THE BIOGRAPHY OF RABIU ALHAJI UMAR JIMETAWIY IN HAUSA LANGUAGE
TAQAITACCEN TARIHINA NI RAUJIMETAWIY
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاه والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
- CIKEKKEN SUNA NA, NA YANKA
Muhammadu Rabiu
- INKIYA / LAQABI
- Babangida
- Jimetawiy
*
- WAJEN HAIHUWA
An Haifeni A Garin Yola-Ta-Arewa ( Wanda Akafi Sani Da JIMETA ) A Anguwar Rumde.
*
- RANAR HAIHUWA
14 May 1999 Fri ( Na Asali Kenan )
15 May 1998 ( Wanda Nake Aiki Dashi Kenan, Bisa Kuskuren Da Aka Samu Wajen Yi Mini .....Card )
*
- WAJEN ZAMA DA ASALI
Mazaunin Yola-Ta-Arewa ( Jimeta ) Jihar Adamawa, Na Zamo Indigene By Birth.
ASALI
Qaramar Hukuman Auyo Ta Jihar Jigawa.
*
- KARATUN ADDINI
Nayi Karatun Al-qur'ani Mai Girma A Gaban Iyayena Da Mijin Yafendona ( Mal. Abdullahi Muhammad, Asali : Katsina, Qabila/Yare : Fulfulde/Fulatanci ) Harna Sauqe, Amma Bani Da Hadda, Nayi Iya Qoqarina Wajen Samun Hadda, Koda Kadan Ne, Amma Allah Mai Nufeni Da Hakan Ba.
Hadisi, Fiqihu Da Nahawu Nayishi Dai-Dai Gwargwado.
*
- KARATUN BOKO
Na Halarci
- Auyo Special Primary School
( 2005 - 2010 ) Auyo, Jigawa
- Gov't Day Junior Secondary School Auyo
( 2010 ) Auyo, Jigawa
- Gov't Day Junior Secondary School Rumde
( 2010 - 2013 ) Jimeta, Adamawa
- Gov't Day Senior Secondary School OLD G.R.A
( 2014 - 2016 ) Jimera, Adamawa
- Usmaniyya Arabic College Yola
( 2017 Reciting NECO Examination ) Jimera, Adamawa
- Adamawa State Polytechnic, Yola
( 2018, Amma Bai Kammalu Ba, Saboda Rashin Kudi Da Matallafi )
*
- SANA'A / AIKI
Ni Jinin Mahauta Ne, A Gefen Uba
Amma Ban Tashi Da Sana'ar Ba,
Ni Jinin Masunta Ne A Gefen Uwa, Amma Shima Ba Abunda Na Iya Akai.
Makanikanci
( Qarqashin Wani / Apprentice )
Leburanci
*
- ADDINI & AQIDAH ETC
- Musulunci, Addini Na.
- Annabi Muhammad SAW,
Annabi Na
- Al-qur'ani Da Hadisi,
Littafaina Tsarkaka.
- Dakin Ka'aba As-'shariffah,
Alqibla Ta.
- Malikiyyah, Mazhaba Ta.
- Ahlul Sunnah Wal Jama'ah - Ash'ariyyah,
Aqdah Ta Sunnah.
- Sufanci, Matafiya Ta / Hanya Ta.
- Qadiriyyah, Dariqa Ta.
*
- YARE, QABILA DA AL'ADA
Hausa
Ni Bahaushe Ne Gaba Da Baya, Uwa Da Uba, Bahaushen Adamawa
*
- 'YAN,UWA DANGI
Ni Na Kasance Ni Kadai Ne Mahaifiyata Ta Haifeni. Amma Ina Da Yayuna Da Qanne Wanda Muke Uba Daya Dasu.
01- Aliyu ( Adimin Gaso )
( Ranar Haihuwa : ....... )
Wajen Haihuwa Auyo, Jigawa
02 - Khadijah. R I P
Ranar Haihuwa : 02 - 02 - 1980
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
03 - Muhammadu Rabiu. R I P
Ranar Haihuwa : 17 - 01 - 1982
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
04 - Yahaya. R I P
Ranar Haihuwa : 12 - 12 - 1983
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
05 - Abdullahi. R I P
Ranar Haihuwa : 01 - 03 - 1985
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
06 - Abdullahi. R I P
Ranar Haihuwa : 22 - 03 - 1987
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
07 - Muhammadu Kabiru
( Kabiru Orto Engineer Sabuwar Auyo
Ranar Haihuwa : ......... 1991
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
08 - Muhammadu Rabiu ( Ni Kenan )
Ranar Haihuwa : 14 - 05 - 1999
Amma Ina Aiki Da 15 - 05 - 1998
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
09 - Khadijah ( Ummi )
Ranar Haihuwa : ....... 2001
Wajen Haihuwa : Jimeta, Adamawa
10 - Ibrahim ( Ibrahim Tela )
Ranar Haihuwa : 25 - 06 - 2003
Wajen Haihuwa : Nassarawa, Kano
11 - Hassan
Ranar Haihuwa : 28 - 03 - 2006
Wajen Haihuwa : Auyo, Jigawa
12 - Hussaina
Ranar Haihuwa : 28 - 03 - 2006
Wajen Haihuwa : Auyo, Jigawa
13 - Adamu ( Abbati )
Ranar Haihuwa : ...... 2008
Wajen Haihuwa : Auyo, Jigawa
14 - Lauratu. R I P
Ranar Haihuwa : ...... 2011
Wajen Haihuwa : Auyo, Jigawa
Wadannan Sune 'Yan,uwana Wanda Muke Uba Daya, Wadanda Suka Rasu, Da Mu Da Muke Raye, Mu Mu Goma-Sha-Hudu 14.
*
- HONORS NAME, NAWA
BPM
Beloved Prophet Muhd S.A.W
PAN
Proudly As Nigerian
PHM
Proudly Hausa Man
CON
Citizen Of Nigeria
MVM / MVMech
Motor Vehicle Mechanic
AUYO
An Haifi Babana A Garin Auyo
YOLA-N
An Haifeni A Yola North ( Jimeta )
*** *** *** *** *** *** *** ***
- -- - { MAHAIFI NA / BABANA } - -- --
- SUNANSA NA YANKA
Umar
- INKIYA / LAQABI
A Adamawa Anfi Saninsa Da Suna
Alhaji Umaru Hadejia ( Saboda Hadejia Tafi Sanuwa Akan Auyo, Bayan Haka Kuma Hakimin Auyo Hadejia Yake Bi.
A Auyo Kuma Anfi Saninsa Da Suna
( Alhajj Umaru Na-Jiimeta, Fawari Auyo )
*
- WAJEN HAIHUWA
An Haifeshi A Auyo, Kano British Nigeria
Wanda Yanzu Take Auyo Local Government Area Jigawa State.
*
- RANAR HAIHUWA
An Haifeshi A Ranar
13 - 04 - 1934 Kamar Yadda Ni 'Daya Daga Cikin 'Ya'yansa Na Gani A Cikin Dukkan Bayanansa.
*
- WAJEN ZAMA / ASALI
MahaifinaYa Zauna A Wajeje Da Dama, Tun Daga Neman Ilimin Muhammadiya, Da Kuma Neman Na Kai.
Ga Kadan Daga Ciki
- Mubi, Gongola, Now Adamawa
- Kwanan Yaji, Gombi, Adamawa
- Jimeta, Gongola Now, Adamawa
Sai Kuma
Auyo, Jigawa.
ASALI
Shi 'Dan Asalin Qaramar Hukumar Auyo Jihar Jigawa, Uwa Da Uba, Kaka Da Kakanaye
*
- KARATUN ADDINI & BOKO
Ya Fara Karantun Muhammadiyarsa A Gida Gaban Iyayensa, Kafin Daga Bisani Aka Kaishi Makarantun Allo, Wasu A Hadejia, Wasu A Nguru, Yobe.
Karatun Fiqhu Da Hadisi Dai-Dai Gwargwado.
KARATUN BOKO
Bai Halarci Makarantar Boko Ba.
*
SANA'A / AIKI
Asalin Sana'arsa Na Gado Wanda Ya Gada Shine Fawa, Mahauci Mai Sana'ar Sayar Da Nama.
Da Kuma Noma.
*
- ADDINI DA AQIDAH ETC
- Musulunci, Addininsa
- Annabi Muhammad SAW
Annabinsa
- Al-qur'ani Da Hadisi
Littatafansa Tsarkaka
- Ka'abah Ash-shariffah
Alqilbarsa
- Malikiyyah, Mazhabarsa
- Ahlul Sunnah Wal Jama'ah ( Ash-ariyyah )
Aqidarsa Ta Sunnah
- Sufanci, Matafiyyarsa
*
- YARE, QABILA DA AL'ADA
Hausa
Shi Bahaushe Ne, Gaba Da Baya, Uwa Da Uba, Bahaushen Auyo, Auyokawa
*
- 'YAN,UWA / DANGI
Mahaifina Iyayensa Sunayensu Ya Kasance
Mal. Muhammad Haruna
( Uba Mai Balangu )
Hajiya Khadijatu Ibrahim
( Iya Diye Fawari, Auyo )
YAN,UWANSA Sun Hada Da
- Aishatu
( Hajiya Iyalluwa, Dubantu, Auyo )
- Umar
( Mahaifinmu Kenan )
- Aminatu R I P
- Alhaji Haruna
( Haruna Gashi Fawari, Auyo )
- Abubakar
( Malam Garba Fawari, Auyo )
- Lauratu R I P
( Hajiya Uwaniyo Digitawa Auyo )
- Musa
( Alhaji Musa K U Auyo )
- Aishatu
( Hajiya Babarno, Maman Hassan Da Hussaina )
*
- IYAYENSA & ASALI DA QALIBA
Mahaifinsa Sunansa Mal. Muhammad Haruna ( Mal. Muhammad Uba Mai Balangu
Kuma Shi ( Kakanmu ) Haifeffen Garin Auyo Ne, Iyayensa Da Kakayensa, Zuriyar Gidan Mahauta.
Kuma Shi Qabilar Hausa Ne Iyaye Da Kakanaye Babu Mis Da Wani Qaliba/Yare.
Mahaifiyarsa Sunanta Khadijatu Ibrahim ( Iya Diye Fawari )
Kuma Ita Haifeffiyar Garin Auyo Ne Iyaye Da Kakanaye, Kuma Ita Zuriyar Mayaqa Ce, Wanda Har Yanzu Danginta Su Suke Riqe Da Sarautar Maqayaqin Auyo,
Kuma Ita 'Yar Qalibar Hausawa Ce Iyaye Da Kakanaye Babu Mis Da Wani Qabila/Yare.
*** *** *** *** *** **** *** *** ***
- - ( MAHAIFIYATA / MAMA NA ) - -
SUNANTA NA YANKA
Aminatu
INKIYA LAQABI
- Ta-Annabi
- Maman Amina ( Kasancewar 'Yar Qanwanta Kuma Takwararta Ta Girma A Hannunta Kafin A Haifeni.
*
- WAJEN HAIHUWA
An Haifi Mama Na, A Garwa, Jamhuriyar Kamaru ( Saboda Yaqin Basasan Najeriya BIAFARA Ya Kai Babanta Can Kamaru, Amma A Rubuce Muna Aiki Da Ngurore, Yola South )
- RANAR HAIHUWA & MUTUWA
An Haifeta A Ranar
15 - 09 - 1966
Ta Rasu A Ranar
22 - 11 - 2015 A Nan Yola North ( Jimeta ) Jihar Adamawa, An Binneta A Naqabartar Da Take Kusa Da Adamawa State Polytechnic Yola ( SPY )
Ta Rasu Tanada Shekara 49yrs
Tana Da 'Da/Yaro Guda 'Daya ( Ni Kenan )
Ubangiji Allah Ya Qara Jaddada Rahma A Gareta.
*
- WAJEN ZAMA & ASALI
Ita Ta Kasance Mazauniyyar Wajeje Uku
- Ngurore, Yola-Ta-Kudu Jihar Adamawa
- Yola-Ta-Arewa Jimeta, Jihar Adamawa
- Q/Hukumar Auyo, Jihar Jigawa
ASALI : Garin Ngurore Qaramar Hukumar Yola-Ta-Kudu Jihar Adamawa
*
- KARATUN ADDINI
Tayi Karantun Muhammadiya A Gaban Iyayenta Biyu, Al-qur'ani, Hadisi Da Fiqhu.
- KARATUN BOKO
Mahaifiyata Bata Ta6a Halartar Makarantar Boko Ba, Tun Daga Primary, Secondary Zuwa Jami'a, Duka Batayi Ba
*
- SANA'AH / AIKI
Mahaifiyata Tayi Sana'o'i Kamar Yadda Sauran Matan Aure Keyi,
AIKI : Matar Aure.
*
- ADDINI & AQIDAH ETC
- Musulunci - Addininta
- Annabi Muhammad S.A.W
Annabinta
- Al-qur'ani Da Hadisi
Littatafanta Tsarkaka
- Qa'aba Ash-shariffah
Alqiblarta
- Malikiyyah - Mazhabarta
- Alhul Sunnah Wal Jama'ah ( Ash-ariyyah )
Aqidarta Ta Sunnah
- Sufanci - Matafiyyarta.
*
- YARE, QABILA DA AL'ADA
Hausa
Ita Bahaushiya Ce, Gaba Da Baya, Uwa Da Uba, Bahaushiyar Adamawa Ko Bahaushiyar Kamaru
Amma Kakanayen-Kakanayenta Nasabarsu Yana Komawa Ga Kano
Gefen Uba : Baginawa, Warawa LGA Kano. Ko Kuma Audaga, Wudil LGA Kano
Gefen Uwa : Gaya LGA Kano
*
- 'YAN,UWA / DANGI
Mahaifiyata Tana Da 'Yar,uwa Wacce Suke Uwa 'Daya Uba 'Daya, Da Kuma 'Yan,uwa Wanda Suke Uba Daya ( Saboda Kakanmu Ya Gamu Da Jinya Tun Mamana Da Qanwarta Suna Yara, Hakan Tasa Ya Saki Kakarmu, Don Kada Ya Tauye Mata Haqqi ) Kuma Tana Da 'Yan,uwa Wanda Suke Uwa 'Daya.
* WANDA SUKE UBA 'DAYA
- Sa'adu R I P
( Malam Sa'adu, Ngurore )
- Ibrahim
( Malam Ibrahim, Mubi )
- Nuhu R I P
( Malam Nuhu, Ngurore )
- Muhamnad R I P
( Malam Muhd Mai Tauhidi Wuro Kuturo Jimeta, Kasuwan Katako Byepass )
- Jamila
( Malama Jamila, Gombe )
* WANDA SUKE UWA 'DAYA
- Aminatu R I P
( Ita Kanta Mamana )
Halimatus Sa'adiyyah R I P
( Qanwarta Wanda Na Zauna A Wajenta )
* WANDA SUKE UWA 'DAYA
- Yahaya
( Kawu Bala )
- Ramatu
( Uwani, Njabbore, Girei Adamawa )
- Abdul-Qadir
( Kawu Dan,azumi , Qanin Bala )
*
- IYAYENTA & ASALI DA QABILA
Mahaifinta Sunansa Malam Hamza Yunusa, Kuma Shi Kakanmu Haifeffen Baginawa, Warawa LGA Kano. Ko Kuma
Audaga, Wudil LGA Kano ( Saboda Shi Kakanmu Tun Yana Yaro Babanshi Ya Bar Yankin Kano, Ya Zo Guya6a, Kirfi LGA Bauchi Ya Zauna, Wanda Yanzu Dangi/Zuriya Suna Can Sun Zama Gari Guda, Hakan Tasa Ba Samu Cikekken Tabbaci Inda Aka Haifi Kakanmu Ba, Daga Bisani Kuma, Kakanmu Ya Baro Babanshi Malam Yunusa A Guya6a, Kirfi, Bauchi, Yazo Nan Ngurore Yayi Zamansa, Shima Ya Kafa Zuriya Guda )
Kuma Shi Jinin Masunta/Kwarawa Ne Da Noma,
Bahaushe Ne Gaba Da Baya, Uwa Da Uba, Bashida Da Mis Da Wani Qabila/Yaren.
Mahaifiyarta Ita Kuma Sunanta : Habibatu Muhamnad, Haifeffiyar Garin Ngurore Yola Ta Kudu Jihar Adamawa.
Mahaifinta Malam Muhammadu Mai Almajirai Ngurore Da Mahaifiyarta Khadijah ( Ladi ) Asalin Iyayensu 'Yan Gaya LGA Kano Ne, Amma Suma Iyayensu Sun Zauna A Zaranda, Toro LGA Bauchi, Zuriya Tana Can Gari Guda, Shima Daga Bisa Ya Baro Zaranda Ya Zauna A Ngurore, Yaci Gaba Da Karantar Da Alqur'ani Har Allah Ya Qar6i Rayuwarsa.
Wasu Daga Cikin 'Ya'yansa Mata Suna Aure A Zarandan, Auren Dangi, 'Daya Tana Jauro Gotel Gombe, 'Yar Autansu Tana Cikin Ngurore A Gidan Da 'Ya'yanta Da Jikoki, Kakarmu Kuma Itane Allah Ya Kawota Aure Jimeta.
Su Dukansu 'Yan Qabilar Hausa Ne.
Hausawa Ne Gaba Da Baya Uwa Da Uba, Babu Mis Da Wani Qabila/Yare
Wannan Dalili Yasa A Cikin Honors Names Nawa Kuke Ganin Nake Rubuta PHM ( Ma'ana Proudly Hausa Man ) Saboda Iyayena Gefen Uwa Da Uba Dukkansu Hausawa Ne Iyayensu Da Kakanayensu
*
Bari In Tsaya Muku Anan, Domin Kawo Tarihin Mutum Abune Dogo Da Tsayi.
Nayi Wannan Rubutun Ne, Domin Tabbatarwa Da Wani, Cewa Nasan Tarihin Iyayena, Da Kuma Daga Ina Suke, Qabilarsu/Yarensu.
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Abu Maryam Muhamnad Rabiu Jimetawiy Bini Alhajj Umar al-Auyowiy Bini Muhammad Bini Haruna
( Wanda Akafi Sani Da )
@raujimetawiy
. Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment