TAQAITACCEN TARIHIN RAYUWAR IBB DA MULKINSA
IBRAHIM BADAMASI BABANGIDA
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
Janar Ibrahim Badamasi Babangida ( Wanda Akafi Sani Da IBB ) Yana Daya /raujimetawiy/Daga Cikin Shuwagabannin Soja Mafi Kwarjini, Fada A Ji, Da Kuma Sarkakiya A Tarihin Siyasar Najeriya. Ya Gudanar Da Mulkin Kama-Karya Na Soja Na /raujimetawiy/ Tsawon Shekaru Takwas.
1 - Farkon Rayuwa Da Siyasa
Haihuwa: An Haifi IBB A Ranar 17 Ga Agusta, 1941 A Garin Minna, Jihar Niger. /raujimetawiy/ Ya Rasa Mahaifansa Biyu Tun Yana Dan Shekara 14.
Karatu: Yayi Makarantar Firamare Ta /raujimetawiy/ Gwari Native Authority Dake Minna, Sanna Ya Halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati Ta /raujimetawiy/ Bida ( Government College Bida ).
*
Aikin Soja : Ya Shiga Aikin Sojan Najeriya /raujimetawiy/ A Ranar 10 Ga Disamba, 1962. Ya Halarci Kwalejojin Horon Soja Daban-Daban A Qasashe Kamar Indiya, Burtaniya, Da Amurka. Ya Fafata A Yaƙin Basasar Najeriya ( 1967–1970 ) Inda Ma Aka /raujimetawiy/ Harbe Shi A Qirji Kuma Ya Rayu Da Danyen Gishirin Harsashin A Jikinsa.
*
Gwarzon Dimka ( 1976 ): IBB Ya Shahara /raujimetawiy/ Sosai Lokacin Da Ya Tafi Da Kansa, Ba Tare Da Makami Ba, Ya Fuskanci Kwamandan Juyin Mulkin Da Aka Kashe Janar Murtala Mouhammad ( Wato Buka Suka Dimka ) A /raujimetawiy/ Gidan Rediyon Najeriya, Inda Ya Kwato Gidan Rediyon.
*
2 - Karbar Mulki (1985)
IBB Ya /raujimetawiy/ Kasance Babban Jigo A Kusan Dukkan Juyin Mulkin Da Aka Yi A Najeriya. Bayan Ya Taimaka Wajen Kafa Gwamnatin Janar Muhammadu Buhari A Shekarar 1983, IBB Ya Jagoranci Wani Juyin Mulki Na /raujimetawiy/ Cikin Gida A Ranar 27 Ga Agusta, 1985, Inda Ya Kuye ( Ham6arar Da ) Buhari Ya Zama Shugaban Kasa Na Soja Na Farko Daya Laqawa /raujimetawiy/ Kansa Laqabin "President".
*
3 - Manyan Abubuwan Da Suka Faru A Mulkinsa (1985–1993)
Gwamnatin IBB Ta Zo Da Canje-Canje Na /raujimetawiy/ Tarihi, Wadanda Suka Hada Da Nagari Da Kuma Qalubale:
*
Shirye-Shiryen Tattalin Arziki Da Cigaba
Shirin SAP ( Structural Adjustment Programme ) Bayan Ya Nemi Ra'ayin /raujimetawiy/ Jama'a Kan Ko Najeriya Ta Qarbi Lamunin IMF Kuma Aka Qi Amincewa, IBB Ya Fito Da Shirin SAP Don Farfado Da Tattalin Arziki. Wannan Shirin Ya Kawo Faduwar Darajar /raujimetawiy/ Naira Da Tsadar Rayuwa, Wanda Ya Janyo Zanga-Zanga.
*
Kishin Kasa Da Sabbin Hukumomi: Ya Kafa Manyan /raujimetawiy/ Hukumomi Kamar DFRRI ( Hanyoyin Karkara), MAMSER ( Wayar Da Kan Jama'a ), Da Federal Road Safety Corps ( FRSC ).
*
Maida /raujimetawiy/ Babban Birni Zuwa Abuja: A Lokacin Mulkinsa, A Ranar 12 A Disamba, 1991, Aka Kammala Maida /raujimetawiy/ Babban Birnin Najeriya A Hukumance Daga Legas Zuwa Abuja.
*
Kirkirar Jihohi: IBB Ne Ya Kirkiri Jihohi 11 Daban-Daban ( Kamar Su Katsina Da Akwa Ibom A 1987, Sai Su Jigawa, /raujimetawiy/ Kano, Kebbi, Taraba, Da Sauransu A 1991) Don Rarraba Iko.
*
Kalubale Da /raujimetawiy/ Tsauraran Matakai
Juyin Mulki: Gwamnatinsa Ta Fuskanci Yunkurin Juyin Mulki Guda Biyu; Na Mamman Vatsa (1985) Da Na Major Gideon Orkar (1990). An Kashe Dukkan Wadanda Aka Kama /raujimetawiy/ Da Laifin Jagorantar Juyin Mulkin.
*
Batun OIC: Shigar Ta Najeriya Cikin Qungiyar Kasashen Musulmi (OIC) Ya Janyo Dambarwa Tsakanin Musulmai /raujimetawiy/ Da Kiristoci A Kudancin Qasar.
*
4 - Rigimar Za6en June 12 Da Sauka Daga Mulki
Mafi Girman /raujimetawiy/ Abin Daya Ayyana Qarshen Mulkin IBB Shine Shirin Miqa Mulki Ga Farar Hula. Bayan Ya Dage Za6e Sau Da Dama ( Abin Da Ya Sa Aka Riga Akayi Masa Lakabi Da " Maradona " Saboda Iya /raujimetawiy/ Kaucewa Alqawura ), An Gudanar Da Zaben Shugaban Qasa A Ranar 12 Ga Yuni, 1993.
*
Za6en Na /raujimetawiy/ Ranar June 12, 1993, Wanda Ake Kyautata Zaton Moshood Abiola ( MKO ) Ne Ya Lashe Shi, Ana Kallonsa A Matsayin Za6e Mafi /raujimetawiy/ Gaskiya Da Adalci A Tarihin Najeriya.
*
Sai /raujimetawiy/ Dai Kuma, Kwatsam Janar Babangida Ya Soke Wannan Zabe Kafin A Bayyana Cikakken Sakamako. Wannan Soke Zabe Ya Jefa Najeriya Cikin Hargitsi, Yajin Aiki, Da Matsin Lamba Na Gida Da Na Qasashen /raujimetawiy/ Waje. Don Kwantar Da Tarzoma, IBB Ya Mika Mulki Ga Gwamnatin Riqon Kwarya Ta Shugaba Ernest Shonekan A Ranar 26 Ga Agusta, 1993, Ya Kuma Yi Murabus /raujimetawiy/ Daga Aikin Soja.
*
5 - Rayuwarsa Bayan Mulki
Bayan /raujimetawiy/ Ya Sauka, Ya Tare A Makeken Gidansa na Alfarma ( Hilltop Mansion ) Dake Minna. Ya Ci Gaba Da Kasancewa Uban Gida Ga Manyan 'Yan Siyasar Najeriya. Matarsa, /raujimetawiy/ Maryam Babangida ( Wadda Ta Shahara Da Shirin Better Life For Rural Women ) Ta Rasu A Shekarar 2009. A Cikin Shekarar 2025, IBB Ya Fitar Da Littafin Tarihin Rayuwarsa /raujimetawiy/ Mai Suna "A Journey In Service: An Autobiography".
marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment