002 HAUSA FULANI KANURI/BAREBARISHIN AKWAI YAREN DA YAFI WANI YAREN FIFIKO A WAJEN ALLAH?

@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya! 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata, Manya Da Qanana, Da Fatan Muna Cikin Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu, Yayyunmu Da Qannanmu, Abokanmu Da Sa'o'inmu Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya, Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahman, In Tamu Tazo Allah Yasa Mu Cika Da Imani.
*
A Gurguje
A 001 In Bamu Manta Ba, Munce Zamu /raujimetawiy/ 'Dan Kawo Hadisai Kamar Guda Biyu Haka.
Na Farko
وقال صلى الله عليه وسلم :
MANZON ALLAH S.A.W YACE :
يَاأَيُّهَا النَّاسُ إِنَّ رَبَّكُمْ وَاحِدُُ
!Ya Ku Mutane ( Lalle Ku Sani ) Ubangijinku Guda Daya Ne ( In Muka Duba Nan, Zamuga Annabi S.A.W Cewa Yayi "Ya Ku Mutane Lallai Ubangijinku Guda 'Daya Ne, /raujimetawiy/ Wannan Izina Ne Ga Balarabe, Bature, Bafaranse, Bafulatani, Kanuri, Bahaushe, Bayarbe, Inyamuri ETC Mu San Cewa Ubangijinmu 'Daya Ne, Babu Wanda Yake /raujimetawiy/ Ubangijinsa Yake Daban )
وَإِنَّ أَبَاكُمْ وَاحِدٌ
Lalle Babanku / Mahaifinku Guda 'Daya Ne ( Wato Annabi Adamu A.S Duk Wasu Ma'abota Yare Na Duniya, Annabi Adamu A.S Ne Babanmu, Don Haka, Don Allah Yayika Farin Fata Ka Kyamaci Ko Ka Zagi Baqin /raujimetawiy/ Fata 'Dan,uwanka Ka Kyamata, 'Dan,uwanka Ka Zaga. /raujimetawiy/
Ko Kuma Don Allah Yayika Bahaushe, Kake Zagin Bafulatani 'Dan Ta'adda, Ko 'Dan Allah Yayika Bafulatani Kana Zagin Bahaushe Bamaguje Etc /raujimetawiy/ Toh Dukkanmu Mu Sani, Babanmu Daya Ne Annabi Adamu A.s )
أَلاَ لا فَضْلَ لِعَرَبِّى عَلَى عَجَمِيِّ، ولاَ لِعَجَمِيِّ عَلَى عَرَبٓيِّ
( Sai Annabi S.A.W Ya Qara Da Cewa ) Ku!! Saurara, Babu Fifiko Ga Balarabe /raujimetawiy/ Akan Ajami, Ko ( Fifiko Ga ) Ajami Akan Balarabe,
وَلاَ لِأَحْمَرَ عَلَى أَسْوَدَ وَلاَ لِأَسْوَدَ عَلَى أَحْمَرَ إَلاَّ بِالْتَقْوَى
( Hakan Babu Fifiko Tsakanin ) Ja-Jayen Fata Da Baqaqen Fata, Ko Baqaqen Fata Akan Ja-Jayen Fata, Sai Dai Da Tsoron Allah ( Nan Ma Annabi S.A.W Ya Qara Nuna Cewa : Tsakanin /raujimetawiy/ Ja-Jayen Fata, Fararen Fata Da Baqaqen Fata Etc Babu Wanda Yafi Wani Fifiko Sai Da Taqawa, Don Haka, Don Allah Yayika Baqin Fata Karkaga Kamar Allah Bayasonka Ne, Yi Qoqari Ka Zama Mai Taqawa, /raujimetawiy/ Kaima Da Allah Yayika Farin Fata Ko Jan Fata Karkaga Kamar Kai Kadai Allah Yafi So, A'a, In Baqin Fata Ya Fika Da Taqwa, Toh Ya Fika )
إِنَّ أَكَرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ
رواه البيهقي
( A Qarshe Dai Annabi S.A.W Ya Rufe Mana Hadisin Da Wannan Kalmar ) Mafi Girmanku A Wajen Allah Wanda Yafi Wani Tsoron Allah.
Imamu Baihaqi Ne Ya Ruwaice Shi.

*

Hadisi Na Biyu

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم
MANZON ALLAH S.A.W YA CE :
 "إن الله لا ينظر إلى صوركم وأموالكم. ولكن ينظر إلى قلوبكم وأعمالكم
رواه مسلم
Lalle Allah Madaukakin Sarki Baya Duba/Kallon Surorinku Ko Dukiyoyinku ( Don Allah Yayika Mai Kyawun Sura/Jiki, Ko Dukiya Ka Dinga Ganin Kamar /raujimetawiy/ Kai Kadai Allah Yafi So, A'a Ina, Gashi Kaji Annabi S.A.W Yace, Allah Ba Ruwansa Da Wannan )
Sai Dai ( Allah ) Yana Duba Ne Izuwa Zuqatanku ( Dangane Da Abubuwan / raujimetawiy/ Da Kuke Qudurtawa/Niyya Na Alkhairi, Imma Na Sharri )
Da Ayyukanku ( Imma Na Alkhairi, Imma Na Sharri, In Kayi Na Alkhairi Kaga /raujimetawiy/ Sakamako Mai Kyau, In Kayi Na Sharri Kaga Sakamako Mara Kyau, Allah Ya Karemu. )
Imam Muslim Ne Ya Rawaito Wannan Hadisin.

*
Daga Qarshe
Ina Mai Qara Jan Kunnenmu, Ko In Ce Tunatarwa,
Bam-Bamce Bam-Bamce Yare/Qabila Da Nuna Wariyar Launin Fata, /raujimetawiy/ Mu Dainashi, Mu Ajiyeshi, Lalle Mu Sani, Dukkanmu Ubangijinmu/Mahaliccinmu Guda 'Daya Ne, Ubanmu/Mahaifinmu Guda 'Daya Ne.
*
23 Ramadan1447 Hijrah
13 March 2026 Miladiyyah
Ranar Juma'ah
12:35am
*
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVM

Comments

Popular posts from this blog

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

RABIU ALHAJI UMAR JIMETAWIY

TAQAITACCEN BAYANI AKAN LAYYA CIKIN HARSHEN HAUSA