TAQAITACCEN TARIHIN GOMBE DA JERIN SARAKUNANTA



@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@

Kafin Na Yi Cikakken Bayanin Yadda Aka Samu Sunan Garin Gombe, /raujimetawiy/ Yana Da Kyau Na Yi Waiwaye, Wanda Masu Hikimar Zance Kan Ce, Shi Waiwayen Adon Tafiya Ne. Kwarai Kuwa Waiwayen Da Zan Yi Yanzu Yana Da Matukar Muhimmanci, Zai Kuma Zama Kamar Wata Fitila Mai Haske Da Zai Haska Abubuwan Da Zan Zayyano /raujimetawiy/ Daki-Daki Cikin Makunshiyar Sakin Layukan Da Za Su Biyo Baya.

Tarihi Ya Nuna Cikin Qarni Na 14 ( 14 Century ) Aka Fara Sanin Garin Gombe, /raujimetawiy/ Sai Dai Kafin Wannan Lokacin An Yi Wasu Mutane Masu Karama Da Sarauta Da Ake Qira ‘Soninke Mandigos’, Wadannan Mutane Su Ne Suka Samar Da Tsatson Garin Gombe, Kuma Mutanen /raujimetawiy/ Yankin Sudan (Tarekh-el-Sudan) Ke Musu Laqabi Da ‘Fararen Shugabanni’. 

Wadannan Mutane Ana Kuma Qiran Su Da ‘Kaya-Manga’. Sun Mulki Yammacin /raujimetawiy/ Sudan Na Wasu Qarnoni Da Dama. A cikin Kaya-Mangan An Samu Wani Mutum Da Ake Qira Bin-Kaya Mob, Wanda /raujimetawiy/ Sarki Ne A Wata Masarauta Da Ake Qira Mande, A Dai Yammacin Sudan Din, Wanda Kuma Wannan Sarki Ya Ci Zamaninsa /raujimetawiy/ A Cikin Qarni Na 10 Ne. Sarki Bin-Kaya Mob Yana Matukar Ji Da Jikansa Bin-Abubakar, Wanda Har Ta Kai Ko Quda Ba Ya So Ya Taba Shi. Ya Mayar Da Shi Dan Lelensa Kuma Shafaffe /raujimetawiy/ Da Mansa. Hakan Ce Ma Ta Sanya Kaya Mob Ya Baiwa Jikan Nasa Wani Bangare Na Masarautar /raujimetawiy/ Tasa Da Ake Qira Ukuba.

Bin-Abubakar Kaka Ne Ga Aliyu Ukuba, Wanda Shi Kuma Yake Mahaifi Ga Usman. /raujimetawiy/ Aliyu Ukuba Shahararren Malami Ne, Ya Haddace Al-kur’ani, Wanda Daga Baya Aka Hada Shi Aure Da ‘Yar Gidan Wani Attajiri A Garin Tibati, Inda Kuma Suka Haifi Usman.
Usman Ya Zauna A Kauyen Lakumma /raujimetawiy/ Kusa Da Garin Shellen, A Nan Kuma Ya Ci Gaba Da Wa’azi Don A Bi Addinin Musulunci.

Da Aka Yi Waiwaye Ne Kan Tarihinsu Game Da Addinin Musulunci, Sai Aka Gano Masarautar Kaya-Manga Sun Karbi Musulunci /raujimetawiy/ Daga Abubakar Almarobid (Sanha-Ja-Imam) Tun A Shekara Ta 1077, Bayan Almarobid Ya Kafa Daular Musulunci A Wajen.

Usman Ukuba Ya Auri Janaba ‘Yar Gidan Gongon ( Amna ), Wanda Shi Ne Sarkin Shellen. Sun Haifi Da Namiji /raujimetawiy/ Da Aka Radawa Suna Abubakar A Garin Mada ( sohon Garin Shellen ) A Shekarar 1762. Zuri’ar Da Ake Qira KAMBARIJO Ke Nan. Ma’anar Kalmar /raujimetawiy/ Kambarijo Ita Ce, Zuri’a Daga Kaya-Manga Da Kuma Mutanen Garin Shellen. Mahaifin Abubakar Ya Mutu Yana Yada Addinin Musulunci A Garin Da Daga Baya Aka San Shi Da Gombe, A Lokacin /raujimetawiy/ Garin Yana Qarqashin Masarautar Adamawa Ne. 

Bayan Mahaifin Abubakar Ya Rasu Ne, Sai Mahaifiyarsa Ta Mayar Da Shi Wajen Kakansa, Wanda A Nan Ne Kakan /raujimetawiy/ Nasa Ya Yi Masa Laqabin ‘Buba Yero’. Kalmar ‘Buba’ Na Nufin Abubakar Yayin Da ‘Yero’ Ta Samo Tsatsonta Daga Kanakuru Janafalu, Wanda Take Nufin Manyan Ko Dara-Daran Idanu. /raujimetawiy/ Kasancewar Da Ma Yana Da Manya Idanu. Sannu A Hankali, Sai Lakabin Buba Yero Ya Danne Asalin Sunansa Na Abubakar Bin-Usmanu. Ya Fara Karatun Muhammadiyarsa A Wajen Mahaifinsa, /raujimetawiy/ Sai Dai Kuma Bayan Rasuwar Mahaifinsa, Sai Ya Tafi Kukawa A Cikin Masarautar /raujimetawiy/ Barno,Inda Ya Ci Gaba Da Karatun Addini.
A Shekarar 1810 Ya Ziyarci Mujaddadi Shehu Usman 'Dan Fodiyo A Garin Degel. Sai Dai Kafin Ya Qarasa Degel Ne Ya Yada Zango A Katsina, Inda A Nan Sarkin Katsina /raujimetawiy/ Ya Ba Shi Auren ‘Yarsa Zulai. An Yi Biki Har Ma Allah Ya Azurta Su Da Da Namiji Aka Masa Suna Sulaiman ( Sarkin Gombe Na Farko, ( 1842-1844 ). Ya Sake Zuwa A Tarihi Lokacin Da Buba Yero /raujimetawiy/ Yake Zuwa Degel Ya Yada Zango A Daura, Inda A Nan Ma Sarkin Daura Ya Hada Shi Aure Da ‘Yarsa Hauwa, Wadda Ita Ce Mahaifiyar Muhammadu Kwairanga ( Sarkin Gombe Na II ). /raujimetawiy/

Tarihi /raujimetawiy/ Ya Nuna In Ka Dauke Sarki Sulaimanu Da Yake Da Tsatso Daga Katsina, Sauran Sarakunan Gombe Tsatson Masarautar /raujimetawiy/ Daura Ne. Buba Yero Ya Shafe Shekaru Goma A Wajen Shehu 'Dan Fodiyo, Wanda A Shekarar 1820 Shehu Ya Ba Shi Tuta /raujimetawiy/ Ta 5 Daga Cikin Tutoci 12 Da Ya Fara Rabawa. Buba Yero Ya Dawo Shellen Daga Nan Ya Ci Gaba Da Jihadi, Har Lokacin Da Shehu Ya Dakatar Da Shi. Daga Nan Kuma Shehu /raujimetawiy/ Ya Bayar Da Qabilar Lala Da Yungur Da Kuma Hona Ga Modibbo Adama Na Adamawa.

Daga Baya Buba Yero Da 'Dan,uwansa Sun Hada Hannu Da Kuma Qarfi Da Qarfe Wajen Ci Gaba Da Jihadi, /raujimetawiy/ Inda Suka Ci Qabilar Fali Da Yaqi, Bayan An Yi Gwajin Kwanji Da Kuma Dauki-Ba-Dadi A Garin /raujimetawiy/ Burmi Wanda Ake Qiran Yakin Da Suna
- -- --- { YAQIN BURMI NA I } --- -- -

Sun Shiga Garin Kororofa Babban Birnin Masarautar Jukun, Inda A Nan Buba Yero Ya Dora Lura Da Wajen /raujimetawiy/ A Hannun Hammaruwa, Sakamakon Zargin Da Buba Yero Ya Yi Na Cewa Za Su Iya Daukar Fansa.

Daga Nan Sai Buba Yero Ya Zauna A Wani Waje Da Ake Qira Gumbol Ribadu, Wanda /raujimetawiy/ Yanzu Yake Qarkashin Masarautar Nafada, A Cikin Shekarar 1814. Ya Zauna Har Tsawon Shekara 7. 

Daga Nan Ya Koma Yamma Da Dukku, Aka Radawa Garin Suna Gombe-Abba, /raujimetawiy/ Wanda Har Yanzu Ana Qiran Garin Da Haka.

Daga Nan Buba Yero Ya Aiki Magajin Garin Gombe-Abba, Da Ya Nemo Masa Wajen Da Zai Yi Dadin Zama. Bayan /raujimetawiy/ Ya Fita Nema Ne Ya Samo Wani Waje Kusa Da Wani Tsauni Da Yake Yamma Da Dukku, Nisan /raujimetawiy/ Wajen Daga Dukku Mil 19 Ne. 
A Nan Buba Yero Ya Gina Gida Kusa Da Wata Bishiyar Kuka Da ‘Yan Qabilar Bolewa Masu Bauta Mata Ke Qiran /raujimetawiy/ Ta Da Gombe-Memositi. Wasu Daga Cikin Bolewa Sun Sauko Daga Tsaunikansu, Suka Kuma Zauna Tare Da Fulani ( Su Buba Yero ), Daga Nan /raujimetawiy/ Kuma Aka Fara Qiran Garin Da Guru-Gombe-Memositi. 

Ana Cikin Haka Kuma Sai Auratayya Ta Shiga Tsakanin Bolewa Da Kuma Fulani.

 Da Tafiya Ta Yi Tafiya, Sai Suka Fara Qiran Garin Da Suna Gombe.

Bayan An Gina Garin Gombe Ne, Sai Kuma Ya Ci Gaba Da Jihadinsa, Inda Da Shi Da Dakarunsa, Suka Karkata /raujimetawiy/ Gami Da Sa Gabansu Arewa. A Qarshe Suka Hadu Da Dakarun Shehu 'Dan Fodiyo, Sannan Suka Tunkari Birnin Ngazargamu ( Babban Birnin Masarautar Barno ), Wanda Sun Yi Hakan /raujimetawiy/ Ne Bayan Sun Yi Galaba A Garin Darazo Da Kuma Logo.

Bayan Wannan Lokacin Ne, Sai Buba Yero Ya Samu Sa6ani Da 'Dan,uwansa Hammaruwa ( Sarkin Muri ), Wanda /raujimetawiy/ Hakan Ne Ya Zama Ummul’aba’isin Da Al’ummar Jalingo Suka Miqa Kukansu Ga Shehu Kan A Ba Su ‘Yancin /raujimetawiy/ Kansu Daga Qasar Gombe.

Shehu Ya Kar6i Kukansu, Ya Kuma Share Musu Hawaye, Inda Ya Ce Da Su Cikin ‘Kirdi’ ( Fulfulde ), Cewa Ya Ba Su ‘Yanci, Amma Har Yanzu Sun Qasa Karbar /raujimetawiy/ Tutar Jihadi, Wannan Dalilin Ne Ya Sa Har Yanzu Ake Qiran Fulanin Jalingo Da Sunan ‘Fulani-Kiri’. Buba Yero Ya Rasu A Shekarar 1841. Buba Yero Bai Yi Mulki Ba, /raujimetawiy/ Ya Dai Kafa Masarautar Gombe Ne. Bayan Ya Rasu Ne, Aka Fara Mulkin Sarauta, /raujimetawiy/ Wanda Ake Qiran Sarki Da ‘Modibbo Gombe’.
Kamar Yadda Na Yi Bayani A Baya Cewa, Buba /raujimetawiy/Yero Ya Auri Zulai ‘Yar Gidan Sarkin Katsina, Wanda A Kan Hanyar Sa Ta Dawowa Ne, /raujimetawiy/ Aka Haifa Masa Sulaimanu A Wani Waje Da Ake Qira Shani Qarkashin Ikon Biu, Wani Gari A Masarautar Barno. Sulaimanu Ne Ya Zama Sarkin Gombe Na Farko.

Bayan Buba Yero Ya Bar Garin Shani Ya Koma Gulani Ne, Matarsa Ta Biyu Hauwa ( ‘Yar Sarkin Daura ), Ta Haifa /raujimetawiy/ Masa Da Namiji, Wanda Aka Sanyawa Suna Muhammadu Kwairanga, Wanda Kuma Shi Ne Ya Zama Sarkin Gombe Na Biyu. Wannan Shi Ne Dalilin Da /raujimetawiy/ Ya Sa Ake Qiran Masarautar Gombe Da ‘Shanima Gulanima Fulbe Janafulu

 - -- --- { YAQIN BURMI NA II } --- -- -
 ( 2 Ga Watan Jimada Akir,1320 H Daidai Da 27-July 1903 )
Wannan Yakin Yana Da Matukar Mahimmanci A /raujimetawiy/ Tarihin Kafuwar Garin Gombe, Kasancewar Bayan Yaqin Ne Garin Gombe Ta Hau Wata Turba Har Zuwa Yau./raujimetawiy/ Sai Dai Kafin Nan Bari Na Dan Yi Baya Da Mai Karatu.

A Zamanin Sarkin Gombe Na Shida, Wato Umaru ( 1899-1922 ), An Samu Hauhawar Qaurar Mutane Zuwa Gombe, /raujimetawiy/ Ciki Har Da Korarru Da Tubabbun Sarakunan Arewa, Wadanda Nasara Masu /raujimetawiy/ Jajayen Kunnuwa Suka Hambarar. 

Wadanda /raujimetawiy/ Suka Hada Da Sarkin Misau Ahmadu Na II ( 1900-1902 ) Da Sarkin Keffi Magaji 'Dan Musa Da Sarkin Malle Basiru /raujimetawiy/ Da Sarkin Bida Da Dai Sauran Masu Fada A Ji Da Kuma Talakawan Da Suka Sha Alwashin /raujimetawiy/ Ba Za Su Zauna Qarkashin Mulkin Nasara Ba. 

Wadannan Sarakuna Da Kuma Sauran /raujimetawiy/ Mutane Sun Yi Kaura Daga Garuruwa Irin Su Kano Da Gombe Da Bauchi Da Misau Da /raujimetawiy/ Bida Da Sauransu. 

Sun Ce /raujimetawiy/ Ba Za Su Zauna Qarkashin Gwamnatin Sir. Fredrick Lugard Ba.
Bayan Sojojin Nasara/Kirista A Qarkashin Lugard Sun Ci Qarfin Kano Da Hadejiya Ne, Sai Suka Tattaro Hankalinsu Garin Gombe, Kasancewar /raujimetawiy/ Sun Samu Labarin Kusan Dukkan Tubabbu Da Qorarrun Sarakuna Sun Hadu /raujimetawiy/ A Garin Burmi. 

Kamar Yadda Ruwa Ba Ya Tsami A Banza Haka Nasara Ya San Tun Da Wadannan /raujimetawiy/ Sarakuna Suka Taru A Waje Daya, To Sun San Ko Ba Dade, Ko Ba Jima Komai Zai Iya Faruwa. Bugu Da Qari Ga Sultan Attahiru Ma /raujimetawiy/ Na Garin Burmi. 

Kuma Dama Sultan Attahiru Ya Samu Labarin Faransawa Suna Jiransa A Tafkin Chadi, Kasancewar Ita Ce Hanyar /raujimetawiy/ Da Yake Bi, Idan Zai Je Aikin Hajji Ko Ummara Ke Nan. Wani Zafi-A-Kan-Zafi Kuma Shi Ne, Ga Fadel-Allah ( 'Dan Gidan Rabeh ) Da Mutanensa Suna /raujimetawiy/ Jiran Sa A Kudancin Burmi. 

Kasancewar Garin Burmi Ne Da Yawancin Wadanda Suka Yi Jihadi Suke, /raujimetawiy/ Sai Suka Yi Ittifakin Ko Da Sama Da Qasa Za Su Hadu, To Sun Shirya Qare Burmi. Wannan Shi Ne Dalilin Da Sultan Attahiru /raujimetawiy/ Ya Shirya Wata Tawaga Ta Malamai Da Sojojin Yaki Da Aka Sanyawa Suna ‘Ferol’.

A Ranar 27 Ga Watan Yulin 1903, Manjo F.C Marsh Ya Iso Garin Burmi, Sannan /raujimetawiy/ Ya Yi Sansaninsa A Kusa Da Shiga Garin. Bayan Ya Yi Kwanaki Uku Ne, Sai Qazamin Yaki /raujimetawiy/ Ya Barke A Wajen, Inda Aka Yi Ta Karon-Battar-Qarfe, Fito-Na-Fito Da Kuma Dauki-Ba-Dadi.
Jinin Mayaka /raujimetawiy/ Sun Zuba, Inda A Qarshe Sojojin Nasaran Suka Yi Galaba. Sai Dai Kuma Sultan Attahiru Da Kuma Manjo F. C Marsh Duka Sun Rasa Rayukansu A /raujimetawiy/ Yakin Da Aka Yi A Garin Burmi. 

Wanda Har A Yanzu Kuma Kaburburansu Suna Garin Na Burmi.

A Cikin Shekarar 1913 Hedikwatar Gombe Ta Tashi Daga Garin Gombe Zuwa Nafada, Wanda A Cewar Nasarar/Kiristan /raujimetawiy/ Nafada Ya Fi Saukin Zuwa Daga Manyan Garuruwan Arewa Irin Su Kano Da Bauchi Da Maiduguri Da Sauransu. 

Har Ila Yau A Wannan Shekarar Aka Girke Sojoji /raujimetawiy/ Masu Lura Da Shige-Da-Fice A Kan Iyaka.

Sarkin Gombe Umaru Ya Halarci Wani Hawan /raujimetawiy/ Daba Da Aka Yi A Kano, Lokacin Da Sarki Edward Na III Da Ke Qasar Ingila Ya Kawo Ziyara Kano.

 Bayan Sarki Umaru Ya Dawo Daga Kano Ne, /raujimetawiy/ Ya Sake Zabar Wani Gari Da Ake Qira Doma Qarkashin Akko. Inda A Shekarar 1919 Aka Sake /raujimetawiy/ Radawa Garin Suna Gombe-Doma. 

A Kuma Wannan Shekarar Ce Aka Mayar /raujimetawiy/ Da Gombe-Doma Zuwa Masarautar Bauchi, Sannan Aka Rage Mata Dagatai Zuwa 3, Wanda A Da Take Da 13.
Daga Nan /raujimetawiy/ Kuma Sai Aka Dawo Garin Gombe Na Yanzu. A Qarshe Ta Zama Qaramar Hukuma, A Qarshen-Qarshe Kuma Cikin /raujimetawiy/ Shekarar 1996 Masarautar Gombe Ta Samu Jiha. A Halin Yanzu Jihar Gombe Ta Zama jiha Cikekke Da Aka Cireta Daga Jihar /raujimetawiy/ Bauchi.

JERIN SUNAYEN SARAKUNAN GOMBE

1 - Modibbo Abubakar Bubayero 'Dan Malam Usmanu
( 1804 - 1841 = 37yrs )
Dole Mu Sanyoshi A Na Farko, Domin Shine Ya Kafa Masarauta, Ya Shagaltu /raujimetawiy/ Da Da'awa Izuwa Addinin Musulunci.

2 - Sulaiman 'Dan Bubayero
( 1841 - 1844 = 3yrs )

3 - Muhammadu Kwairanga 'Dan Bubayero
( 1844 - 1881= 37yrs )

4 - Abdulkadir Zailani 'Dan Kwairanga
( 1881 - 1888 = 7yrs )

5 - Hassan 'Dan Kwairanga
( 1888 - 1895 = 7yrs )

6 - Tukur 'Dan Kwairanga
( 1895 - 1898 = 3yrs )

7 - Umaru 'Dan Kwairanga
( 1898 - 1920 = 22yrs )

8 - Haruna 'Dan Umaru
( 1920 - 1935 =15yrs )

9 - Abubakar 'Dan Umaru
( 1935 - 1984 = 48yrs )

10 - Shehu 'Dan Abubakar
( 1984 - 2014 = 30yrs )

11 - Abubakar 'Dan Shehu Abubakar
( 2014 Zuwa Yau )

Sarakuna Uku Daga Cikin Goma Kabarin Su Yana Gombe Abba. Bubayero, Kwairanga Da Tukur.
Sulaimanu /raujimetawiy/ Kabarin Sa Yana Kano.
Abdulkadir Zailani Kabarin Sa Yana Birin Bolawa.
Hassan Kabarin Sa Yana Dukku.
Sai Umaru, /raujimetawiy/ Haruna, Abubakar Da Shehu Su Kuma Kabarin Su Yana Nan A Fadar Gombe.

Muna Rokon Allah (SWA) Ya Jikan Su da Gafara, /raujimetawiy/ Allah Ya Kar6i Uzurin Su Ya Basu Aljannah Tare Da Dukkan 'Yan Uwa Musulmai /raujimetawiy/ Masu Imani.
Ameen Summa Ameen

marubuci

Abu Maryam Muhammad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar el-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna

( Which Popular Know As )

             @raujimetawiy
   Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N

Comments

Popular posts from this blog

TAQAITACCEN TARIHIN DAULAR AUYO

HAPPY BIRTHDAY TO YOU OUR DEAR FATHER, 13 APRIL

YAU SHEKARA GOMA DA RASUWA MAMANA