TAQAITACCEN TARIHIN MASARAUTAR KATSINA GIDAN KORAU
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Shi Gidan Korau Dake Cikin Gida, Korau 'Din Me Ya Gina Shi A Wajen Farko-Farkon /raujimetawiy/ Qarni Ma Goma Sha Biyar.
Korau Musulmi Ne Wanda Ake Yi Masa 'Laqabin Muhammadu Korau. Ya Fito Ne Daga Qabilar Wangarawa /raujimetawiy/ Dake Rusasshiyar Daular Mali. Shi Korau, Tare Da Jama'arsa, Sun Mamaye Qasar 'Yandoto, Wadda Ke Katsina-Laka, A Farkon Qarni Na Goma Sha Biyar. Daga Nan Kuma Suka Gangaro Katsina-Jigawa, Suka Yaqi Sarkin Katsina /raujimetawiy/ Dake Birnin Katsina Mai Suna Jibda Yaqi Sanau. Bayan Cin Nasara Yaqi, Sai Korau Ya 'Dare Qaragar Mulkin Katsina Ya Zama Sarkin Katsina /raujimetawiy/ Na Farko A Tsatson Wangarawa.
*
Kamar Yadda Bayani Ya Gabata Cewa, Korau Ne Ya Gina Gidan Sarkin Katsina /raujimetawiy/ Na Yanzu Dake Cikin Gida, Ya Zauna A Ciki Har Qarshen Rayuwarsa. Haka 'Ya'ya Da Jikoki Waɗanda Suka Yi Sarautar Katsina A Daular /raujimetawiy/ Wangarawa, Suma A Nan Suka Zauna Tun Daga Shi Korau Wanda Yayi Zamani Daga ( 1348 - 1398 )Har /raujimetawiy/ Dai A Qarshen Mulkin Wangarawa A Shekara Ta 1807.
*
Anyi Sarakunan Katsina Na Wangarawa Waken Guda Ashirin Da Tara, Kuma /raujimetawiy/ Duk A Nan Gidan Korau Wanda Ke Cikin Gida, /raujimetawiy/ Suka Yi Sarauta.
*
Muhimmai Daga Cikin Wadannan Sarakuna Na Hausawa Zuriyar Wangarawa, /raujimetawiy/ Da Suka Yi Mulkin Katsina, Daga Nan Gidan Korau Dake Cikin Gida, /raujimetawiy/ Akwai Korau Shi Kansa.
*
Akwai /raujimetawiy/ Ali Murabit, Ali Karyagiwa, Ibrahim Maje, Uban Yara, Janhazo, Gunawa Agwaragi, Sarki Gozo, Bawa Ɗangiwa, Maremawa, Magaji Halidu, Da Sauransu.
*
A Lokacin /raujimetawiy/'Mulkin Korau ( 1348 - 1398 ) Aka Gina Gidan Sarkin Katsina Da Ke Cikin Gida, A Lokacinsa Ne Aka Tabbatar Da Kafuwar /raujimetawiy/ Qasar Katsina Wadda Ta Haɗa Da Karofi, 'Yanɗaka Dur6i, Da Sauran Su, Mai Babban Birni A Katsina, Mai Fada A Cikin Gida. Ali Murabit ( 1452 - 1475 ) Daya Biyo Baya, /raujimetawiy/ Shi Yasa Aka Gina Ganuwar Qofar Soro, Wadda Ta Zagaye Gidan Korau, Wadda Aka Yiwa Qofofi Guda Biyu, Qofar /raujimetawiy/ Soro Ta Shiga Fadar Sarki, Da Qofar Bai, Ta Bayan Gidan Sarki.
*
Tun Daga Zamanin Ali Murabit Ne Aka Fara Samun Kafuwar Cikin Gida. Daga Baya /raujimetawiy/ Kuma, Ali Murabit, Ya Fara Gina Babbar Ganuwar Katsina, Wadda Ta Zagaye Duk Unguwannin Dake Cikin /raujimetawiy/ Birni Katsina.
*
Amma Ba a Qarasa Ginin Ba Sai Zamanin Ibrahim Maje (1599-1613). Shi Ibrahim Maje Baya Ga Cigaba Da Ginin /raujimetawiy/ Ganuwa, Ya Kuma Qarfafa Addinin Musulinci A Qasar Katsina Baki Dayanta, ( Saboda Tsa6ar Rashin Son Gaskiya Da Qin Hausawa, Anan Sai Kaji Ana Cewa Sarakunan Ha6e, Wato Sarakunan Arna Maguzawa, Duk Wanda Ya Kafurta Mutum Musulmi Hadisin Yana Nan Sananne, Shine Kafirinin )
*
Shi Kuma Ali Karyagiwa ( 1475 - 1525 ) Wanda Yayi Mulki Kafin Ibrahim Maje, Ya Qara Fadada Qasar /raujimetawiy/ Katsina, Inda Aka Kai Yaƙi Har Kuyambana Da Birnin Gwari Da Zamfara, /raujimetawiy/ Don Qara Samun Qasar Mulki. Umurnin Yin Hakan Ya Fito Ne Daga Fadar Cikin Gida.
*
Kuma A Zamanin Karyagiwa Aka Kar6i /raujimetawiy/ Baquncin Wani Malami Mai Suna Muhammad Bin Ahmad Al-Taszakht, Wanda Aka Fi Sani Da 'Dantakun. /raujimetawiy/ Shi 'Dantakun, Ya Zama Babban Alqali A Katsina.
*
Lokacin Mulkin Uban Yara Da Janhazo ( 1708 - 1740 ) Katsina Ta Tsunduma Cikin Yaqi Da Maqwabtanta, Musamman Ma Gobir Da Kano.
*
A Zamaninsa Ne Martabar Malaman /raujimetawiy/ Birnin Katsina, Irinsu Abu Abdullahi Bin Ghumehu Bin Nuh Al-Barnawiy, Al-Katsinawiy ( 'Danmasani ), Da Kuma 'Dayan /raujimetawiy/ Malamin Muhammadu Bin Al-Sabbagh, Al-Katsinawiy ( 'Danmasani ), Ta 'Daukaka, Wato Wadannan Malamai Suka Shahara /raujimetawiy/ A Ko'ina A Duniyar Lokacinsu.
*
Shi Kuma /raujimetawiy/ Gunawa Agwaragi ( 1779 - 1788 ), A Lokacinsa Aka Dinga Samun Hamayyar Gadon Sarauta Tsakanin 'Ya'Ya Da Jikoki Na Sarakunan /raujimetawiy/ Da Suka Gabata A Nan Cikin Gida, Wanda Har Abin Ya Kai Ga Yaqin Basasa.
*
Sarki Goza ( 1788 - 1802 ), Shi Kuma Ya Haɗu Da Fitinu Na 'Yan Cikin Birnin Katsina Da Na 'Yan Cikin Gida. Haka Aka Yi Tayi Har /raujimetawiy/ Bawa 'Dangiwa ( 1802 - 1804 ) Yazo, Wanda Shima Ya Cigaba Da Fuskantar Wannan Fitina.
*
Su 'Yan Cikin Birni Wadanda Ke Yammacin /raujimetawiy/ Cikin Gida, 'Yan Kasuwa Ne Attajirai Da Malamai Masu 'Dinbin Ilmi Da Dukiya. Su Kuma 'Yan Cikin Gida, /raujimetawiy/ Fadawan Sarki Ne Da Barorinsa, Bayinsa Da Barwansa Da Mayaqansa. Wannan Bambancin Shi Ya Kawo /raujimetawiy/ Kallon Raini Tsakani Sassan Biyu.
*
Baya Ga Wannan Sai Ga Wata Babbar Sabuwar Matsala Ta Fuskanci Bawa 'Dangiwa, Mai Fada A Cikin Gida. /raujimetawiy/ Matsalar Kuwa Itace Ta Jihadi, Wanda Ya 'Bullowa Katsina Da Masarautarta, A Qarqashin Jagorancin Mallam Ummarum Dallaje Da /raujimetawiy/ Malam Muhammadu Na'-Alhaji Da Mallam Ummaru Dumyawa.
*
Wadannan /raujimetawiy/ Mujahidai Sun Kar6o Tutar Qaddamar Da Jihadi Daga Sakkwato Ga Qasar Katsina Baki 'Dayanta, Da Masarautar /raujimetawiy/ Katsina 'Din Dake Cikin Gida. Anci Gaba Da Yin Yaqi Tsakanin Mayaƙan Jama'a Na Masu Jihadi Da Mayaƙan Sarakunan /raujimetawiy/ Katsina Har Allah Yayiwa 'Dangiwa Rasuwa. Wanda Ya Kar6i Ragamar Mulki Da Ci Gaba Da Yaqi, Shine Muhammadu Maremawa ( 1804 - 1805 ), Wanda A Wata Gwabzawar Da Akayi A Iyatawa, Aka /raujimetawiy/ Kashe Shi. Sai Magaji Halidu Ya Kar6i Sarauta, Aka Cigaba Da Yaqi.
*
A Shekarar 1807, Mayaqan Jama'a Sunci Katsina Da Yaqi, Inda Shi Magaji Halidu ( 1805 - 1807 ) Ya Tsere Zuwa /raujimetawiy/ Dankama Daga Can Sai Damagaram. Shi Kuma Ummarun Dallaje ( 1807 ), Wanda Shine Jagaban Yaqi Ya Shige Gidan Sarautar /raujimetawiy/ Gidan Korau Dake Cikin Gida, Ya Zama Sarkin Katsina Na Farko A /raujimetawiy/ Daular Usman 'Danfodiyo, A Kuma Zuriyar Fulani Na Dallazawa.
*
Daga /raujimetawiy/ Lokacin Da Ummaru Dallaje Ya Shiga Gidan Korau Dake Cikin Gidan, Daga Nan Ne Mulkin Dallazawa Ya Fara, A Shekarar /raujimetawiy/ 1807 Wanda Ya Kai Qarshe A Shekarar 1906.
*
Ummarun Dallaje, Ya Jaddada Addinin Musulinci A Qasar Katsina Baki 'Daya, Ya Kafa Mulki Irin Na Tarayya, A Inda Aka Ba Malam Muhammadu Na'Alhaji Kudu Maso Yamman /raujimetawiy/ Katsina A Matsayin 'Yandakan Katsina, Mai Fadarsa A Zakka Da Gidansa Na Mulki A 'Yantaba Dake Cikin Birnin Katsina.
*
Shi Kuma Malam Ummarun Dumyawa, /raujimetawiy/ Aka Ba Shi Mulkin Arewa Maso Yammacin Katsina, A Matsayin Sarkin Sullu6awan Katsina, Mai Fadarsa A Bugaje Da Kuma Gidan Sarautarsa Dake Sullu6awa /raujimetawiy/ Ta Qofar Guga. Shi Kuma Ummarun Dallaje Ya Zama Sarkin Katsina Gaba 'Dayanta, Mai Babbar Fadarsa /raujimetawiy/ A Gidan Korau Dake Cikin Gida.
*
Abubakar Saddiqu Shine Ya Gaji Ummarun Dallaje A Shekarar 1835, Wanda Shima, Ya Zauna, Yayi Rayuwarsa /raujimetawiy/ A Gidan Korau Na Cikin Gida. A zamanin mulkin Saddiq, An Sami Tawaye Na Maradawa, Wato Sarakuman /raujimetawiy/ Hausawa Na Katsina Wadanda Aka Ci Da Yaqi, Suka Koma Maradi. Su Wadannan Maraɗawa, Sun Quduri Aniyar Dawowa Katsina, Da Nufin /raujimetawiy/ Kar6ar Mulki Daga Hannun Fulani Dallazawa.
*
Wannan Shiya Kawo Yaqe-Yaqe A Tsakanin /raujimetawiy/ Mayaqan Maradawa Da Mayaqan Katsina A Qarqashin Jagorancin Abubakar Saddiqu Tareda Taimakon Mayaqan Kuma Manyan /raujimetawiy/ Sarakunan Fada, Irinsu Dur6i Gidado Da Abdu Nadabo, Tarno /raujimetawiy/ Gajeren Badde.
*
Bayan Rasuwar Abubakar Saddiqu, Sai Muhammadu Bello Ya 'Dare Karaga A Shekarar 1844. Shima, A Nan Gidan Korau Dake Ciki Gida Ya Zauna /raujimetawiy/ Yayi Mulkinsa. A Zamanin Bello 'Din Ne, Aka Qarfafa Harkokin Shari'a A Katsina, Aka Inganta Kar6ar Baqi Malamai /raujimetawiy/ Da 'Yan Kasuwa. Muhammadu Bello Ya Kakkafa Sababbin Jini A Mulkinsa, Irin Gidado, Tarno Gajeren Badde Da Abdu Nadabo. Wadannan Mutane /raujimetawiy/ Sune Manyan Jarumai Na Katsina, Waɗanda Suka Dinga Fafatawa Da Maradawa, Kuma Sune Manyan Fadawa /raujimetawiy/ Masu Murɗa Zare A Fadar Cikin Gida.
"
Ahmadu Rufa'i ( 1869 - 1870 ) Da Ibrahim Muhammadu Bello ( 1870 - 1882 ) Suma, Sunyi Mulkin Katsina, /raujimetawiy/ Kuma A Nan Gidan Korau Na Cikin Gida Suka Zauna Suka Rasu A Nan.
*
A Zamanin Rufa'i Ne, Yaqi Da Maradawa Ya Tsananta, Harma Ya Hana Abubuwa Na Cigaba. Ibrahim Bello Ya Zama Sarki Bayan Rasuwar Ahmadu Rufa'i A (1870). Shima Ibrahim, Ya Gaji Wannan Fitina Ta Yaqi Da Maradawa, A Qarqashinsu /raujimetawiy/ 'Danmari Da 'Danbaskare.
*
A Zamanin Sarkin Ibrahim Ne Aka Gina Qofar /raujimetawiy/ Shiga Cikin Gida, Wato Qofar Soro, Inda Akayi Mata Gini Inda Ake Wuchewa Ta Chikin Qofar /raujimetawiy/ Idan Za'a Shiga Gidan Korau. Bayan Rasuwar Ibrahim Bello, Sai Musa Ya Gaji Sarauta A Shekarar 1882, Wanda Shi Ma Yayi Rayuwarsa A Gidan Korau Na Cikin Gida. A Zamanin Musa Ne Mayan Dakarun Nan Na Katsina, Kuma Manyan Fadar Cikin Gida, /raujimetawiy/ Irinsu Durɓi Gidado Da Abdu Nadabo Suka Rasu.
*
Abubakar Ibrahim Ya Gaji Sarauta A Shekarata 1887, Wanda Shima Ya Zauna A /raujimetawiy/ Cikin Gidan Korau Na Cikin Gida. Amma Abubakar Ba a Gidan Korau Ya Rasu Ba, Domin Turawa Sun Tu6eshi Daga Sarauta, Suka Tafi Dashi Ilorin, /raujimetawiy/ A Shekarar 1925 Aka Dawo Dashi Kano A Zamanin Darkin Kano Usman 'Dan Abdullahi Maje Karofi, Sarkin Katsina Abubakar Ya Rasu A /raujimetawiy/ Kano A Shekarar 1940 Zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero. Kamar Yadda Bayani Ya Gabata, A Zamanin Abubakar Ne Turawa /raujimetawiy/ Ingilishi Suka Kama Katsina, Koda Yake Ba a Yi Yaqi Da Su Ba.
*
Bayan /raujimetawiy/ Tu6e Abubakar Da Turawa Sukayi A Dalilin Rashin Fahimtar Da Ta Shiga Tsakanin Sarki Abubakar Da Turawa, Sai /raujimetawiy/ Turawan Suka Tu6e Shi, Sukayi Masa Murabus, Suka Tafi Dashi Ilorin. Sai Suka Naɗa Muhammadu Yero Sarkin Katsina, Wanda Shima, Ya 'Dan Zauna A Gidan Korau Na Cikin Gida, Kafin /raujimetawiy/ Abinda Ya Dami Abubakar, Shima Ya Same Shi. Turawa Sun Tuhume Shi Da Rashin Iya Aiki Wanda A Wannan Dalili Suka /raujimetawiy/ Tu6eshi, Suka Kai Shi Lakwaja.
*
Wannan Al'amari Ya Auku Ne A Shekara /raujimetawiy/ Ta 1906. Wannan Ne Kuma Ya Kawo Qarshen Mulkin Qasar Katsina Da Dallazawa Suka Yi /raujimetawiy/ Daga Gidan Korau Na Cikin Gida.
*
Muhammadu Dikko, 'Dan Durɓi Gidado, Ya Zama Sarkin Katsina Na Farko A Tsatson Fulani Sullu6awa. Shi Dikko, Turawa Ne Suka Nada Shi, Ya Zama Sarkin Katsina A Shekarar 1906, Bayan /raujimetawiy/ Tu6e Muhammadu Yero Da Aka Yi.
*
A Zamanin Muhammadu Dikko Ne Aka Matso Da Qofar Shiga Cikin Gida, Wato Qofar Soro Inda Take A Yanzu, Aka Yi Mata Ginin Dutse Da Tagogi, Aka Kuma Yi Mata Bene Wanda A Katsina Ake Qira Soro. Daga /raujimetawiy/ Manne Ma, Qofar Ta Sami Sunan Qofar Soro, Wato Qofa Mai Nene Ko Soro. Daga Baya, An Kuma Riƙa Qiran Qofar Da Sunan Kan-Giwa, Saboda /raujimetawiy/ Wannan Soron Yana Kama Da Kan Giwa Da Aka Sani. Qofar An Danya Mata Agogo, Wadda A Da, Take Bugawa Duk Bayan Awa Guda, Wadda /raujimetawiy/ Ake Jin Qarar Bugawar A Ko'ina Cikin Birnin Katsina.
*
A zaminin Dikko Ne, Aka Gyara Filin Dake Gaban Kan-Giwa Ko Ƙofar Soro, /raujimetawiy/ Ya Zama Filin Yin Jahi Ran Salla Qara A Ko Babba, Da Kuma Yiwa Hakimai Da Jama'ar Katsina Da Suka Taru A Wurin Jawabi. A Yamma Da Filin Aka Yi Ofishin 'Yan Doka, Wanda Ya Zama Ofishin 'Yan Sanda A Yanzu. A Arewa Da /raujimetawiy/ Filin Kan-Giwa Ko Qofar Soro, Aka Gina 'Dakunan Shari'a Na Alqali Babba Da Alƙali Qarami, Wanda Kafin Wannan Lokacin, A Zauruka Ake Yin Shari'ar.
*
An Kuma Gina Sakatariya Ta Ma'aikatan En'e Ta Katsina. A Kudu Kuwa, Da Filin Na Ƙofar Soro, Aka Gina Ma'aikatar Wakshof Inda Ake Yin Kere-Kere. A Can Gaba Da Ma'aikatar /raujimetawiy/ Aka Gina Babban Masallacin Juma'a Na Uku A Katsina. Dikko Yayi Gaba 'Dayan Rayuwarsa A Gidan Korau Dake Cikin Gida, Kuma Ya Rasu A Nan A Shekarar 1944.
*
Wanda Ya Gaji Muhammadu Dikko Shine Ma Kamar Mahaifinsa, Ya Zauna /raujimetawiy/ A Gidan Korau.
*
A Zamanin Usman Nagogo, An Qarfafa /raujimetawiy/ Bayar Da Ilmin Boko Da Buɗe Makarantun Boko A Birni Da Qauye Na Faɗin Qasar Katsina. Sarki Usman Nagogo Ya Tasu A Shekara Ta 1981. Wanda Ya Gaji Sarki Usman, Shine /raujimetawiy/ Muhammadu Kabir Usman A Shekara Ta 1981. A Zamanin Mulkin Kabir Usman Ne, Qasar Katsina Ta Sami Jihar Kanta A Shekara Ta 1987, Wanda A Dalilin Haka, Garin Katsina Da Wurare Da Dama A Jihar, Suka Sami Cigaba. Abdulmumin Kabir Usman, Shiya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Sarki. Kamar /raujimetawiy/ Sauran Sarakunan Katsina, Shima A Gidan Korau Na Cikin Gida Yake Zaune.
*
Abin Lura A Nan, Game Da Gidan Korau Na Cikin Gida Shi Ne, Duk Ilahirin /raujimetawiy/ Sarakunan Katsina, Tun Daga Hausawa Na Xuriyar Korau Na Wangarawa, Har Zuwa Fulani Dallazawa, Zuwa Fulani Sulluɓawa, Dukkaninsu A Gidan Korau 'Din Ne /raujimetawiy/ Suka Zauna, Suka Yi Sarauta, Kuma Wata Qila, Suka Rasu A Nan, Inka 'Debe Abubakar Saddiƙu Wanda Aka Tuɓe Daga /raujimetawiy/ Sarautar Katsina, Aka Tafi Dashi Qasar Sakkwato, Da Abubakar Ibahim Da Muhammadu Yero Wadanda Turawa /raujimetawiy/ Suka Tafi Sa Su Wani Wuri Na Daban.
*
Abin Lura Na Biyu, Shine, Gidan Korau Wanda Aka Gina A Farko-Farkon Qarni /raujimetawiy/ Na Goma Sha Biyar, Yana Da Wajen Shekara Dari Biyar ( 500 ) Da Ginawa.
Allah Ya Gafartawa Magabatanmu
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
JERIN SUNAYEN SARAKUNAN KATSINA
01 - Kumayo,
02 - Rumbarumba,
03 - Bataretare
04 - Korau
05 - Jin-Narata
06 - Yanka Tsari
07 - Jid-Da Yaki ( Sanau )
08 - Muhammadu korau
( 1348 - 1398 )
09 - Usman Maje
( 1393 - 1405 )
10 - Ibrahim Soro
( 1405 - 1408 )
11 - Marubuci
(1408 - 1426 )
12 - Muhammadu Turare
( 1426 - 1436 )
13 - Ali Murabus
( 1436 - 1462 )
14 - Ali Karya Giwa
( 1462 - 1475 )
15. Usman Tsaga Rana I
( 1475 - 1525 )
16. Usman Sa-Damisa Gudu
( 1525 - 1531 )
17 - Ibrahim Maje
( 1531 - 1599)
18 - Malam Yusufu
( 1599 - 1613 )
19 - Abdulkadir
( 1613 - 1615 )
20 - Ashafa
( 1615 - 1615)
21 - Gabdo
( 1615 - 1625 )
22 - Muhammadu Warri
( 1625 - 1637 )
23 - Tsaga Rana I
( 1637 - 1649 )
24 - Mai Karaye
( 1646 - 1660 )
25 - Suleiman
( 1660 - 1673 )
26 - Usman Tsaga Rana II
( 1673 - 1692 )
27 - Muhammadu Toyariru
( 1692 - 1705 )
28 - Yanka Tsari
( 1705 - 1708 )
29 - Uban Yara
( 1708 - 1740 )
30 - Jan-Hazo Dan-Uban Yara
( 1740 - 1751 )
31 - Tsaga Rana II
( 1751 - 1764 )
32 - Muhammadu Kayiba
( 1764 - 1771 )
33 - Karya Giwa
( 1771 - 1788 )
34 - Giwa Agwaragi
( 1789 - 1802 )
35. Gozo
( 1802 - 1804 )
36 - Bawa Danguwa
( 1804 - 1805 )
37 - Muhammadu Maremawa
( 1805 - 1806 )
38 - Magajin Haladu
( 1806 - 1807 )
39 - Ummarun Dallaji
( 1807 - 1835 )
40 - Abubakar Saddiku
( 1835 - 1844 )
41 - Muhammadu Bello
( 1844 - 1869)
42 - Amadu Rufa'I
( 1869 - 1869 )
43 - Ibrahim
( 1869 - 1882 )
44 - Musa
( 1882 - 1887 )
45 - Abubakar
( 1887 - 1905 )
46. Yero Dan Musa
( 1905 - 1906 )
47 - Muhammadu Dikko
( 1907-1944 )
48 - Usman Nagogo
(1944-1981),
49 - Kabir Usman
( 1982 - 2008)
50. Abdulmumin Kabir Usman
( 2008 Till Date June, 2026 )
marubuci
Abu Maryam Muhammad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna
( Wanda Aka Fi Sani Da )
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment