MAGUZANCI BA QABILA BA CE A TARIHI - AKIDA CE TA GARGAJIYA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
A Tarihin Al’ummar Hausawa, Akwai Batutuwa Da Dama Da Ake Yawan /raujimetawiy/ Rikicewa A Kansu, Musamman Idan Ana Magana A Kan Asali, Al’ada, Da Addini. Daya Daga Cikin Irin Wadannan Batutuwa Shi Ne Batun Maguzanci. /raujimetawiy/ Wasu Sukan Yi Kuskuren 'Daukar Maguzanci A Matsayin Wata Qabila Daban, Alhali A Mahangar Tarihi, Ilimin Al’adu, Da Fahimtar Zamantakewar Bil’adama, Maguzanci Ba Qabila Ba Ne, Sai Dai Tsarin Aqida Da Addinin Gargajiya Da Wasu Hausawa Suka Rika Bi Kafin Zuwan Musulunci.
Domin Fahimtar Wannan Batu Sosai, Dole Ne Mu Fara Da Bambance Ma’anar Qabila Da Kuma Ma’anar Addini Ko Akida.
MENENE QABILA?
Qabila Tana Nufin Al’umma Mai Asali Guda, /raujimetawiy/ Wadda Take Da Alaka Ta Jini, Harshe, Al’ada, Da Tarihin Da Ya Hada Su. Qabila Ba Abu Na Ne Da Mutum Yake Iya Canzawa Cikin Sauki Ba, Domin Tana Da Alaqa Da Zuriyar Da Mutum Ya Fito Daga Cikinta./raujimetawiy/ Hausawa, Misali, Suna Daya Daga Cikin Manyan Qabilu A Nahiyar Afrika, Musamman A Yankin Yammacin Afrika. Suna Da Harshensu Na Hausa, /raujimetawiy/ Suna Da Al’adunsu, Suna Da Tarihin Da Ya Shafe Daruruwan Shekaru.
MENENE MAGUZANCIN?
Maguzanci Kuwa Yana Nufin Tsoffin Aqidu Da Addinan Gargajiya Da Wasu Hausawa Suka Rika Bi Tun Kafin /raujimetawiy/ Zuwan Musulunci. A Wancan Lokaci, Mutane Suna Da Hanyoyi Daban-Daban Na Bauta, Suna Girmama Iskoki, Suna Yin Wasu Bukukuwa Na Gargajiya, Suna Da Tsarin Rayuwa Da Ya Shafi Imani Da /raujimetawiy/ Abubuwan Da Suka Gada Daga Kakanninsu.
Wadannan Al’adu Da Aqidu Su Ne Aka Qira Maguzanci Daga Baya. Saboda Haka, Maguzanci Ba Ya Nufin Wata /raujimetawiy/ Sabuwar Qabila, Sai Dai Yana Nufin Irin Tsarin Bautar Gargajiya Da Wasu Daga Cikin Hausawa Suka Bi A Wani Lokaci Na Tarihi.
Kuma Shi /raujimetawiy/ Addinin Gargajiya Kowacce Qabila Ka Gani, Sunyi Nasu Kalan Gargajiyancin/Maguzancin Kafin Daga Bisani Addinin Musulunci Ya Shiga Qabilar, Hausawa /raujimetawiy/ Sukan Ce Da 'Yan,uwansu Hausawa Wadanda Sukayi Riqo Da Addinin Gargajiya Da Maguzawa.
Kamar Yadda /raujimetawiy/ Larabawa Kafin Zuwan Musulunci Ake Cewa Zamanin Zahiliyyah.
BAMBANCI TSAKANIN ASALI DA AQIDA
Dole Ne Mu Fahimci Cewa Akwai Babban Bambanci Tsakanin Asali ( Qabila ) Da Kuma Akida ( Addini ). Addini /raujimetawiy/Abu Ne Da Mutum Zai Iya Canzawa Daga Lokaci Zuwa Lokaci, Amma Asalin Kabila Yana Nan Yadda Yake.
Mutum Na Iya Kasancewa Bahaushe, Amma Addininsa Ya Bambanta Da Na Wani Bahaushe. A Tarihi, Akwai Hausawa Da Suka
Kasance:
Masu Bin Addinan
- Gargajiya Maguzanci
- Musulunci
- Kiristanci
Amma Duk Da Wannan Bambanci Na Addini, Asalin Kabilarsu Guda 'Daya Ne Wato Hausa.
Saboda Haka, A Lokacin Da Musulunci Ya Fara Shiga Kasashen Hausa Ta Hannun Malamai Da ‘Yan Kasuwa, Wasu Daga Cikin Hausawa Sun Rungumi /raujimetawiy/ Musulunci Cikin Sauri, Yayin Da Wasu Suka Ci Gaba Da Rike Tsoffin Al’adunsu. Wadanda Suka Ci Gaba Da Rike Tsoffin Al’adu Su Ne Aka Rika Kira Maguzawa.
Amma Wannan Suna Bai Sauya Asalinsu Na Hausa Ba.
TARIHI YA NUNA HADIN KAI NA ASALI
Idan Muka Dubi Tarihin Hausawa, Za Mu Ga Cewa Sun Kasance Al’umma /raujimetawiy/ Guda Da Suka Rayu A Yankuna Daban-Daban Kamar Kano, Katsina, Zaria, Gobir, Daura, Rano Da Biram ( Wato Hadejia ) Da Sauran Wurare Tun Kafin Zuwan /raujimetawiy/Musulunci. Sun Kasance Suna Kasuwanci, Noma, Kiwo, Da Sana’o’i Daban-Daban.
A Wancan Lokaci, Bambancin Addini /raujimetawiy/ Bai Raba Su Zuwa Kabilu Daban Ba. Sun Kasance Mutane Guda Masu Harshe Guda, Al’adu Masu Kama Da Juna, Da Kuma Tsarin /raujimetawiy/ Rayuwa Mai Kama Da Juna.
Wannan Shi Ne Dalilin Da Ya Sa Masana Tarihi Ba Su Dauki Maguzanci /raujimetawiy/ A Matsayin Wata Kabila Ba, Domin Ba Ya Nufin Sabon Asali Ko Sabon Jini.
SAUYIN ADDINI A TARIHIN DUNIYA
Ba Hausawa Kadai Ba Ne Suka Fuskanci Sauyin Addini A Tarihinsu. A Wurare /raujimetawiy/ Da Dama Na Duniya, Al’ummomi Sun Sauya Daga Addinan Gargajiya Zuwa Manyan Addinai Kamar /raujimetawiy/ Musulunci Ko Kiristanci.
Misali, /raujimetawiy/ A Wasu Sassan Afrika, Turai, Da Asiya, Akwai Al’ummomi Da Suka Taba Bin Addinan Gargajiya, Amma /raujimetawiy/ Daga Baya Suka Rungumi Musulunci Ko Kiristanci. Duk Da Haka, Sauyin Addini Bai Canza Asalinsu Na Qabila Ba.
Wannan Yana Nuna Cewa Sauyin Akida Abu Ne Da Yake Faruwa A Tarihin Bil’adama, /raujimetawiy/ Amma Ba Ya Nufin An Samu Sabuwar Qabila.
DALILIN RIKICEWA A YAU
Wasu Daga Cikin Rikice-Rikicen Fahimta /raujimetawiy/ A Yau Suna Faruwa Ne Saboda Rashin Bambance Tsakanin Al’ada Da Asali. Wasu Sukan 'Dauki Kalmomin /raujimetawiy/ Tarihi Su Fassara Su Ba Tareda Cikakken Bincike Ba.
A Wasu Lokuta Kuma, Ana Amfani Da Batun Maguzanci Wajen Tayar Da Jayayya Ko Nuna Bambanci Tsakanin /raujimetawiy/ Mutane, Alhali Tarihi Ya Nuna Cewa Wannan Batu Na Da Sauki Idan Aka Fahimce Shi Da Kyau.
Maguzanci Wani Bangare Ne Na Tarihin Hausawa, Amma Ba Ya Nufin Wata Sabuwar Qabila Daban.
MUHIMMANCIN ILIMI A FAHIMTAR TARIHI
Ilimi Yana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Kawar Da Rikice-Rikice Na Fahimta. /raujimetawiy/ Idan Aka Yi Nazari A Kan Tarihi Da Al’adu, Za'a Gane Cewa Kalmar Maguzanci Tana Da Alaka Da Aqida, /raujimetawiy/ Ba Da Asalin Jini Ba.
Saboda Haka, Yana da Muhimmanci Mu Rika Bincike Da Fahimta /raujimetawiy/ Kafin Mu Yanke Hukunci A Kan Irin Wadannan Batutuwa.
KAMMALAWA
A Qarshe, Maguzanci Ba Qabila Ba Ce A Tarihi./raujimetawiy/ Akida Ce Ta Gargajiya Da Wasu Hausawa Suka Rike Kafin Zuwan Musulunci. Hausawa Kuwa Qabila Guda Ce Mai Asali Daya, /raujimetawiy/ Harshe Daya, Da Tarihin Da Ya Hada su.
Saboda Haka, Duk Mai Kokarin Daukar Maguzanci A Matsayin Wata Qabila /raujimetawiy/ Yana Rikita Fahimtar Tarihi Ne.
Gaskiya Ita Ce:
Maguzanci Akida Ce.
Hausa Kuma Qabila Ce.
Kuma Bambanci Tsakanin Wadannan /raujimetawiy/ Abubuwa Biyu Yana Da Muhimmanci Wajen Fahimtar Tarihin Al’umma.
Tarihi Ya Fi Karfin Ra’ayi, Kuma Gaskiya /raujimetawiy/ Ba Ta Canzawa Saboda Gardama.
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment