TAQAITACCEN TARIHIN DAURA DA JERIN SARAKUNANTA



@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.

Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen.
*
 - -- --- { TARIHIN DAURA } --- -- -
Asalin Mutanen Daura Da Kafuwar Masarautar Daura
Abu Ne /raujimetawiy/ Mawuyaci Kwarai Ace An Tabbatar Da Ainaihin Asalin Kafuwar Kowacce Irin Al'umma Ko Qasa Ba Tare Da An Ta6o Matsugunnin Farko Na 'Dan Adam Ba. Har Yanzu Dai Babu Wani Bigire / Wuri Takamaimai Inda Marubuta /raujimetawiy/ Tarihi Suka Hadu A Kan Cewa Shine Inda 'Dan Adam Ya Fara Zama; Wasu Su Ce A Nahiyar Afrika Ne; Wasu Su Ce A Qasashen Nahiyar Su Ne; Wasu Su Ce A /raujimetawiy/  Qasashen Hindu Ne; Wasu Ma Sunce A Qasashen Turai Ne Da Dai Sauran Sassa Na Qasashen Duniyarnan Tamu. Duk Da Haka, Masana Tarihi Da Masana /raujimetawiy/ 'Dabi'u Da Al'adun 'Dan Adam Da Na Qasashe Da Dauloli, Sun Hadu Akan Cewar Bigire / Wuri Na Farkon Da 'Dan Adam Ya Fara Wayewa Da Kuma /raujimetawiy/ Nuna Basira Da Hikima Da Zaman Duniya Mahaliccinsa Yayi Masa Baiwa Dasu, Shine Wurin Da Yanzu Aka Fi Sani Da Qasashen Gabas Ta Tsakiya. Daga Wannan Yanki Na Duniyanan /raujimetawiy/ Ne Zamu Gutsuri Tarihin Kafuwar Masarautar Daura Da Mutanen Daura.
*
Kusan Dukkan Litattafan Tarihin Da Sukayi /raujimetawiy/ Bayanin Kafuwar Daular Daura, Sun Tsamo Tarihinne Daga Cikin Mashahurin Kundin Tarihin Nan Da Aka Fi Sani Da Suna "GIRGAM" Wanda Akace A Halin Yanzu /raujimetawiy/ Akwai Wani Sashe Na Kundin Yana Can Damagaram. Shi Kuma Ya Kar6eshi Ne Daga Wurin Sarki Nuu A Yayin Da Yake Zaune A Zango, Sanadiyyar Aukuwar /raujimetawiy/ Mulkin Fulani A Daular Daura. Wani Sashe Na Wannan Kundi Kuma Ance Yana Wata Cibiyar Ajiyar Kayan Tarihi A Ingila. /raujimetawiy/ Shi Kuma Turawa Ne Sukayi Dabarar Daukeshi Daga Fadar Daura, A Yayin Da Duke Mulkin Qasar Nan. Har Yau Kuma /raujimetawiy/ Basu Dawo Da Shi Ba.
*
Abubuwan /raujimetawiy/ Dashi Wannan Kittafi Girgam Ya Nuna Shi Ne Cewar Tun Zamanin Kana'ana 'Dan Annabi Nuhu A.S. Mutane Ke Zaune A Wurin Da Ake Qira Falasdinu. /raujimetawiy/ Wasu Daga Cikin Wadannan Mutane Na Kan'ana Ne Suka Yi Hijira Daga Inda Suke Zaune Wato Falasdinu A Qarqashin /raujimetawiy/ Jagorancin Wani Da Ake Qira Najibu, Suka Yiwo Kudu Maso Yamma Har Sai Da Suka Iso Surin Da A Yanzu Ake Qira ( Lubayya ) Libya.
*
A Da Can Kuma Duk Wannan Sashe Yana /raujimetawiy/ Qarqashin Qasashen Misra Ne. A Wannan Wuri Ne Su Mutanen Najibu Suka Zauna Shekaru Masu Yawan Gaske, Harma Sukayi /raujimetawiy/ Auratayya Tsakaninsu Da Mutanen Da Suka Tarar A Wurin, Wato Qabilar Kibdawa (Coptics) /raujimetawiy/ Wadanda Suka Kasance Masu Baqar Fata Ne. Sun Hayayyafa Fa Wadannan Mutane, Ta Yadda Bayan Shekaru Masu Yawa, Saiya Kasance Launin Jikin Jikokin Mutanen Najib Mutanen Kan'an Ya /raujimetawiy/ Jirkice Daga Launi Irin Na Larabawa Ya Komo Na Baqaqen Mutane.
*
A Dai Dai /raujimetawiy/ Lokacin Da Najib Yayi Zango A Qasashen Masar Sai 'Dan Sa Abduk-Dar Ya Wuto Zuwa Qasashen Tura Bulus Inda Ya Zauna Na /raujimetawiy/ Wani 'Dan Lokaci Harma Ya Nemi Sarauta A 'Daya Daga Cikin Biranen Amma Mutanen Suka Qi Yarda Dasu Ba Bashi. Ganin Haka, Sai Abduldar Ya Taso Daga Qasashen Turabulus, Shi Da Mutanensa Wadanda Suka Biyoshi /raujimetawiy/ Daga Inda Suka Rabu Da Mahaifinsa Wato Masar, Suka Fuskanci Kudu. Suna Tafiya Suka Ratsa Hamadar Rairayin Nan Ta Sahara Har Suka Iso Wani Dausayi Mai Ni'ima Da Qoramu Da Ake Qira "Gigido". Wurin /raujimetawiy/ Da Akafi Sani Da Tsohon Birni. A wannan Wuri Mai ni'ima Ne Suka Tsaida Shawarsu Su Zauna.
*
Zaman Abduldar Da Mutanensa A Wannan Wuri "Dausayi" Shiya Haifar Da Kafuwar Da Garin Da Yanzu /raujimetawiy/ Aka Sani Da Sunan 'Daura'. Domin Kuwa Sanadiyar Zamansu A Wannan Wuri Mai Dausayi Da Qoramu, Yasa Suka Saki Jiki Har Suka Kafa Gari Wanda Ya Kasaita Har Ya Zama Daula Mai Fadi Wanda Ta Mamaye 'Yan Karkaru /raujimetawiy/ Dake Kusa Da Ita Harma Da Masu Nisa Da Ita.
*
Bayan Mutuwar Abduldar 'Ya'yansa Da Jikokinsa Mata Ne Suka Ringa Yin Sarautar Wannan Daular Da Ake Qira Daura. Ana /raujimetawiy/ Qiransu Da Sarautar Magajiya. Ga Sunayensu : Kufuru, Gini, Yakumo, Yakunya, Walzamu, Yanbamu, Gizir-Gizir, Innagari, Da Daurama Itace Ta Qarshe /raujimetawiy/ Da Tayi Sarauta A Tsohon Birni. Itace Ta Matsa Kudu Ta Kafa Garin Daura Na Yanzu. Daga Sunanta Ne Aka Sami Sunan Wannan Gari Daura, Kuma Sarautar Daura Ta Tashi /raujimetawiy/ Daga Magajiya Ta Koma Daurama. Bayan Mutuwarta A Daura Ga Sauran Matan Da Sukayi Sarauta : Gamata, Shata, Batatuma, Sandamata, Jamata, Hamata, Zama Da Shawata.
*
Masana Tarihi Su Suna Cewa A Zamanin Daurama Shawata Ne Bayajidda /raujimetawiy/ Yazo Daura. Domin Itace Magajiya Ta Goma Sha Bakwai Kuma Ta Qarshe A Jerin Sarautar Mata
*
Koda Yake Anyi Bayani Cewa, Abduldar /raujimetawiy/ Da Mutanensa Sun Zauna A Dausayin Gigidohar Suka Kafa Daula, Da Kuma Bayanin Qaurar Sarauniya Daurama Zuwa Inda Garin Daura /raujimetawiy/ Yake A Yanzu, Ba Wai Ana Nufin Babu Wasu Mutane Da Ke Zaune A Wannan Wuri Bane Sam Sam. A'a, Akwai Mutane Wadanda Ke Zaune A Karkara Mai Dausayi, Tun Kafin Zuwan Su Abduldar Da Mtanensa. /raujimetawiy/ Sai Dai Su Wadannan Mutane Ba Wai Suna Zaune Ne A Tattare Ba, Kowa Yana Zaune Ne Da Iyalinsa Da Danginsa.
 Galibinsu Mafarauta Ne Da Suke Haqar Tam. /raujimetawiy/ Kuma Suna Yawo Daga Wannan Wuri Zuwa Wancan. Basu Da Wani Tsari Na Shugabanci Ko Addini, Balle Wani /raujimetawiy/ Hali Na Cigaba Ko Zamantakewa Da Dabi'u Irin Na Al'ummar Da Kanta Ya Waye Ko Ya Fara Wayewa. Misali
*
Akwai Irin Wannan Mutane A Kewaye /raujimetawiy/ Da Gigido Harma Yawansu Na Farauta Da Hakar Tama Da Kuma Hanyoyin Neman Abinci Kan Dauke Su Zuwa Wurare Masu Nisa. Kamar Yanda Aka Same Su A Wurare Kamar Gindin Dutsen /raujimetawiy/ Dala A Kano, Qasashen Da Yanzu Aka Sani Da Sunayen Katsina, Rano, Gobir, Zazzau, Gaya, Garun Gabas Da Sauran Wuraren Da Suka Zamo Qasashe Hausa /raujimetawiy/  A Yau.
Tun Da Yake Irin Wadannan Mutane Ba'a Zaune Suke Wuri Gida Ba, Kuma Basu Da Tsari Na Shugabanci Saiya Kasance Suna /raujimetawiy/ Zaune Ne Cikin Tsoro Da Rashin Aminci.
*
Zuwan Abduldar Dausayin Gigido Shiya /raujimetawiy/ Haifar Da Kafuwar Daular Daura. Bayan Mutuwarsa Mata Suka Ringa Yin Sarautar Qasar Daura. Tarihin /raujimetawiy/ Da Aka Samo Daga Girgam Ya Nuna Mana Cewa Mata Goma Sha Bakwai Sukayi Sarautar Daura Kafin /raujimetawiy/ Sarauta Ta Koma Hannun Maza.
*
MASARAUTARTAR  DAURA DA JERIN SARAKUNANTA

Tun Farkon Kafuwar Masarautar Daura /raujimetawiy/ Zuwa Yau, Tayi Sarakuna Sittin ( 60 ), Tun Daga Kan Abduldari, Mutumin Daya Taso Daga Gabas Ta Tsakiya Ya Fara Kafa Ita Masarautar Ta Daura A Wani Dausayi /raujimetawiy/ Da Ake Qira 'Gigido' Kamar Yadda Yazo A Littafin Taqaitaccen Tarihin Daura Wanda Fadar Mai Martaba Sarkin Daura Ta Wallafa. Sai Dai Akwai Wata Matsala Babba Guda 'Daya Ta Rashin /raujimetawiy/ Samu Cikakken Jerin Sunayen Sarakunan Na Daura Tun Daga Dauri Zuwa Yau. Saboda Ko Shima Wakilin Tarihi Malam Mamman Siya Abubakar Cewa Yayi Ba Mu Da Cikakken Tarihin Daura Daga Lokacin Kafuwar Mulki, Sai Bayan Jihadin Shehu Usmanu 'Danfodiyo Da Ya Auku A Farkon /raujimetawiy/ Qarni Na Sha Tara Saboda Haka Ga 'Dan Abin Da Ya Samu Dangane Da Jerin Sunayen Sarakunan /raujimetawiy/ Daura.

- { RUKUNIN SARAKUNAN FARKO } -

01 - Abduldari
02 - Kufuru.
03 - Gino
04 - Yakumo
05 - Yakunya
06 - Walzamu
07 - Yanbamu
08 - Gizirgizir
09 - Innagari
10 - Daurama
11 - Gamata
12 - Shata
13 - Batatuma
14 - Sandamata
15 - Jamatu
16 - Hamata
18 - Zama
19 - Shawa
20 - Bawo
*
SARAKUNA NA BIYU
 - -- -- { SARAKUNAN FULANI } -- -- -

01 - Malam Isiyaku
02 - Malam Yusufu
03 - Malam Muhammadu Sani
04 - Malam Zubairu
05 - Malam Muhammadu Bello
06 - Malam Muhammadu Altine
07 - Malam Muhammadu Mai Gardo
08 - Buntarawa Sogiji
09 - Magajiya Murnai
*
 -- - { SARAKUNAN HAUSAWA } - --
Tun Daga Masu Gudun Hijira Har Zuwa Yau

01 - Sarkin Gwari Abdu ( Abdullahi )
02 - Sarki Lukudi 'Dan Tsoho
03 - Sarki Nuhu 'Dan Lukudi
04 - Sarki Mamman Sha 'Dan Sarkin Gwari Abdu
05 - Sarki Haruna 'Dan Sarki Lukudi
06 - Sarki 'Dan'aro 'Dan Sarkin Gwari Abdu
07 - Sarki Tafida 'Dan Sarki Nuhu
08 - Sarki Sulaiman 'Dan Sarkin Gwari Abdu
09 - Sarki Yusufu 'Dan Sarki Lukudi
10 - Sarki Tafida 'Dan Sarki Nuhu
( A Karo Na Biyu )
11 - Sarki Musa 'Dan Sarki Nuhu
12 - Sarki Abdurrahman 'Dan Sarki Musa
13 - Sarki Muhammadu Bashar
14 - Sarki Umar Faruq Umar
*

 
marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna

( Wanda Aka Fi Sani Da )

@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA