MENENE BAMBAMCI TSAKANIN QABILA DA ADDINI


..
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.

A Gurguje
Bazaka Iya Sanin Dangantaka Da Alaka Dake Tsakanin Qabila Da Addini Ba /raujimetawiy/ Sai Idan Kasan Ma'anar Kowanne A Cikin Su.
 
MENE NE ADDINI?
Addini Tsarin Tafiyar Da Rayuwa Ne Ta Sigar Imani Da Bauta /raujimetawiy/ Ko Ibada Da Koyi Da Kyawawan Dabi'u Domin Samun Ingantacciyar Rayuwa. Addini Yakan Taimaka Waje Daidaita Rayuwar Al'umma /raujimetawiy/ Kauce Ma Barna Tareda Samar Da Hadinkai Ga Al'umma.

MENE NE QABILA?
Qabila Na Nufin Gungu Ko Qungiyar Wasu Al'umma ( Mutane ) Masu Asali, Yare Da Al'ada Iri 'Daya. /raujimetawiy/ Ma'ana Mutanen Da Suke Daga Tushe Daya Jini Daya.

BANBANCE BANBANCEN DAKE TSAKANIN QABILA DA ADDINI.

1-Addini Hanyar Rayuwa Ne / Qabila Asali Ne.
2 - Ana Iya Rayuwa Babu Addini / Ba'a Iya Rayuwa Ba Qabila.
3 - Addini Ya Shafi Bauta Ko Ibada / Qabila Ya Shafi Yare Da Al'ada

SHIN MUTUM YANA IYA ZAMA BABU QABILA? 
Bazai Iya Yiwuwa Mutum Ya Rayu Babu Qabila Ba, Kasancewar /raujimetawiy/ Kowane Mutum Ana Haihuwarsa Da Jinin Qabilarsa Kuma Yana Kasancewa Tsatso Ko Asalin Qabilar Da Mahaifinsa Ya Fito, Hakan Yana Nuna /raujimetawiy/ Matukar Haihuwarka Akayi To Kanada Qabila.

SHIN MUTUM YANA IYA ZAMA BABU ADDINI?
 Mutane Da Yawa Suna Rayuwa Bisa Mabanbantan Addinai Kuma /raujimetawiy/ Akwai Wasu Mutane Da Basuda Wani Addini Da Suke Bi Domin Shi Addini Hanyar Rayuwa Ne Data Shafi Imani Da Bauta. Don Haka Akan Sami Wadanda Basu Bin Wannan /raujimetawiy/ Hanyar Rayuwa Domin Basuyi Imani Da Itaba.

SHIN DOLE KOWA SAI YANADA ADDINI KUMA YANADA QABILA?
Mutum /raujimetawiy/ Yanada Zabi Akan Addinin Da Zaibi Mai Yiwuwa Ya Zabi Kasancewa Bashida Addini Gaba Daya Don Haka Baza'a Iya Qiranshi Mabiyin Wani Addini Ba Haka Mutum Yanada Zabi Akan Qabilar Da Yakeso Yabi Musamman Qabilar Da Ta Hadiyeshi "Assimilation" Amma A Bi Diddiki Na /raujimetawiy/ Fasahar Zamani Na Zaren DNA Dole Qabilarsa Ta Asali Zata Zama Asalinsa. Wato Wajibi Ne Ya Kasance Yanada Qabila Domin Babu Wani /raujimetawiy/ Mutum Da Bashida Qabila A Duniya.
Ita Qabila Maganar Jini Ce Ba Imani Ba.

SHIN TSAKANIN QABILA DA ADDINI WANE YAFI MAHIMMANCI? A Kowane Qabila Ana Iya Samun Kowane Addini ( Imma Musulmi, Kirista, Bayahude Ko Addinin Gargajiya ) Amma A Kowane Qabila Iyakar /raujimetawiy/ Qabilar Kawai Ake Samu, Haka Zalika Addini Baya Fitar Da Mutum Daga Qabilarsa Kuma Qabila Bata Fitarda Mutum Daga Addininsa, Mutum Zai Iya Kasancewa /raujimetawiy/ Bashida Addini Amma Dole Yanada Qabila Matukar Ba Robot "Mutun-Mutumi" Bane.

marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna

( Ko Kuma )

@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA