( Kamar Su Alade Etc )
*
Masha Allah Alhamdulillahi
Duka-Duka Anan Zamu Tsaya Da Izinin Allah.
Daga Qarshe Ina Yi Mana Adu'ar Matasa Da 'Yan Mata, Zawara Maza Da Zawara Mata, /raujimetawiy/ Da Basuda Aure, Ubangiji Allah Ya Hore Musu Dalilin Yin Auren, Wadanda Suke Da Auren Ubangiji Allah Riqa Musu.
Mazaje Nagari, Mataye Nagari Da Zuriya Ta Gari /raujimetawiy/ Ubangiji Allah Ya Bamu.
Ameen Summa Ameen.
*
Insha Allahu Kuma A Kashi Na Biyar Kuma Zamu Tashi A
وما فسد من النكاح
*
24 Jimada Sani 1447 Hijrah
14 December 2025 Miladiyya
Ranar Lahadi
3pm

marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, JMT, YOLA

Comments

Popular posts from this blog

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

RABIU ALHAJI UMAR JIMETAWIY

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA