008 TAQAITACCEN BAYANI AKAN AURE, SAKI, BIKO, ZIHARI, ILA'I, LI'ANI, KUL'I DA KUMA SHAYARWA


@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*** *** ***   *** *** ***   *** *** ***
A Gurguje Insha Allahu Zamu 'Dan Ta6a Bayani Akan AURE, SAKI ETC
Daga /raujimetawiy/ Littafin Da Ake Qira Da RISALA Wanda 
Abu Muhammad Abdullahi Bini Abiy Zaideen Al-Qirawaniy RH Ya Wallafa.
*
A Gurguje In Bamu Manta Ba, Munce A Kashi Na Bakwai Munce Insha Allahu /raujimetawiy/ Zamu Tashi A Inda Malam RH Yake Cewa
*
وَلاَ يَجُوزُ نِكَاحُ الْمُحْرِمِ لِنَفْسِهِ وَلاَ يَعْقِدُ نِكَاحََا لِغَيْرِهِ
Baya /raujimetawiy/ Halatta Ga Wanda Ya 'Daura Haramin ( Aikin Hajji ) Ya 'Daurawa Kansa Aure Ko Ya 'Daurawa /raujimetawiy/ Waninsa Aure.
Hakanan In Mun Koma 
MINHAJUL MUSLIM
Shafi Na 343
Bugun Darul Fikr
Zamuga
٤ - نكاح المحرم
Auren Mai Harami
وهو أن يتزوج الرجل، وهو محرم بحج أو عمرة قبل التحلل منهما
Shine Mutum Yayi /raujimetawiy/ Aure Yana Mai ( Sanye Da Kayan ) Harami Na Aikin Hajji Ko Umrah
وحكم هذا النكاح البطلان 
Hukuncin Wannan /raujimetawiy/ Auren ( Aure Ne ) Batacce
ثم إذا أراد التزوج بها جدد عقدها بعد انقضاء حجة أو عمرته
Sannan Idan Nufin/Niyyan Sake Aure Da /raujimetawiy/ Ita, Sai Ya Sake/Qubla /raujimetawiy/ Auren Bayan Ya Qare/Gama Aikin Hajji Ko Aikin Umransa,
لقوله صلى الله عليه وسلم " لاَ يَنْكِحُ المُحْرِمُ ولاَ يُنْكَحُ " رواه مسلم
أي لا يعقد عقد نكاح له، ولا يعقد لغيره 
والنهى هنا التحريم
Saboda Fadin MANZON ALLAH S.A.W " Mai Harami ( Wanda Ya Daura Haramin /raujimetawiy/ Aikin Hajji Ko Umrah ) Ba Ya Aure, Kuma Ba Ya Aurarwa " Muslim
Shine Bazai 'Daurawa Kansa Aure Ba, Kuma Bazai 'Daurawa Wani Aure Ba.
Hani Anan /raujimetawiy/ Shine Saboda 'Daura Harami Da Yayi.
وَلاَ يَجُوزُ نِكَاحُ المَريضِ وَيُفْسَخُ، وَإِنْ بَنَى بِهَا فَلَهَا الصَّدَاقُ فِى الثُلُثُ مُبَدَّأَ
Baya Halatta Auren Mara Lafiya, ( Kuma Idan /raujimetawiy/ An Daura Za'a Warware ( Auren ) Idan Mijin/Angon Ya Sadu/Jima'i Da Ita Toh Taci Daya-Bisa-Uku Sadakin, Za'a Bata Kafin /raujimetawiy/ A Warware
وَلاَ مِيرَاثَ لَهَا
Kuma /raujimetawiy/ Batada Gado
( Anan Akwai Buqatar, Idan Za'a 'Daura Aure Tsakanin Mace Da Namiji, A Tabbatar Suna Lafiya Qalau, Babu Koda Zazza6i A Jikinsu Balle Sauran /raujimetawiy/ Cututtuka Manya Manya )
وَلَوْ طَلَقَ المَرٓيضُ امْرَأَتَهُ لزِمَهُ ذَلِكَ وَكَانَ لَهَا المِيرَاثُ مِنْهُ إِنْ مَاتَ فِى مَرَضِهِ ذَلِكَ
Inda Mara /raujimetawiy/ Lafiya Zai Saki Matarsa ( Jinyar Da Yake Cikin Hankalinsa ) Toh Sakin Ya Lazimceshi Wato Sakin Ya Saku,
Idan Ya Rasu A Wannan Rashin Lafiyar, Daya Saketa Tanada /raujimetawiy/ Gadonsa.
*
ومَنْ طَلَّقَ امْرَأَتِهِ ثَلاَثََا لَمْ تَحِلَّ لَهُ بِمِلْكِِ ولاَ نِكَاحِ حَتَّى تَنْكِحَ زَوْجََا غَيرَهُ
Wanda Ya Saki Matarsa Saki Uku, Toh /raujimetawiy/ Bata Halatta A Gareshi ( Ya Sake Saduwa/Jima'i ) Da Ita, Ta Hanyar Mallaka ( Na Baiwa ) Ko Ta Aure, Har Sai Ta Auri Wani Mijin /raujimetawiy/ Daban.
Saboda Al-qur'ani Mai Girma Yace
ﻓَﺈِﻥْ ﻃَﻠَّﻘَﻬَﺎ ﻓَﻼَ ﺗَﺤِﻞُّ ﻟَﻪُ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪُ ﺣَﺘَّﻰٰ ﺗَﻨْﻜِﺢَ ﺯَﻭْﺟًﺎ ﻏَﻴْﺮَﻩُ ) سورة البقرة
Idan Ka Saketa ( Saki Uku ) Toh Bata Halatta A Gareshi ( Ya Sadu Da Ita, Ko Ya Sake Aureta ) Har Sai Ta Auri Wani Mijin Waninsa ) Suratul Baqara.
*
وَطَلاَقُ الثَّلاَثَ فِى كَلِمَةِ وَاحِدَةِِ بِدْعَةُُ، وَيَلْزَمُهُ وإِنْ وَقَعَ
Yin Saki Uku Cikin Kalma Daya Bidi'ah /raujimetawiy/ Ne, ( Idan Hakan Ya Faru ) Ya Lazimceshi Wato Sakin Ya Yu
( Amma Hukuncin Saki Uku A Kalma 'Daya Akwai Zantuka Akai, Sai Ku Tuntu6i Malam Kusa Da Ku,Domin Warware Wannan Matsalar )
وطَلاَقُُ السُّنَةِ مُبَاحِ وَهُوَ أَنْ يُطَلِّقَهَا فِى طُهْرِِ لَمْ يَقْرَبُهَا فِيهِ طَلْقَةُُ
Saki Na Sunnah Shine Mutum Ya Saki Matarsa Tana Cikin Tsarki, Tsarkin /raujimetawiy/ Da Bai Kusanceta Ba ( Da Saduwa/Jima'i ) ( Idan Zaiyi Sakin ) Saki Daya Zaiyi,
ثُمَّ لاَ يَتْبِعَهَا طَلاَقََا حَتَّى تَنْقَضِيَ العدَّةُ، وَلَهُ الرَّجْعَةُ فِى التَّى تَحِيضُ مَا لَمْ تَدْخُلُ فِى الحَيْضَةِ الثَّالِثَةِ فِى الْحُرَّةِ أَوْ الثَّانِيَةِ فِى الأَمَةِ
( Idan /raujimetawiy/ Yayi Saki 'Dayan ) Bazai Sake Bin Ta Da Wani Sakin Ba, Har Sai Ta Gama Idda, ( Amma Idan Tana Cikin Iddan ) Yana Iya Maida Ita ( Wato : Biko Ko Kome ) Muddin Bata Shiga Idda Na Uku ba, Idan /raujimetawiy/ ( Matar ) 'Ya Ce / 'Yantacce Ce ( Ba Baiwa Ba ) Idan Kuma Baiwa Ce Idda Biyu.
( Wato : Idan Mutum Ya Saki Matarsa Saki Daya Ko Biyu, Kafin Tayi Idda Sau Uku Ta Gama, Toh Yana Maida ( Biko/Komenta ) Amma /raujimetawiy/ Idan Harta Tayi Idda Sau Uku Bai Maida Ita Ba, Toh Anan Baida Daman Yin Bikonta Sai Dai Ya Sake Neman Aurenta, In Sun Dai-Daita A Sake 'Daura Musu Aure, Kuma /raujimetawiy/ Koda An Sake 'Daura Auren, Wannan Hukuncin Saki Biyun Yananan, Inda Zai Sake Sakinta Saki 'Daya, Toh Shikenan Saita Sake Auren Wani Ta Fito, Auren Ma, Ba Auren Kisan Wuta Ba /raujimetawiy/ )
*
فَإِنْ كَانَتْ مِمَّنْ لَمْ تَحِيضَ أَوْ مِمَّنْ قَدْ يَئٰسَتْ مِنَ الْمَحِيضَ طَلَّقَهَا مَتَى شَاءَ
Idan /raujimetawiy/ Ta Kasance Wacce Bata Haida Ce ( Kamar Yarinya Qarama Ce, Wacce Bata Kai Yin Idda Ba, Don A Zamanin Da Iyaye Suna Iya Aurar Da 'Ya'yansu Qana-Qana ) Ko Kuma Wacce Ta Cire Tsammani Da Yin Idda ( Saboda Girma/Tsufa, Don Akwai Lokacin Da Mace Take Kaiwa Ta Daina Yin Jini, Toh Anan Mijin ) Yana Iya Sakinta A Duk Lokacin Da Ya Ga Dama,
وَكَذَلِكَ الْحَامٓلُ وَتُرْتَجَعُ الحَامِلُ مَا لَمْ تَضَعْ 
Hakanan Mace Mai Ciki Ana Iya Bikonta Muddin Bata Haihu Ba
والمُعْتَدَّةُ بِالشُّهْرِ مَا لَمْ تَنْقَضِ
Wacce Takeyin Idda Cikin Wata 'Daya, ( Mijinta /raujimetawiy/ Yana Iya Maida Ita) Muddin Bata Gama Ba.
والأَقْرَاءُ هِيَ الأطْهَارُ 
Wal Aqra'u ( Aqra'u ) Yana Nufin Tsarki
*
وَيُنْهَى أَنْ يُطَلِّقَ فِى الحَيْضِ فَإنْ طَلَّقَ لَزِمَهُ وَيُجْبَرُ عَلَى الرَّجْعَةِ مَا لَمْ تَنْقَضِ الْعِدَّةُ
Anyi Hani Da /raujimetawiy/ Yin Saki ( Lokacin Da Mace Take Cikin ) Idda, Idan Ma Ya Saketa ( Tana Cikin Iddan ) Ya Lazimceshi Sakin Ya Yu, Amma Za'a Tilastashi Wajen Maida Da /raujimetawiy/ Ita, Muddin Bata Gama Iddan Ba
وَالَّتِى لَمْ يَدْخُلُ بِهَا يُطَلِّقُهَا مَتَى شَاءَ، والوَاحِدَةُ  تُبِينُهَا.
Wacce Ba'a Sadu/Jima'i Da Ita Ba, ( Mijinta ) Yana /raujimetawiy/ Iya Sakinta A Duk Lokacin Da Ya Gama, ( Sakinma ) Saki 'Daya 
*
وَالثَّلاَثُ تُحَرِّمُهَا إِلاَ بَعْدَ زَوْجِِ، وَمَنْ قَالَ لِزَوجَتِهِ أَنْتِ طَالِقُُ فَهِيَ وَاحدَةُُ حَتَّى يَنْوِيَ أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ
Saki Uku Tana Haramta, Sai Bayan Ta Sake Wani Aure ( Shima Bayaninsa Munyishi A Baya, Dangane /raujimetawiy/ Da Wanda Ya Saki Matarsa Saki Uku )
Wanda Yacewa Matarsa Ke Sakakkiyace, ( Toh Hukuncin Saki, Saki ) 'Daya Ne, Har Sai In Yayi Niyyan Yawaita Hakan.
*
والْخُلْعُ طَلْقَةُُ لاَ رَجْعَةِ فِيهَا وَإِنْ لَمْ يُسَمِّ طَلاَقََا إِذَا أَعْطَتْهُ شَيْئََا فَخَلَعَهَا بِهِ مِنْ نفْسِهِ
Kul'i ( Shi Kul'i ) Saki Ne Babu Biko/Kome A Cikinsa, Koda A Ba'a Ambaci ( Adadin ) Sakin Ba, Idan ( Matar ) Ta /raujimetawiy/ Wani Abu Ta Bashi, Tayi Kul'in Kanta Dashi A Wajensa,
( Shi Kul'i Yana Faruwa Ne, Idan Mace Taga Ta Gaji Da Zama Da Mijinta /raujimetawiy/ Tana So Su Rabu, Toh Tana Iya 'Daukan Wani Abu Kamar Kudi, Qadara Etc Ta Bawa Mijin Tace Ga Wannan Kaje Kayi Wani Auren, Toh Da Zarar Mijin Ya Sa Hannu Ya Kar6a, Toh Kul'i Ya Afku Saki /raujimetawiy/ Ya Afku, Koda Ba'a Ambaci Adadin Sakiba, Kuma Miji Bashida Daman Yin Biko/Kome, Sai Dai Su Sake Sabon Aure, Idan /raujimetawiy/ Idan An Samu Dai-Daito A Tsakaninsu )
*
وَمَنْ قَالَ لِزَوجَتِهِ : أَنْتِ طَالِقُُ أَلْبَتَّةَ فَهِىَ ثَلاَثُ دَخَلَ بِهَا أو لَمْ يَدْخُلُ،
Duk Wanda Yace Da Matarsa Ke Sakekkiyace ( Albatatun ) Yanke Take ( Hukuncinsa Hukuncin ) Saki Uku Ne, Ya Sadu Da Ita, Ko Bai/raujimetawiy/ Sadu Da Ita Ba, ( Saki Uku Ne Hukuncin )
وَإِنْ قَالَ بَرِيَّةُُ أَوْ خَلِيَّةُ أَوْ حَرَامُُ أَوْ حَبْلُكِ عَلَى غَارِبِكَ فَهِىَ ثَلاَثُُ فِى الَّتِى دَخَلَ بِهَا ، وَيُنَوَّى فِى التِى لَمْ يَدْخُلْ بِهَا.
Ko Kuma /raujimetawiy/ Idan Yace Da Matarsa Ke Ku6utacciya Ce Ko Ke Tu6a66iya Ce, Ko Ke Harumce ( A Gareni ) Ko Igiyanki ( Na Aure ) Yana Wuyanki, Toh ( Hukuncin ) Saki Uku Ne, Ga Wacce ( Mijin ) Ya Sadu/Jima'i Da Ita, Amma Wacce Bai Sadu Da Ita Ba, Zaiyi Niyya ( Wato /raujimetawiy/ Za'a Nemi Saki Nawa Yayi )
*
وَالمُطَلَّقةِ قَبْلَ البِنَاءِ لَهَا نِصْفُ الصَّدَاق إِلاَّ أَن تَعْفُوَ عَنْهُ هِيَ إِنْ كَانَتْ ثَيِبَا فإِنْ كَانَتْ بِكْرََا فَذَلِكَ إِلَى أَبِيهَا وَكَذَلِكَ السَّيِدِ فٓى أَمَتِهِ
Wacce Aka Saka /raujimetawiy/ Kafin A Sadu/Jima'i Da Ita, Toh Taci Rabin Sadaki, Sai Dai Idan Ta Yafe Masa Idan Itan Bazawara Ce, Idan Kuma /raujimetawiy/ Budurwa Ce ( Hukuncin Yafewa Ko Rashin Yafewa Yana Hannu ) Babanta, Baiwa Kuma Yana Hannun Shugabanta.
*
وَمَنْ طَلَقَ فَيَنْبَغِى لَهُ أَنْ يُمَتُعَ ولاَ يُجْبَرُ ، وَالَّتِى لَمْ يَدْخُلْ بِهَا وَقَدْ فَرَضَ لَهَا فلاَ مُتْعَةَ لَهَا وَلاَ للْمُخْتَلَعَةِ
Wacce Aka Saketa Yana Kamata Ga Shi /raujimetawiy/ ( Mijin ) Ya Bata Wani Abu Da Zata 'Dan Ji Dadi ( Wanda Zai Kore Mata Jin Takaicin Sakin ) Amma Ba Dole Bane, Amma Wacce Ba'a Sadu/Jima'i Da Ita Ba, Kuma An Ambata A Gareta Toh Babu Mutu'ah Akanta, Hakanan Wacce Akayi Kul'i Da Ita, Itama Babu Mutu'a Akanta.
( Maganan /raujimetawiy/ Bada Wani Abu Ga Mace Idan An Saketa, 
Yazo A Al-qur'ani Suratul Baqara Aya 236
 Amma Ba Dole Bane
Ga Abunda Allah Ya Ce :
ﻻَ ﺟُﻨَﺎﺡَ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﺇِﻥْ ﻃَﻠَّﻘْﺘُﻢُ اﻟﻨِّﺴَﺎءَ ﻣَﺎ ﻟَﻢْ ﺗَﻤَﺴُّﻮﻫُﻦَّ ﺃَﻭْ ﺗَﻔْﺮِﺿُﻮا ﻟَﻬُﻦَّ ﻓَﺮِﻳﻀَﺔً ۚ ﻭَﻣَﺘِّﻌُﻮﻫُﻦَّ ﻋَﻠَﻰ اﻟْﻤُﻮﺳِﻊِ ﻗَﺪَﺭُﻩُ ﻭَﻋَﻠَﻰ اﻟْﻤُﻘْﺘِﺮِ ﻗَﺪَﺭُﻩُ ﻣَﺘَﺎﻋًﺎ ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ۖ ﺣَﻘًّﺎ ﻋَﻠَﻰ اﻟْﻤُﺤْﺴِﻨِﻴﻦَ
*** *** ***    *** *** ***    *** *** ***
Masha Allah Alhamdulillahi
Duka Duka Anan Zan Tsaya Bi'izinillah.
Insha Allahu Kuma A Kashi Na Tara Kuma Zamu Tashi A Inda Malam Yake Cewa :
وإن مات عن التى لم يفرض لها ولم يبن بها فلها الميراث ولا صداق لها
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

06 Muharram 1448 Hijrah
21 June 2026 Miladiyya
Ranar Lahadi

marubuci

                  @raujimetawiy
.       Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA