TAQAITACCEN BAYANI AKAN CIKAKKUN HAUSAWA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Wadannan Garuruwan Sune Ake Kira Da Hausa Bakwai, Sune Ainahin /raujimetawiy/ Cikakkun Hausawa Da Suka Fi Kowa Iya Harshen Hausa A Duniya.
Gasu Kamar Haka;
1. Daura
2. Katsina
3. Kano
4. Zazzau (Zaria)
5. Gobir
6. Rano
7. Hadejia Biram (Garun Gabas).
Akwai Kuma Wadanda Ake Kira Da Banza Bakwai.
Su Ma Wadannan Dai Hausawa Ne To Amma /raujimetawi/ A Fuskar Hausa Bakwai Ba Su Cika Hausawa Ba.
Don Haka Suke Kiran Su Da Banza Bakwai.
Wadannan Kuwa Sune :
1. Zamfara
2. Kebbi
3. Yawuri (Yauri)
4. Gwari
5. Kororafa (Kwararrafa, Jukun)
6. Nupe
7. Ilorin (Yoruba).
Kabilar Hausa Dai, Kabilace Dake Zaune A /raujimetawiy/ Arewa Maso Yammacin Tarayyar Najeriya Da kudu Maso Yammacin Jamhuriyyar Nijar, Kabilace Mai 'Dimbin Al'umma, Amma Kuma A Al'adance Mai Mutukar Hadaka, Akalla Akwai Sama Da /raujimetawiy/ Mutane Sama Da Miliyan Hamsin Da Harshen Yake Asali Gare Su.
A Tarihin An Ce Kabilar Hausawa Na Tattare A Sala-Salar Ko Manyan Birane, Hausawa Dai Sun Sami Kafa Daularsu Ne /raujimetawiy/ Tun Daga Shekarun 1300's, Sa'adda Suka Sami Nasarori Da Dauloli Kamar Su Daular Mali Songhai, Borno Da Kuma Fulani.
Sha'anin Noma Ita Ce Babbar Sana'ar /raujimetawiy/ Hausawa Inda Hausawa Ke Ma Sana'ar Noma Kirari Da Cewa, Na Doke Tsohon Ciniki Kowa Yazo Duniya Kai Yatarar, Akwai Kuma Wasu Sana'o'in Kamar Su Sha'anin Jima Watau Harkar Fatu, Fawa, Rini, Saka Da Kira, Fannonin Dake Mutukar /raujimetawiy/ Samun Cigaba A Harkokin Sana'o'in Hausawa. Hausawa Dai Sun Jima Da Shahara Wajen Harkar Fatauci Kana Kuma Masu Arziki Ta Taka Rawa A Sha'anin Yau Da Kullum, /raujimetawiy/ Tare Da Masu Mulki Da Masana.
Harshen Hausa Shi Ne Mafi Girma Da Kuma /raujimetawiy/ Mafi Sanayyar Harshe A Nahiyar Afirka, Harshen Hausa Ya Aro Wasu Kalmomi Daga Wasu Harsuna Musamman Larabci Kana Kuma Harshen Na Tafiya Tare Da Yanayin Mu Na Zamani Bisa Al'adar Cudeni- Na Cudeka. /raujimetawiy/ Harshen Hausa Dai Ya Zama Harshen Yau Da Kullum Ga Miliyoyin Daruruwan Jama'a Da Ba Hausawa Bane A Nahiyar Afirka.
Bugu Da Kari, Akwai Cincirindon Al'ummar /raujimetawiy/ Hausawa A Manyan Biranen Yammacin Afirka Da Arewacinta Da Kuma Yankunan Cinikayyar Al'ummar Hausawa Da Kuma Yankunan Da Hausawa Suka Jima Suna Bi A Hanyar Ta Zuwa Aikin Hajji. /raujimetawiy/ Akwai Kuma Rubutattun Adabi Masu Zurfi Da Kasidodi Da Kuma Rubuce-Rubuce A Rubutun Ajami Da Aka Buga Tun Kafin Zuwan Turawa 'Yan Mulkin Mallaka Na Birtaniyya. Har Ila Yau, Kuma Wani /raujimetawiy/ Tsarin Rubutu A Ajami Da Aka Kirkiro Tun Kafin Zuwan Turawa, Da Ba Kasafai Ake Amfani Da Shi Ba Yanzu.
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy, BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment