TAQAITACCEN TARIHIN MASARAUTAR HADEJIA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Nan Kuma Nazo Gida Ne, A Matsayina Na Mahaifina/Babana Uwa Da Uba/Babansa Kaka Da Kakanaye Dukansu Haifaffun Auyo Ne, /raujimetawiy/ Sanin Masana Tarihi Auyo Dadadden Gari Ne, Da Ya Riga Hadejia Kafuwa Da Shekaru Aru-Aru, Sai Dai Abunda Auyo Ta Rasa Shine Rubutaccen Littafin Tarihinta.
Masarautar Hadejia Dadaddiyar Masarauta Ce Wadda Ta Kafu Shekaru Da Dama Da Suka Gabata, Daga Lokacin Kafuwarta Kawo Yanzu Masarautar Tayi Fice Fa Kuma Yin Suna Bisa Ga Muhimman Tarihi Da Take Dashi. Sannan Tana Daga Cikin Masarautun Da Sarakunan Hausawa Suka Mulka Kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, Kuma Tana Daya Daga Cikin Masarautun Da Suke Qarqashin Daular Usmaniyya. Daga Gabas Ya Yi Iyaka Da Tsohuwar Daular Borno Da Gorgaram, Daga Yamma Tayi Iyaka Da Masarautar Kano, Daga Kudu Kuma Ta Yi Iyaka Da Masarautar Katagum Sannan Daga Arewa Ta Yi Iyaka Da Masarautar Gumel. Birnin Masarautar Yana Cikin Garin Hadejia Dake Arewa Maso Gabashin Jigawa A Arewacin Nigeria.
Sunan Garin Ya Samo Asalinsa Daga Wani Maharbi Wadda Shine Ya Qafa Garin, Wannan Maharbi Ana Qiransa Da Suna HADE, Yana Da Matarsa Da Ake Kiranta Da Suna JIYA, Sunayen Wadannan Mutane Shi Aka Hada Ya Zama Hadejia . A Wancan Lokacin Mutanen Wasu Garuruwa In Zasu Zo sukan ce mun tafi garin Haden jiya, Wato Ana Masa Lakabi Da Sunan Matarsa. Saboda Taqaita Kalma Ta Hausawa Shine Yasa Aka Hade Sunan Ya Zama Hadejia . A Wani Littafi Da Marigayi Tafidan Hadejia Abdu Maigari Ya Rubuta Ya Bayyana Cewa ‘‘Shi Wannan Mutumin Da Ya Kafa Hadejia Wato Hade Ya Taho Ne Daga Yankin Machina.
A Yawon Farauta Da Yake Har Ya Iso Wannan Yanki, Kuma Da Ya Shigo Sai Yaga Daji Mai Ni’ima Da Tsuntsaye Da Namun Daji Ta Ko Ina, Kuma Ga Kogi Ya Fito Daga Yamma Ya Gangara Zuwa Gabas Sannan Ga ‘Ya’yan Itatuwa Kala Kala. Da Ganin Haka Sai Ya Kewaye Dajin Sosai Don Ya Samu Inda Ya Dace Ya Zauna, Sai Ya Samu Wuri Ya Qafa Gadonsa Irin Na Maharba Yaci Gaba Da Farautar Namun Daji Da Tarkon Tsuntsaye’’. Bayan Kwanaki Wannan Maharbi Yana Zaune A Wannan Wuri Sai Yayi Shawarar Ya Koma Ya Dauko Matarsa Don Suci Gaba Da Zama A Wannan Wuri. A Lokacinda Yayi Niyyar Komawa Sai Ya Debi Abinda Zai Iya Diba Na Naman Da Yayi Farautarsa Ya Dawo Garinsu Ya Dauki Matarsa Ya Koma Wannan Dajin Da Yanzu Ake Qira Da Suna Hadejia , Sai Ya Kafa Bukkarsa A Kan Jigawa Kuma Yaci Gaba Da Farautarsa A Wannan Wuri Har Mazauna Karkara Dake Kusa Da Wurin Suka San Da Zamansa Suke Zuwa Sayen Nama Da Sauran Dabbobin Daji.
Ana Haka Ne Jama’a Suka RinKa Zuwa Suna Qafa Bukkokinsu Wasu Masunta Wasu Kuma Mafarauta Da Masu Kamun Tsuntsaye Har Gari Ya Zama Gari Ake Qiransa Garun Haden Jiya, Sannan Akayi Shugabanci, Zuwa Wani Dogon Lokaci Aka Taqaita Kalmar Ta Zama Hadejia . Ance A Lokacinda Ya Zauna A Bangaren Arewa Akwai Wani Gari Da Ake Qira Hadegwaigwai Inda Yanzu Rubban Dakata Take, Sannan A Bangaren Gabas Akwai Gari Da Ake Qira Kulunfarda Inda A Da Can Yake Kan Hanyar Tandanu. A Yamma Kuma Akwai Garin Kadime Sannan A Arewa Akwai Garin Da Ake Kira Majeri, A Bangaren Kudu Kuma Akwai Garin Tunawa Wadda Yanzu Ake Qira Auyakayi. Sannan Akwai Kudiginda Hadebaqo Wadda A Lokacin Take Kusa Da Kafur, Sannan Akwai Urki Wadda Yanzu Ake Kira Unik Sannan Akwai Majawa, Da Kuma Manyan Garuruwa Irinsu Auyo, Garungabas, Kazura, Dawa Da Fagi.
A Wancan Lokacin Ance Hadejia Tana Qarqashin Daular Auyo Ne Amma Wasu Sunce A’a Tana Qarqashin Ikon Garungabas Ne Tunda Daga Can Ne Ake Nada Sarki Ake Kawoshi Hadejia, Masu Wannan Da’awa Sun Bada Labari Kamar Haka…
‘A Zamanin Sarkin Kano Yakubu Dan Abdullahi Barja Wadda Yayi Sarautar Kano A Cikin Shekarar (1452-1463), Algalfati Dan Sarkin Machina Yaje Kano Tare Da ‘Yan,uwansa Guda Uku Inda Sarkin Kanon Ya Bashi Sarautar Gaya, Dan,uwansa Na Farko Kuma Yaje Rano Sarkin Rano Ya Bashi Sarautar Dal, Na Biyun Kuma Yaje Zazzau Sarkin Zazzau Ya Bashi Sarautar Gayan, Na ukun Yazo Biram Garungabas Inda Sarkin Gabas Ya Bashi Sarautar Hadejia, Zuriyarsa Ne Sukayi Mulkin Hadejia Har Tsawon Lokacinda Sarkin Borno Mai Ali Ghaji Ya Tura Dansa Mai Idris Aloma Ya Yaki Kano, Sai Ya Biyo Ta Hadejia Ya Yake Ta Ya Cinyeta Da Yaki Da Sauran Qasashen Dake Yammacin Borno, Sai Ya Danka Ikon Hadejia Da Garungabas Da Dawa Da Fagi A Hannun Galadiman Borno, Kuma Shi Galadiman Borno Sai Ya Barsu A Rarrabe Kamar Yadda Suke Tun Farko. Sashen Auyo Ya Barshi A Hannun Sarkin Auyo, Hadejia Ya Barta A Hannun Sarkin Hadejia , Garungabas Ya Barta A Hannun Sarkin Gabas, Sannan Dawa Da Gatare Da Sauran Duk Sai Ya Barsu A Hannun Fadawansa, Amma Duk A Wurinsa Suke Karbar Umarni Kuma Shi Ake Kaiwa Albarkar Kasa Har Zuwa Tsawon Lokaci’. Koda Yake Ba’a Samu Rubutaccen Tarihi Game Da Sarakunan Hausawa Da Suka Mulki Qasar Hadejia Ba.
Ance Anyi Sarakuna Guda Talatin Da Biyu (32), Kafin Mulkin Fulani. Masarautar Hadejia Tana Da Fadin Qasa Wadda Ta Kai Murabba’in Kilo Mita Dubu Shida Da Dari Tara Da Sittin Da Uku (6963), Wannan Yanki Yana Da Shimfidaddiyar Qasa Mai Kyau Wadda Ake Kwatanta Yanayinta Da Na Kasar Chadi, Kuma Tana Da Jigayi Masu Tarin Yashi Da Kuma Kwari Mai Tabo Da Kaka Amma Bata Da Tsaunuka Ko Duwatsu. Kasar Hadejia Tana Da Kogi Wadda Ya Kasance Akwai Ruwa Kowane Lokaci, Sannan Tana Da Fadamu Masu Yawa Wadanda Suke Kafewa Lokaci Zuwa Lokaci. Kogin Kasar Hadejia Ya Taso Ne Daga Kudancin Katsina Ta Arewa Da Zaria Sannan Ya Nufi Arewa Maso Gabas Ya Shigo Ta Kasar Kano Ya Ratsa Kasar Hadejia, Sannan Ya Nufi Tafkin Chadi. Wannan Kogi Ya Ratsa Ne Ta Kudancin Hadejia Da Gabashinta, Wannan Bangare Ne Da Yake Samarda Ruwan Sha Da Kamun Kifi Da Kuma Aiwatar Da Noman Rani. A Lokacin Damina Kogin Yakan Cika Inda Yake Samarda Kananan Fadamu A Sassa Daban Daban Wadda Ake Amfani Dasu A Wajen Noman Lambu. A bangaren Noma Masarautar Hadejia Tana Gabatarda Noma A Lokuta Biyu Wato Rani Da Damina, Inda Masana Yanayin Qasa Suka Tabbatar Cewa Duk Abinda Aka Shuka A Wannan Qasar Zai Fito Yayi Kyau Da Iznin Allah Saboda Yanayin Kyawun Qasar.
GUDUNMAWAR DA MASARAUTAR HADEJIA TA BAYAR GA DAULAR USMANIYYA
Masarautar Hadejia Kamar Sauran Masarautu Ta Bada Gudunmawa Sosai Wajen Tabbatar Da Kafuwar Daular Usmaniyya, Domin Tana Daga Cikin Masarautun Da Suke Iyaka Da Daular /raujimetawiy/ Barno. Masarautar Hadejia Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Jihadin Shehu Usman Danfodiyo A Zamanin Sarkin Fulanin Hadejia Umaru. Sarkin Fulani Umaru Yana Nan Yana Sarautar Fulani Sai Suka Samu /raujimetawiy/ Labarin Jihadin Shehu Usman Danfodiyo , Bayan Yaji Labarin Jihadin Shehu Sai Ya Tara Jama’ar Fulani Sukayi Shawara Da Suje Suyi Mubaya'a Da Da'awar Shehu, /raujimetawiy/ Anan Wasu Manyan Fulani Suka Ki Yarda Da Hakan, Ciki Harda Kawunsa Mai Suna Jinagana. Sai Sarkin Fulani Umaru Ya Tura Mutanensa Qarkashin Jagorancin Dan,uwansa Malam Sambo, Sukaje Suka Miqa Mubaya'arsu Ga Shehu Da Kuma /raujimetawiy/ Nuna Goyon Baya Da Da'awarsa Ta Jaddada Addinin Musulunci. Shehu Yayi Naraba Da Zuwansu /raujimetawiy/ Kuma Ya Baiwa Sambo Tuta Kuma Yayi Musu Umarnin Shiryar Da Sauran Yankunan Nan Biyar Na Qasar Hadejia . Sannan Yacewa Laraima Ya Kula Da Yankin Gabashin /raujimetawiy/ Hadejia Inda Marma Da Fagi Da Dawa Suke Yaje Yayi Qokarin Shiryar Dasu Kan Tabarkin Addinin Musulunci. Amma Bai Bashi Tuta Ba, Sai Sukayi Bankwana Da Shehu Suka Dawo Hadejia Suka Isarda Sakon Shehu Ga /raujimetawiy/ Sarkin Fulani Umaru Suka Sanar Dashi Kyautar Da Shehu Ya Yiwa Laraima, Sai Aka Hada Laraima Da Mutane Suka Tafi Yankinda Shehu Yace Yaje /raujimetawiy/ Ya Shiryar Dasu Wato Marma Da Fagi Da Dawa. Laraima Sai Ya Zauna A Marma Saida Suka Shiryar Da Duk Mutanen Wannan Yankin, Kuma ‘Ya’yansa Ne Sukaci Gaba Da Shugabancin Wannan Yanki /raujimetawiy/ Na Gabas Har Zuwa Lokacinda Sarkin Hadejia Buhari Ya Hade Kasar Da Tasa, Wadda A Baya Madaci Ce Iyakar Hadejia Daga Gabas. /raujimetawiy/ Wannan Yana Nuna Mana Cewa Masarautar Hadejia Ta Bada Gudunmawa Game Da Tabbatar Da Daular Usmaniyya, Domin Tana Iyaka Da Daula Mai Karfin Gaske Kuma Dadaddiyar Wato Daular Kanem Borno.
A Zamanin /raujimetawiy/ Sarkin Hadejia Sambo Masarautar Ta Bada Gudunmawa Sosai Wajen Tabbatar Da Umarnin Shehu Na Jaddada Addinin Musulunci, Bayan Rasuwar Dan Uwansa /raujimetawiy/ Sarkin Fulani Umaru An Nada Dan Wansa Wato Mamman Kankiya, Wadda Shima Ya Rasu Cikin Watanni Takwas. A Lokacin Da Sarkin /raujimetawiy/ Hadejia Sambo Yayi Shekara Yana Sarautar Hadejia Sai Yayi Niyya Ya Tafi Wurin Shehu, Da Zuwansa Shehu Yayi Murna Kuma Yayi Godiya Ga Irin Qoqarin Da Sambo Yake A Kasar Hadejia . Bayan Sambo /raujimetawiy/ Yayi Kwanaki A Wurin Shehu Ya Gama Abinda Zaiyi Sai Yayi Sallama Da Shehu Yayi Shirin Dawowa Gida, Shehu Ya Qara Yin Godiya Ga Sambo Kuma Ya Baiwa Sambo Ikon Duk Wani Bafulatani /raujimetawiy/ Wadda Yake Da Jar Saniya (Aborawa) Tun Daga Bakin Dajin Rubu Har Zuwa Iyakar Kasar Barno. Daga Ban Sai Sambo Yayi Godiya Sukayi Bankwana Ya Dawo Hadejia Tare Da Mabiyansa. Wannan Kyauta Da Shehu Ya Masa Ta Ikon Duk /raujimetawiy/ Fulani Masu Jar Saniya (Aborawa) Tasa Sambo Yawan Dawainiya Domin Nemawa Wadannan Fulani Matsuguni, Kuma Har Zuwa Wannan Lokaci Duk Bafilatanin Da Ka Ganshi Da Jar Saniya Idan /raujimetawiy/ Ka Tambayeshi Zakaji Asalinsa Daga Kasar Hadejia Yake.
Sarkin Hadejia Sambo Ya Sake Faɗaɗa Qasar Hadejia Daga Gabas Har Saida Ya Mamaye Galibin Qasashen /raujimetawiy/ Da Galadiman Barno Yake Iko Dasu Suka Dawo Qarqashin Ikon Hadejia , Amma Banda Dawa Da Fagi Domin Shehu Ya Bada Su Ga Laraima. Daga Yamma Har /raujimetawiy/ Saida Ya Kai Kaugama Da Sharkawa, Da Majeri A Yamma Ta Arewa. Daga Gabas Maso Kudu Saida Yakai Har Damaturu Inda Ya Yaqi Garin, Sannan Daga Gabas Kuma Ya /raujimetawiy/ Tsaida Iyakarsa A Madachi. A Bangaren Arewa Kuwa Galibin Garuruwan Sun Bishi Ba Tare Da Wata Jayayya Ba Saida Ya Mamaye Garungabas Da Kazura Da Gatare Har /raujimetawiy/ Zuwa Iyakar Machina Da Damagaram.
Saboda Irin Gudunmawa Da Masarautar Hadejia Ta Bayar Ga Daular /raujimetawiy/ Usmaniyya, An Taba Baiwa Sarkin Hadejia Muhammadu Sarautar Sarkin Yaqin Sarkin Musulmi.
JERIN SARAKUNAN HADEJIA
ZUWA YAU ( MAY, 2026 )
Kamar Yanda Na Baku Labari A Baya Hadejia Anyi Sarakunan Hausawa Kafin Zuwan Fulani.
A Shekarar 1100 Aka Fara Mulki A Biram Wato Garun Gabas, Kuma A Shekarar 1805 Fulani Suka Fara Mulkin Hadejia. Ga Sunayen Sarakunan /raujimetawiy/ Tun Daga Shekarar 1700 Zuwa Yau Wato 2026
SARAKUNAN HAUSAWA
1, Kankarau ( 1700 )
2, Asawa
3, Mamman Bako
4, Kawu
5, Baude
6. Musa
7, Abubakar ( 1805 )
Wadannan sune wasu daga cikin Sarakunan Hausawa ( Amma Wasu Tsaban Rashin Yiwa Tarihi Adalci, Sai Suna Cewa Sarakunan Ha6e, Wato Arna, Ko A Ina Masu Suna Abubakar, Musa Da Mamman Bako Zasu Zama Ha6e/Arna/Maguzawa, Anayin Adalci Jama'ah Wajen Bada Tarihi Ko Ba Na Qabilarka/Yarenka Bane.
A Lokacin Sarkin Hadejia Na Hausawa Wato Abubakar Fulani Suka Zo Qasar Hadejia, A Karkashin Jagorancin Ardo Abdure 'Dan Jamdoji, Kuma Sarkin Hausawa Abubakar Shine Ya Basu Wurin Zama, Kuma /raujimetawiy/ Zamanin Sarkin Fulani Sambo Suka Dawo Inda Fadar Hadejia Take Yanzu. Kafin Su Kwaci Mulki A Hannun Sarakunan Hausawa
Sarakunan Fulani Sun Karbi Mulkin Hadejia /raujimetawiy/ Tun Daga Shekarar 1808 Har Zuwa Yau. Ga Jerin Sarakunan Fulani..
SARAKUNAN FULANI
1 - Umaru 'Dan Ardo Abdure
( 1805 - 1808 )
2 - Mamman Kankiya 'Dan Umaru
( 1808 - 1808 )
3 - Sambo 'Dan Ardo Abdure [ 1st.time ]
1808 - 1845 )
4 - Garko Gambo 'Dan Sambo
( 1845 - 1847 )
5 - Abdul-Qadir 'Dan Sambo
( 1847 - 1848 )
6, Sambo 'Dan Ardo Abdure [ 2nd Time ]
( 1848 - 1848 )
7 - Buhari 'Dan Sambo. [ 1st Time ]
( 1848 - 1850 )
8 - Ahmadu 'Dan Sambo
( 1850 - 1851 )
9 - Buhari 'Dan Sambo [ 2nd Time ]
( 1851 - 1863 )
10 - Umaru 'Dan Buhari
( 1863 - 1865 )
11 - Haru Bubba 'Dan Sambo
( 1865 - 1885 )
12 - Muhammadu Mai Shahada 'Dan Haru Bubba
( 1885 - 1906 )
13 - Haru Mai Karamba 'Dan Muhammadu
( 1906 - 1909 )
14 - Abdul-Qadir 'Dan Haru Mai Karamba
( 1909 - 1925 )
15 - Usman 'Dan Haru Mai Karamba
( 1925 - 1950 )
16 - Haruna 'Dan Abdul-Qadir
( 1950 - 1985 )
17 - Abubakar Maje 'Dan Haruna
( 1985 - 2002 )
18 - Adamu 'Dan Abubakar Maje
(2002 Till Date ( 2026 )
marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar el-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna
Popular Know As
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO YOLA-N
Comments
Post a Comment