005 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa.
*
A Gurguje
In Bamu Manta Ba, A Kashi Na Hudu Munce Insha Allahu Ta'alah Zamu Tashi A Inda Malam RH Yake Cewa :
وَمَا فُسدَ َ مِنْ نِكَاحِ لِصَدَاقِهِ فُسِخَ قَبْلَ البِنَاءِ
Auren Da Ake Batashi Saboda Sadakinsa ( Kamar A Bayar Da Abunda Baya /raujimetawiy/ Halatta A Matsayin Sadaki ) Sai Ayi Qoqari A Bata/Warware Auren Kafin Mijin Ya Sadu/Jima'i Da Ita,
فَإنْ دَخَلَ بِهَا مَضَى وَكَانَ صَدَاقُُ المِثْلِ
Idan Kuma ( Mijin ) Ya Sadu/Jima'i Da Ita, Toh Yayi, Amma Kuma Za''a Bada Sadaki Misli ( Wato Kwatankwancinta, Idan 'Yar Sarauta Ce, Sai /raujimetawiy/ A Bada Sadakin Kwatankwacin 'Ya'Yan Sarakuna, Idan 'Yar Masu Kudi Ce Kwatankwancinta, Idan 'Yar Talaka Ce Itama /raujimetawiy/ Haka. )
ومَا فَسَدَ مِنْ النِّكَاحِ لِعِقْدِهِ، وَفُسِخَ بَعْدَ البِنَاءِ فَفِيهِ المُسَمَّى
Auran Da Aka 'Batashi Saboda Sadakinsa, Sai Bayan Bina'i ( Saduwa ) Aka Rabashi/Batashi, Toh Za'a Bada Abunda Aka Ambata Na Sadaki. /raujimetawiy/
وَتَقَعُ بِهِ الْحُرْمَةِ كَمَا تَقَعُ بِالنِّكَاحِ الصَّحِيحِ
Haramcin Aure Yana Afkuwa A Cikinsa Kamar Yadda Yake Afkuwa A Aure /raujimetawiy/ Managarci.
( Wato : Auren Da Ake Warwareshi Dangane Da Sadaki /raujimetawiy/ A Wasu Lokutan Haramcin Yin Aure Yana Shiga )
ولَكِنْ لاَ تَحِلُّ بِهِ المُطَلَّقَةُ ثَلاَثََا،
Sai Dai Bata Halatta Da Wacce Aka Saka Saki Uku
وَلاَ يُحَصِّنُ بِهِ الزَّوْجَانِ
Kuma Baya Katange Ma'aurata
( Wato : Duk Wanda Ya Saki Matarsa Saki Uku, Ba Ta Halatta A Gareshi /raujimetawiy/ Ya Aureta, Har Sai Tayi Wani Auren Ta Fito.
Idan Ta Fito Tsohon Mijin Yana Iya Aurenta Idan Sun Daidaita Tsakaninsu )
*
وحَرَّمَ اللَّهُ سُبْحَانَهُ منَ النِّسَاءِ سَبْعََا بِالْقَرَابةِ، وَسَبْعََا بالرَّضَاعِ وَالصِّهْرِ
Allah Madaukakin Sarki Ya Haramta ( Auren ) Mata ( Nau'i ) Bakwai Saboda Kusanci /raujimetawiy/ Da Mata ( Nau'i ) Bakwai Saboda Shayarwa Da Surkuntaka/In-law.
.
فقال عزّ وجلّ
" حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالاَتُكُمْ وَبَنَاتُ الأَخِ وبَنَاتُ الأُخْتِ "
سورة النساء آية ٢٣
Allah Ya Daukaka Ya Buwaya Ya Ce
" An Haramta Muku Auren Iyayenku, Da 'Ya'yanku ( Mutum Ya Auri 'Ya'yansa Wannan An Haramta ) Da 'Yan,uwanku ( Mutum Ya Auri Yayarsa Ko /raujimetawiy/ Qanwarsa, Ko Mace Ta Auri Yayanta Ko Qaninta, Uwa Daya Uba Daya, Ko Uba Daya, Ko Uwa Daya, Wannan An Haramta. Hakan Mutum Ya Auri ) Goggonsa/Yaqunbo ( Yayar Babansa Ko Qanwar Babansa, Wannan Ma An Haramta. ) Da Yafendo ( Wannan Ma An Haramta Mutum Ya Auri, Yayar Mamansa Ko Qanwar Mamansa ) Da 'Yayan Dan,uwa Namiji ( Mutum Ya Auri 'Ya'yan Yayansa Ko Qaninsa /raujimetawiy/ Wanda Suke Uwa Daya Uba Daya, Ko Uba Daya, Ko Uwa Daya Wannan Ma An Haramta ) Da 'Ya'yan 'Yar,uwa Ta Mace ( Shima Hukuncin Daya Yake Da 'Ya'yan Dan,uwa Namiji ) "
Suratul Nisa'i Ayata 23
فَهَؤُلاَءِ منَ القَرَابَةِ
Wadannan Sune Daga Kusanci ( Wato /raujimetawiy/ Jerin Nau'o'in Mata Guda Bakwai Da Aka Hana Aurensu, Saboda Su 'Yan,uwane Na Jini Na Kusanci )
.
وَاللَّوَاتِى مِنَ الرَّضَاعِ والصِّهْرِ
Amma Wadanda Suke Ta Gefen Shayarwa Da Surkuntaka/In-law
Sune Zasu Zo Kamar Haka
-
قَولُهُ تَعَالَى " وَأَمَّهَاتُكُمٌ اللاَّتِى أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنْ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبٕائِبُكُمْ اللاَّتِى فِى حُجُورِكُم مِنْ نِسَائِكُمْ اللإّتٓى دَخٕلْتُمْ بِهِنَّ فَإِنْ لَمْ تَكُونُوا دَخَلْتُمْ بِهنَّ فلاَ جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلاَئِلُ أَبْنَائِكُمْ الَّذِينَ مِنْ أصْلاَبِكُمْ وأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الأُخْتَيْنِ إِلاَ مَا قَدْ سَلَفَ "
Allah Madaukakin Sarki Yake Cewa
" Da Iyayenku Wadanda Suka Shayarwa Daku ( Domin Larabawa A Daa Sun Kasance Suna Bada 'Ya'yansu Ga Wasu Matan Daban Su Shayar /raujimetawiy/ Musu Da 'Ya'yansu, Toh Suma An Haramta Aurensu ) Da 'Yan,uwanku Na Wajen Shayarwa ( Wanda Mace 'Daya Ta Shayar Daku Da Nononta, Toh Babu Aure A Tsakaninku ) Da Iyayen Matayenku ( Wato Surakananku, Suma An Haramta Muku Aurensu ) Da Agola Da Suke Cikin 'Dakunanku Na Matayenku, Idan Kun Sadu Da Su, /raujimetawiy/ Idan Baku Sadu Da Su Ba, Toh Babu Laifi Ku Auresu, ( Abun Nufi, Kaine Ka Auri Mace Bazawarar Da Takeda 'Ya Budurwa, Sai Yaga 'Yar, Yaga Yanaso, Toh Anan In /raujimetawiy/ Bai Sadu Da Uwar Ba, Yana Iya Fasa Auren Uwar Ya Auri 'Yar. Idan Kuma Ya Sadu Da Uwar Toh 'Yar Ta Haramta A Gareshi. " Da Matayen 'Ya'yayenku Wadanda Kuka Haifa Na Tsatsonku ( Wato /raujimetawiy/ Uba Ya Haramta Ya Auri Matar 'Dansa Na Cikinsa. Hakanan Yana Haramta Ga Mutum ) Ya Hada 'Yan,uwan Juna ( Zaman Kishi, Babu Kyau Mutum Auri Yaya Da Qanwa A Hadasu Zaman Kishi ) Sai Abunda Ya Riga Ya Wuce ( Wato A Zamanin Zahiliya An Aikata Waɗannan Abubuwan. "
.
Aya Ta Ci Gaba Cewa
وَلاَ تَنْكِحُوا مَا نَكَحَ ٱبَاؤَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ
Kada Ku Auri Matayen Da Iyayenku Suka Aura.
*
وَحَرَّمَ النّٕبِيُّ صلى الله عليه وسلم بِالرَّضَاعِ مَا يَحْرُمُ مِنَ النَّسَبِ
Annabi S.A.W Ya Haramta, Na Shayarwa Kamar Yadda Yake Haramta Na /raujimetawiy/ Nasaba
( Wato Annabi S.A.W Ya Haramta 'Yan,uwa Na Shayarwa Su Auri Junansu, Kamar Yadda Bazai Yuwu Mutum /raujimetawiy/ Ya Auri 'Yar,uwarsa Ta Tsa-Tso, Qanwa Ko Adda )
وَنَهَى أنْ تُنْكَحُ الْمَرْأَةِ عَلَى عَمَّتِهَا أَوْ خَالَتِهَا
An Hana ( Mutum ) Ya Auri Mace Sannan Ya Auro Goggonta/Yaqunbonta ( 'Yar,uwar Babanta, Qanwar Babanta Ko Addar/Yayar Babanta ) Ko Yafendonta ( 'Yar,uwar Mamanta, Qanwar Mamanta Ko Addar Mamanta /raujimetawiy/ A Hadasu Suyi Zaman Kishi, Yin Hakan Babu Kyau An Hana )
فَمَنْ نَكَحَ امْرَأَةََ حَرَّمَتُ بِالْعُقْدِ دُونَ أَنْ تَمَسَّ عَلَى ٱبَائِهِ وأَبْنَائِهِ
Wanda Ya Auri Mace, Daga Sa'ilin Da Aka Daura Auren Wannan Matar/Amaryar Ta Haramta Ga Iyayen Mijin Da 'Ya'yansa ( Su Aura ) Ko Da /raujimetawiy/ Mijin Bai Tara/Sadu Da Ita Ba.
وحَرُمَتْ عَلَيْهِ أَمَّهَاتُهَا
( Hakanan Shima Mijin/Angon ) Iyayenta Sun Haramta A Gareshi ( Ya Auresu )
وَلاَ تَحْرِمُ عَلَيْهِ بَنَاتُهَا حَتَّى يَدْخَلُ بِالأُمِ
( Amma Shi Mijin/Angon ) 'Ya'yanta (Na Cikinta, Ita Matar/Amaryar, Idan Bazawarace Mai 'Ya'ya ) Basa Haramta A Gareshi Har Sai Ya Sadu/Jima'i Da /raujimetawiy/ Ita ( Idan Ya Sadu Da Ita Toh 'Ya'yanta Sun Haramta A Gareshi )
أَوْ يَتَلَلَّذُ بِهَا بِنَكَاحِ أَوْ مِلْكِ يَمِيْنِ أوْ بِشُبَهَةِ مِن نِكَاحِ أَو مِلْكِِ
Ko Yaji Dadi Da Ita Ta Hanyar Aure Ko Ta Hanyar Mallaka Na Baiwa/Quyanga, /raujimetawiy/ Ko Abunda Yayi Kama Da, Ta Hanyar Aure Ko Ta Mallaka Na Baiwa/Quyanga ( Inde Miji Yaji Dadi Da Matar Something Like Romance, Ko Baikai Ga Saduwa Ba, Toh, 'Ya'yanta Sun Haramta/raujimetawiy/ Gareshi.
*
وَلاَ يَحْرُمُ بِالزِّنَا حَلاَلِ
Zina Baya Haramta Halal
( Ma'ana, Mace Da Namiji Ne Sukayi Zina, Sau Daya Ne, Ko Sau Da Yawa, Idan Sun Tuba Ga Allah Sun Daina, Suna Iyayin Aure. )
*
Duka Duka Anan Zan Tsaya Bi'izinillah Ta'alah.
Insha Allahu Kuma A Kashi Na Shida Zamu Tashi A
وحرم الله سبحانه وطء الكوافر ممن ليس من أهل الكتاب بملك أو نكاح
.
Ina Mai Bada Haquri Dangane Da Jinkiri Da Ake Samu,
Kashi Na Hudu Na Sakeshi A
24 Jimada Sani 1447 Hijrah
14 December 2025 Miladiyya
Ranar Lahadi
3pm
.
Saboda Sha'anin Rayuwa Yadda Muka Tsinci Kanmu A Qasar.
*
marubuci
#raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-NORTH
*
02 Zul-Qa'adah 1447 Hijrah
19 April 2026 Miladiyya
Ranar Lahadi
11am
Comments
Post a Comment