001 HAUSA FULANI KANURI/BAREBARI SHIN AKWAI YAREN DA YAFI WANI YAREN FIFIKO A WAJEN ALLAH

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
-
A Gurguje
Cikin Ikon Allah S.W.T Ina So Na 'Danyi Magana Akan Shin Akwai Wata /raujimetawiy/ Qabila Ko Yaren Da Yafi Wani Fifiko A Wajen Allah.
Ba Tareda Ayyana Ni Wani Yare Bane, Zanyi/raujimetawiy/ Magana Don Kada Wani Yace Nayi Son Kai.
*
Zan Bada Misali Da Yaruka Guda Uku, Wanda /raujimetawiy/ Sune Manyan Yaruka A Arewacin Najeriya FULANI, HAUSA DA KANURI/ BAREBARI Wanda Kuma Kaso 90% Duka Addini 'Daya Suke Bi Shine /raujimetawiy/ Musulunci.
Amma Yau An Wayi Gari, Bahaushe Yana Ganin Bafulatani Ba Komai Ba, Bafulatani Yana Ganin Bahaushe Ba Komai Ba, Kanuri Ma Haka.
*
Kowa Yana Ganin Yafi Kowa Asali Da Tushe, Akwai Kalmomi Marasa. Dadi Da /raujimetawiy/ 'Dan Wannan Yaren Yake Jifan 'Dan Wancan Yaren Dashi, 'Dan Wancan Yaren Yake Jifan 'Dan Wannan Yaren Dashi, Ni Bazan Iya Ambata Su Ba.
*
- Toh Da Kake Ganin Kanka KANURI/BAREBARI /raujimetawiy/ Kake Ganin BAHAUSHE Ko BAFULATANI Wani Qasqantacce Kai Kadai Ne Yare Tsayayye.
- Ko Kai BAFULATANI Kake Ganin BAHAUSHE Ko KANURI/BAREBARI Su Wasu Qasqantattu Ne, Kai Ne Kadai /raujimetawiy/ Yare Tsayayye.
- Ko Kai BAHAUSHE Ne Kake Gani KANURI/BAREBARI Ko BAFULATANI Su Qasqantattu Ne, Kaine /raujimetawiy/ Kadai Yare Tsayayye.
Toh Tsaya Kuji Abund Allah S.W.T Ya Fada
*
قَالَ اللَّهُ تَعَالَى
يَأَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرِِ وَأُنْثَىٰ
ALLAH MADAUKAKIN SARKI YA CE
" Ya! Ku Mutane ( Lalle Ku Sani ) Mun Halicceku Ne Daga Namiji Da Mace ( Dukkanmu An Haliccemu Ne Daga Jikin Namiji Da Mace, Ba Wanda Aka /raujimetawiy/ Haifeshi Daga Namiji Da Namiji Ko Mace Da Mace, Dukkanmu An Haifemu Ne Daga Haduwan Ruwan Maniyyin Namiji Da Na Mace, )
وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبََا
Kuma Muka Sanyaku Wasu Akan Tudu Wasu A Kwari ( Ko Kai Kanka Inka Tsaya Zakaga Wannan Anguwan Ko Wannan Garin Akan Tudu Suke, Even Ambaliyar Ruwa Baya Ta6asu, Wasu Kuma A Kwari Suke Rayuwarsu, /raujimetawiy/ Ruwan Sama Mai 'Dan Qarfi Saiya Yayi Musu Ambaliya )
وَقَبَائِلَ لِتَعَارِفُوا
 Kuma Muka Sanyaku Qabila Daban-Daban Yare Daban-Daban Domin Kusan Junanku ( Toh Muji Da Kyau, Allah Yace Ya Sanyamu Qabila Yare Daban-Daban Domin Mu San Junanmu, /raujimetawiy/ Ba Don Mu Dinga Zagin Junanmu Ba, Misali In Ance
Auwal, Sai Ace Ai Bahaushe Ne.
Sani, Sai Ace Ai Bafulatani Ne.
Salisu, Sai Ace Ai Kanuri Ne.
Rabiu, Ai Barebari Ne. /raujimetawiy/
Toh Mun Gani Koh, Mun San Junanmu Ta Hanyan Suna Da Tare.
إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَُهِ أَتْقَاكُمْ
Mafi Girmanku A Wajen Allah, Shine Wanda Yafi Wani Tsoron Allah
( Toh Munji Dai, /raujimetawiy/ Allah Bai Ce Yare Kaza Shine Mafi Girma A Wajena, A'a Cewa Yayi Mafi Girmanku A Wajen Allah Wanda Yafi Wani /raujimetawiy/ Tsoron Allah,
Wannan Aya Kadai Ta Ishemu Izna.
إِنٌَ اللًَهَ عَلِيمُُ خَبِيرُُ
Lalle Allah Masani Ne ( Dangane Da Abunda Kuke Aikatawa ) Kuma Masani Ne ( Akan Abunda Kuke Aikatawa )
سورة الحجرات
*
Karmu Tsawaita Rubutu, Zamu Tsaya Anan Da Izinin Allah, A 002 Kuma /raujimetawiy/ Insha Allahu Zamu Kawo Hadisai Kamar Guda Biyu.

28 Rajab 1447 Hijrah
16 January 2026 Miladiyya
Ranar Juma'ah

marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM , CON , MVM

Comments

Popular posts from this blog

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAUSHE AKE SA RAI DA DAREN LAILATUL QADARI ETC

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA