006 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa.
*
In Bamu Manta Ba, A Kashi Na Biyar Munce Zamu Tashi A Inda Malam /raujimetawiy/ Littafi Yake Cewa :
وَحَرَّمَ اللَّهُ سُبْحَانَهُ وَطْءَ الْكَوافِرِ مِمَّنْ لَيْسَ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ بِمِلْكِ أَوْ نِكَاحِ
Allah Tsarki Ya Tabbata Gareshi Ya Haramta /raujimetawiy/ Saduwa/Jima'i Da Kafirai ( Masu Bautan Gumaka, Dodanni ) Wadanda Su Ahlul Kitabi Ba ( Yahudawa Da Kiristoci ) Ta Hanyar Mallaka ( Na Bayi Da Quyangi ) Ko /raujimetawiy/ Ta Hanyar Aure.
وَيَحِلُّ وَطْءُ الكِتَابِيَّاتِ بِالمٓلْكِ
Yana Halatta Saduwa/Jima'i Da Ahlul Kitabi ( Bayahudiya Ko Kirista ) Ta Hanyar /raujimetawiy/ Mallaka ( Na Baiwa Ko Quyanga )
( Domin Shari'ar /raujimetawiy/ Ta Yarda Ga Mutumin Da Yakeda Bayi Da Quyangi A Duk Lokacin Da Yaso Yana Iya Saduwa/Jima'i Da Su, Toh Anan Idan Musulmi Ne Ya Mallaki Baiwa/Quyanga Bayahudiya Ko Kirista /raujimetawiy/ Yana Iya Saduwa Da Ita, Amma Idan 'Yar Addinin Gargajiya Ce, Toh An Haneshi Da Saduwa Da Ita. )
وَيحِلُّ وَطْءُ حَرَائِرِهِنَّ باِلنِكَاحِ
Yana Halatta ( Ga Mutum ) Saduwa/Jima'i Da 'Yantattunsu Ta Hanyar Yin Aure.
( Wato Mutum Musulmi Yana Iya Auren Bayahudiya Ko Kirista Wacce Ba /raujimetawiy/ Baiwa Ba, Dole Kuma Idan Aure Ya Shiga Saduwa/Jima'i Zai Biyo Baya )
وَلاَ يَحِلُّ وَطْءُ إِمَائِهِنَّ بِالنِّكَاحِ لِحُرِّ ولاَ لِعَبْدِِ
Baya Halatta Saduwa Da Bayinsu/Quyanginsu Ta Hanyar Aure, Ga Mutum 'Yantacce Ko Bawa.
( Wato Baya Kamata Ga Mutum Musulmi /raujimetawiy/ 'Yantacce Ko Bawa Yaje Ya Auri Bayin/Quyangin Yahudawa Ko Kiristoci, Balle Aje Ga Saduwa/Jima'i )
Idan Muka Je Ga
MUWADDA MALIK
KITABUL NIKAHI
16 BABU NAHYU ANIN NIKAHI I'MA'I AHLUL KITABI
HADISI NA 1148
Imam Malik Ya Kawo Taqaitattun Aya Guda Biyu,
( Suratul Ma'idah Da Suratul Nisa'i )
Hani Akan Hakan.
ولاَ تَتَزَوَّجُ المَرْأَةَ عَبْدَهَا وَلاَ عَبْدَ وَلِدَهَا
Mace Kada Ta Auri Bawanta, Ko Bawan 'Danta
( Anyi Hani Da Hakan, Saboda Ita Matar /raujimetawiy/ Itace Take Da Haqqin Ciyar Dashi, Idan Ta Aureshi Waye Zai Ciyar Da Wani Kenan? Amma Idan Ta 'Yantar Dashi Da Sana'ah, Tana Iya /raujimetawiy/ Aurenshi.
وَلاَ الرَّجُلُ أَمَتَهُ، ولاَ أَمَةَ وَلَدِهِ
( Hakan An Hana ) Mutum Ya Auri Baiwarsa /raujimetawiy/ Ko Baiwar 'Dansa / Yaronsa ( Amma Indai Akwai Soyayya Ta Gaikiya, Mutum Yana Iya 'Yantar Da Baiwarsa, Ya Aureta )
وَلَهُ أَنْ يَتَزَوَّجَ أَمَةَ وَالِدِهِ وَأَمَةَ أَمِّهِ
( Malam Yace : ) Amma Yana Iya Auran, Baiwar /raujimetawiy/ Babansa, Ko Baiwar Mamansa ( Amma Dangane Da Baiwar Babansa Za'a Duba A Gani Shin Baban Bai Ta6a Saduwa/Jima'i Da Ita Ba, /raujimetawiy/ )
.
ولهُ أنْ يَتَزَوَّجَ بِنْتَ امْرَأَةِ أَبِيْهِ مِنْ رَجُلِ غَيْرِهِ
Hakan /raujimetawiy/ Mutum Yana Iya Auran Yarinyar Matar Babanshi, Wanda Ita Yarinyar Babanta Daban.
وتَتَزَوَّجُ المَرْأَةُ ابنَ زَوْجَةِ أبِيهَا مٓنْ رَجُلِِ غيْرِهِ
Hakanan Mace Tana Iya Auren Yaron Mijin Mamanta Wanda Babansa /raujimetawiy/ Daban.
*
وَيَجُوزُ لِلْحُرِّ والْعَبْدِ نِكَاحُ أَرْبَعِ حَرَائِرَ مُسْلِمَاتِِ أوْ كِتَابيَّاتِ
Yana /raujimetawiy/ Halatta Ga Mutum 'Da ( 'Yantacce ) Da Bawa Su Auri, Mata Guda Hudu Musulmai 'Yantattu, Ko Kuma Su Auri Ahlul Kibati /raujimetawiy/ ( Bayahudiya Ko Kirista )
وَلِلْعَبْدِ نِكَاحُ أَرْبَعِ إِمَاءِ مُسْلِمَاتِ
Hakan Bawa Yana Iya Auren Mata Bayi Guda Hudu ( Inya Ga Dama, Guda 4 Ko 3 Ko 2 Ko Kuma Guda 1 )
وَلِلْحُرِّ ذَلِكَ إِنْ خَشِيَ العَنَتَ، وَلَمْ يَجِدْ لِلحَٕرَائِرِ طَوْلاََ.
Hakan Mutum 'Da 'Yantacce Yana Iya Auren ( Mata Bayi ) Inya Ji Tsoron Fadawa/Afkawa Zina,
In Bai /raujimetawiy/ Samu Mata 'Yantattu Ba, Da Zai Iya Aurensu, Saboda Rashin Kudi ( Sai Ya Auri Bayin )
*
وَلْيَغْدِلْ بيْنَ نِسَائِهِ، وَعَلَيْهِ النَّفَقَةُ والسُكْنَى بِقَدْرِ وُجُودِهِ
( Shi Miji Dole Ne Akansa ) Yayi Adalci A Tsakanin /raujimetawiy/ Matansa ( In Matansa Biyu Ne, Zuwa Hudu, Domin Rashin Yin Adalci Hadisi Ya Fada Mana : Mutum /raujimetawiy/ Zai Tashi Gobe Qiyama Da Shanyayyen Gefe Daya )
Ciyarwa Da Matsuguni/Gida Yana Kanshi ( Shi Miji ) Gwargwadon Samunshi.
وَلاَ قَسَمَ فِى الْمَبِيْتِ لِأَمَتِهِ وَلاَ لِأُمِ ولٕدِهِ
Babu Rabon /raujimetawiy/ Kwana Ga Baiwarsa Ko Uwar 'Dansa ( Mutum Yake Da Mata Da Bayi Mata Da Kuma Baiwar Da Ta Haifa Masa Yaro, /raujimetawiy/ Toh Anan Mutum Bazai Raba Kwanaki A Tsakaninsu Ba, Saboda Su Wadancan Bayinsa Ne, Yana Da Daman Saduwa/Jima'i Dasu A Duk Lokacin /raujimetawiy/ Da Ya Ga Dama, A Tsakanin Matansa Ne Zaiyi Wannan Rabiyar Kwanakin )
ولاَ نَفَقَةَ لِلزَّوْجَةِ حَتَّى يَدْخُلَ بِهَا، أوْ يُدْعَى إلَى الدُّخُّولُ،
Babu Ciyarwa Akan Miji Har Sai Ya Sadu/Jima'i Da Ita ( Kamar Idan An 'Daura Aure, Toh A Wannan Lokacin Angon /raujimetawiy/ Ciyar Da Amaryar Bai Hau Kansa Tukun, Har Sai An Samu Saduwa/Jima'i A Tsakaninsu )
Ko Kuma Ya Nemata Izuwa Saduwan/Jima'in,
وهِيَ مِمَّنْ يُوطَأُّ مِثّلُهَا.
Ita Kuma Matar Itace Wacce Takai A Sadu/Jima'i Da /raujimetawiy/ Ita.
*
Insha Allahu Kuma A Kashi Na Bakwai Zamu /raujimetawiy/ Tashi A Inda Malam Yake Cewa
ونكاح التفويض جائز
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
23'Zul-Hajj 1447 Hijrah
08 June 2026 Miladiyyah
Ranar Litinin
2pm
**
marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Bini Alhajj Umar Bini Muhammad Bini Haruna.
( Wanda Akafi Sani Da )
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment