SANA'O'IN HAUSAWA DA TASIRINSU A RAYUWA






@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*
Tsawon Qarnuka, Hausawa Sun Shahara Wajen /raujimetawiy/ Jajircewa, Neman Abin Kai, Da Gina Al’umma Mai Cike Da Tsari Da Wayewa. Ko Da Yake Noma Ne Ginshikin Tattalin Arzikin Hausawa, Al’ummomin Hausa Sun Samar Da Tarin Sana’o’i /raujimetawiy/ Na Musamman Da Suka Gina Cigabansu A Fannoni Daban-Daban. Wannan Rarraba Sana’o’i Ya Nuna /raujimetawiy/ Ingantacciyan Tsarin Zamantakewa Da Wayewar Da Al’ummar Ta Samu Tun Fil Azal.

*

1 - Malumta ( Malamai )
Malamai :- Su Ne Ginshiƙin Ilimi, Shari’a, Da Tarbiyya, Suna Gudanar Da Koyarwa, /raujimetawiy/ Rubuce-Rubuce, Da Bada Shawara Ga Masu Mulki.
( Mahaifiyar Mamana Wato Kakata : Itama Babanta Da Mamanta Malamai Ne Alarammomi, Hausawa Da /raujimetawiy/ Suka Fito Daga Gaya LGA Kano, Yawon Neman Ilimi Zama Ya Kawosu Wani Qauye Da Ake Qira Da Zaranda, Toro LGA Bauchi, /raujimetawiy/ Wanda A Can 'Yan,uwanmu Family Masu Yawa, Shi Kuma Kakan Mamanmu Yazo Nan Ngurore, Yola South LGA Adamawa Ya Zauna, Har Allah Ya Qar6i Rayuwarsa, Duk Wani /raujimetawiy/ Tsohon Zama A Ngurore Shekara 40yrs Zuwa 50yrs Yasan Waye Malam Muhammadu Mai Almajirai, Nan Anguwar Yalwa Kusa Da Babban Masallacin /raujimetawiy/ Juma'ah, Ni Mai Rubutu, 'Da/Yaro Ne Ga Jikarsa ) Ina Alfahari Da Hakan

*

2  - Fawa :- ( Mahauta / Rinjawa )
Nima Mai Rubutu Wannan Shine Sana'ar Iyayena Da Kakanayena  Ta Gefen /raujimetawiy/ Mahaifina Ni Zuriyar Mahauta Ne Daga Garin AUYO LGA JIGAWA, Ina Alfahari Da Hakan. Ina Miqa Gaisuwan Ban Girma Ga Sarkin Fawa MAL. HARUNA MUHAMMAD Sarkin Fawan Auyo
Tareda Yerima MUHAMMAD HARUNA ( WUNINI ) Abokina Tun Na Yarinta, Da Qaninsa ALI HARUNA Yarima Na II Da ILLIYA Yarima Na III
Mahauta Su Ne Masu Yanka Dabbobi Da Sarrafa Nama. Ayyukansu /raujimetawiy/ Na Samar Da Nama Kuma Su  Ba Da Kayan /raujimetawiy/ Fata Ga Majema Da Sauran Sana’o’i.

*

3 -  Kamun Kifi ( Masunta )
Masunta Na Taka Rawa A Yankunan /raujimetawiy/ Da Hausawa Ke Da Ruwa, Suna Samar Da Kifi Domin Abinci Da Kasuwanci, Sannan /raujimetawiy/ Suna Bayar Da Magunguna Musamman Na Sanyi.
( Mahaifin Mamana Wato Kakana, Shima Masunci Ne Iyaye Da Kakanaye, Hausawa Ne Da Suka Fito Daga /raujimetawiy/ Qauyen Da Ake Qirada Baginawa Jihar Kano, Allah Ya Kawo Zamansu Wani Qauye Da Ake Qira Da Guya6a, Kirfi LGA Bauchi, Wanda A Can Still Akwai /raujimetawiy/ 'Yan,uwanmu Family Da Yawa.
Daga Bisani Allah Ya Kawo Kakanmu /raujimetawiy/ Zama Anan Ngurore, Yola South LGA Adamawa Har Allah Ya Kar6i Rayuwarsa, Gamunan Jikokinsa Muna Rayuwanmu )

*

4 - Mayaqa
Mayaqa :- Su Ne Masu Kare Qasa, Masarauta, /raujimetawiy/ Da Hanyoyin Kasuwanci. Ayyukansu Suna Taimakawa Wajen Tsare Al’umma.
( Nanma Mahaifiyar Babana Wato Kakata Itama /raujimetawiy/ Ta Kasance Jinin Mayaqa Ce, Wanda Har Yanzu Danginta Su Suke Riqe Da Sarautar Magayaqin Qaramar Hukumar Auyo /raujimetawiy/ Ta Jihar Jigawa. Ina Miqa Gaisuwar Ban Girma Da Jinjina Ga Baffana ALH. MUHAMMAD MUSA ( BABA MAKANA ) Magayaqin Auyo Na VII
Tareda /raujimetawiy/ Hikiminmu ALH. UMAR MUHAMMAD BAFFA Hakimin Auyo )

*

5 -  Noma
Noma :- Shine Tushen Tattalin Arziki, Inda Ake Noman, Wake, Shinkafa, Gero, Dawa, Masara, Gyada Auduga Da Sauran Amfanin Gona Domin Ciyar Da Iyali Da Kuma Kasuwanci. /raujimetawiy/ Sana'ar Noma Itace Uba Ga Duk Sana'o'in Hausawa, Noma Shine Sana'ar Da Kowanne Bahaushe Yana Yinta.

*

6 - Saqa ( Masaqa )
Masaqa :- Sune Masu Sarrafa Auduga Xuwa Zare Gami Da Qera Tufafi /raujimetawiy/ Irinsu Gwado, Riga, Wando, Da Zani, Ta Amfani Da Fasahar Gargajiya Ta Hausawa. Saƙa Ta /raujimetawiy/ Taka Muhimmiyar Rawa A Cikin Kasuwancin Hausawa Tun Qarni Da Dama Saboda Yadda Qasar Hausa Ta Shahara A Qasashe Makwabtanta.

*

7 - Sassaqa ( Masassaqa )
Masassaqa :- Sukan /raujimetawiy/  Qera Kayan 'Daki Irinsu ( Akushi, Ƙoshiya ) Da Sauran Abubuwan Amfanin Gida, Kayan Aikin Gona, Da Siffofi Na Gine-Gine Kamar Mutum Mutumi. Sana’ar Ta Ba Da Gudummawa Ga Al’ada Da Gine-Ginen /raujimetawiy/ Hausawa.

*

8 - Qira ( Maqera )
Maqera :- Na Aikin Qera Takubba, Kibiyoyi, Gatari, Kayayyakin Noma, Da Kayan Amfanin Yau Da Kullum. Ayyukansu Sun Zama Ginshiki Ga Noma, Yaqi, Da Sauran Sana’o’i. Masana Na Qiran /raujimetawiy/  Wannan Sana'a Da Uwa Ta Duk Sana'o'in Hausawa Saboda Kusan Kowacce Sana'a Sai Da Kayan Aikin Da Maqera Suka Samar Ake Yinta.
Garin Kano Ya Kafu Ne Sanadin Maqeri Wato Kanau Wanda Ya Ke Neman /raujimetawiy/ Tama Dan Yin Ayyukan Sa Tun Sama Da Shekaru 2000.

*

9 - Farauta ( Mafarauta )
Mafarauta :-  Na Samar Da Nama, Fata, Da Sinadaran Magunguna. A Tarihi, Sukan Kasance Masu Kare Garuruwa Da Unguwanni Daga Barazanar Dabbobi Dake Shigowa Daga Dajuka. /raujimetawiy/

*

10 - Jima: Sarrafa Fata ( Majema )
Majema :- Sune Masu Goge Fata Da Sarrafa Ta Zuwa Takalmi, Jaka, Rawani, Sirdi, Kayan Ado, Da Kayan Yaqi. Aikin Fatar Kano Tayi Suna A Duniya Tun /raujimetawiy/ Tsawon Qarni Mai Yawa.

*

11 - Rini ( Marina )
Marina :- Sune Masu Rini, Musamman/raujimetawiy/  Da Rinin Indigo. Ramin Rini Na Kano Ya Zama Alama Ta Fasaha Da Kimiyyar Hausawa Tun Tsawon Zamani.

*

12 - Fatauci ( Fatake / ’Yan Kasuwa )
Masu Fatauci :- Sun Kafa Gagarumin Tsarin Kasuwanci Daga Arewacin Afirka /raujimetawiy/ Zuwa Kudancin Nahiyar, Suna Musayar Kaya Irin Su Tufafi, Zane, Hatsi, Fata, Gishiri, Da Kayan Marmari.

*

13 - Magunguna ( Magori )
Magori :- Sukan Hada Magungunan Gargajiya Ta Hanyar Amfani Da Ganye, Su /raujimetawiy/ Na Yin Magungunan Gargajiya Dan Warkarwa, Suna Ba Da Ilimin Da Aka Gada Tun Kaka Da Kakanni.

*

14 - Dukawa
Dukawa :- Su Ne /raujimetawiy/'Kwararru Wajen Aikin Samar Da Angara, Batta, Kambu, Laya, Zobba, Abun /raujimetawiy/ Hannu, Da Sauran Kayan Ado Fa Ake Yi Da Fata Ko Sauran Kayan Gargajiya. Ayyukansu Na Da Kima.

*

15 - Kida ( Makada )
Makaɗa :- Suna Furta Tarihin Al’umma, Suna 'Daukaka Jarumai, Kuma Suna Nishadantar Da Jama’a A Biki, Fada, /raujimetawiy/ Da Bukukuwan Gargajiya.

*

16 - Sadarwa  ( Sanƙira )
Sanqira :- Su Ne Masu Isar Da Saqonni, /raujimetawiy/ Sanar Da Al’amura, Da Kula Da Hukunce-Hukuncen Fada, Suna Tabbatar Da Isar Bayani Daga Masarauta Zuwa Al’umma.

*

17 - Gyartai :- Masu Aikin Qworai 
Gyartai Na Sarrafa Qworai Ta Hanyar Sassaƙa, Zane, Kyalliya, Da Qawata /raujimetawiy/ Su Zuwa Kwanduna, Kwalabe, Tuluna, Da Kayan Ado Ko Kayan 'Dauki Na  Amare.

*

18 - Wanzamai :- Masu Aikin Aski da Kananan Ayyukan Tiyata.
Wanzamai Su Ne Likitocin Gargajiya Da Ke Da Kwarewa A Fannoni Da Dama Irin Su Kaciya, Ƙaho ( Fidda Jini ), Maganin Kumburi, /raujimetawiy/ Tiyatar Qananan Ciwuka, Aski Da Gyaran Fuska, Samar Da Magungunan Ganye Masu Kare Cuta, Sana’arsu Ta Kasance Ginshiki A Kiwon Lafiyar /raujimetawiy/ Hausawa.

*

19 - Madaura :- Masu Gyaran Qashi (Orthopedic Specialists)
Madaura :- Su Ne Kwararru Wajen:
Gyara /raujimetawiy/ Qashi Da Ya Karye, Maida Ga6a Da Ta Zame Ko Gocewa, 'Daure Qashi Da itace Ko Kyalle, Amfani Da Ganye Da Wasu Sinadaran Domin Rage Zafin Jinyar Dogon /raujimetawiy/ Lokaci Har Marar Lafiya Ya Murmure

*

20 - Sana'ar Wasanni :- ( ’Yan Wasa ) Dambe Da Kokowa
Nishadin Gargajiya Yana Da Muhimmanci A Cikin Al’adun Hausa.

- DAMBE

Wasan Dambe, Wasa Ne Da Yawanci Matasa Masu Jini A Jika Ke Yi Musamman Mahauta.
Ana Rufe /raujimetawiy/ Hannu 'Daya Da Kyalle Domin Dukan Abokin Wasa.Wasan Yana Nuna Jarumta, Da Qarfi.

- KOKUWA

Sana’a Ce /raujimetawiy/ Ta Nishadi A Bukukuwa, Bikin Aure, Da Shagulgula.Wasan Yana Nuna Qarfi, Hazaka, Da Girmamawa Ga Matasa, Yana /raujimetawiy/ Taimakawa Matasa Shahara Da Samun Suna A Gari.

Langa: Wasa Ne Da Matasa Maza  Ke Yi Dan Nishaɗantar Da Kan Su.

*

Tarin Sana’o’in Hausawa Daga Noma Zuwa Fasaha, Daga Magani Zuwa Qera Kaya, Daga Ilimi Zuwa Wasanni Na Nuna Wata Al’umma Mai Cikakken /raujimetawiy/ Tsari, Wayewar Kai, Da Himmar Aiki. Bahaushe Ba Ya Yarda Da Zaman Banza, Domin Sana’a Ita Ce Ginshikin /raujimetawiy/ Mutunci, Arziki, Da Zaman Lafiya A Cikin Hausawa. 

*

A Halin /raujimetawiy/ Yanzu Wadansu Cikin Wadannan Sana'o'i Hausawa Mun Yi Watsi Da Su Saboda Sakaci Da Rashin Gane Girma Da Martabar Da Allah Ya Sawa Dukkan /raujimetawiy/ Sana'o'in Mu, Yana Da Kyau Mu Gane Cewa In Da Za Mu 'Dauko Wadannan Sana'o'i 'Daya Bayan 'Daya Mu Inganta Su To Tabbas Za Mu Yaƙi Talauci /raujimetawiy/ Da Dogaro Da Aikin Gwamnati. 

*

Qira Ga Hukumomin Gwamnati Da Su Yi /raujimetawiy/'Yunkurin Farfaɗo Da wadannan Sana'o'i Ta Hanyar Samar Da Tallafi Na Kayan Zamani Ga Waɗan Da Ke Gudanar Da Wadannan Ayyukan Domin Mu Dawo /raujimetawiy/ Da Martabar Sana'o'in Mu Na Cikin Gida Dan Cigaba Da Gogayya Da Qasashen Duniya Kamar Yadda A Baya Tun Daga Qarni Na 15th Har Zuwa Na 19th Mu Ke Gogayya Da Manyan /raujimetawiy/ Daulolin Duniya Wajen Fitar Da Kaya Da Abinci. In Har Aka Inganta Sana'o'inmu To Ba Ko Tantama Za Mu Iya Samar Da Duk Wani /raujimetawiy/ Abun Buqata Da Kan Mu A Cikin Gida Ba Tare Da Dogara Da Qasashen Waje Ba.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna

( Ko Kuma )

@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments