002 TAQAITACCEN BAYANI AKAN SALLAN JUMA'AH
kashi na 2
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشراف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidah Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Insha Allahu Cikin Wannan Rubutun Zamu 'Dan 'Dauko Taqaitaccen Bayani /raujimetawiy/ Dangane Da Sallan Juma'ah Daga Littafin Fiqhun Mazhabar Malikiyyah, Sanannen Littafin Da Kowa Yasanshi, Wato ISHMAWIY Wanda AL-SHEIKH AL-IMAM AL-ALIMU AL-ALAMATU ABDUL-BARIYI AL-ASHMAWIY RUFA'IYUN Allah Yaji Qansa Da Rahma Wallafa.
**** **** **** **** **** ****
A Gurguje
Kafin In Shiga Cikin Littafin Ishmawiy, Akwai Hadisin Daya Kamata In Rubuta Tun A Kashi Na 1
Dangane Da Falalar Ranar Juma'ah
Gashi Nan Kamar Haka
قال سيدى الشيخ عبد القادر الجيلاني
Sayyadil Shaikh Abdul-Qadir Jilani ( Rahimahullahu Ta'alah, Jagoran Dariqar Tamu Dariqar Qadiriyyah ) Yace
وأخبرنا أبو نصر عن والده بإسناد عن ثابت البنانى عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال
Abu Nasri Ya Bamu Labari Shi Kuma Daga Mahaifinsa Tareda Isnadi, /raujimetawiy/ Daga Sabitul Bunaniy Daga Anas 'Dan Malik Allah Ya Qara Masa Yarda, Daga Annabi Tsira Da Amincin Allah Su Qara Tabbata A Gareshi Shi Yace :
" إن لله تعالى ستمائة ألف عتيق من النار فى كل يوم وليلة الجمعة ويوم الجمعة أربع وعشرون ساعة فى كل ساعة ستمائة ألف عتيق من النار كلهم قد استوجبوا النار "
" Lalle Allah SWT Yanada Wadanda Yake 'Yantawa Su Dubu 'Dari Shida Daga Shiga Wuta, A Kowanne Rana ( Ta Juma'ah ) Da Daren Juma'ah, A Ranar Ranar Juma'ah Kuma Akwai Sa'o'i Guda Ashirin Da Hudu, A Kowanne Sa'a Yana 'Yanta Dubu Dari Hudu Daga Shiga Wuta, Wanda Dukkansu Sun Cancanci Shiga Wuta "
Idan Mukayi /raujimetawiy/ Duba Da Wadannan Hadisai, Ya Ishemu Mu Gane Ranar Juma'ah Ba Rana Bace Da Zamu Dinga Wasa Da Ita, Kamata Yayi Muna Dagewa Da Yawaita Karatun Al-qur'ani, Hailala, Salati Da Istigfari Etc
Yanzu Kuma Cikin Ikon Allah Bari Mu Shiga Cikin Littafin Ishmawiy
Malam Mai Littafi Ya Ce
بابُُ صَلاَةِ الْجُمُعَةِ
BABI ZAI KARANTAR DAMU SALLAN JUMA'AH
وَصلاَةِ الُجُمُعَةِ فَرْضُُ عَلَى الأَعْيَانِ
Ita /raujimetawiy/ Sallan Juma'ah Farillah Ce Abisa Dole ( Ga Wanda Ta Hau Kanshi )
وَلَهَا شُرّوطُ وُجُوبِِ وَأَرْكَانُ وَآدَابُ وَأَعذَارُ تُبِيحُ التَّخَلُّفِ عَنْهَا،
Tana Da Sharuda Na Wajibi ( Ita Sallar Juma'an, Sannan Kuma Tanada ) Rukunoni, Da Ladubai, Da Kuma /raujimetawiy/ Uzurai Wacce Take Halatta A Bar Zuwa ( Sallan Juma'an )
*
فَأَمَّا شُرُوطُ وُجُوبِهَا فَسَبْعَةُُ :
Amma Sharudanta Na Wajibi Guda Bakwai /raujimetawiy/ Ne
الإِسْلاَمُ
وَالْبُلُوغُ
وَالْعَقْلُ
وَالذُّكُورِيَّةِ
وَالحُرِّيَّةِ
والْإِقَامَةُ
والصِّحَّةِ
- MUSULUNCI
Sallan Juma'ah /raujimetawiy/ Baya Halatta Akan Wanda Ba Musulmi Ba ( Kamar Bayahude, Kirista Da Mai Bin Addinin Gargajiya ) Sai Akan /raujimetawiy/ Musulmi Yake Wajaba.
- BALAGA
Hakanan Sallan Juma'an Tana Wajaba Akan /raujimetawiy/ Mutum Baligi, Bata Wajaba Akan Yaro Qarami Wanda Bai Balaga Ba, Wanda Bai Kai Matakin Yin Mafarki Ba, /raujimetawiy/ Amma Anada Buqatan Zuwa Dasu Domin Su Taso Da Abin.
- HANKALI
Sallan Juma'ah Bata Wajaba Akan Mutumin Da Yake Mara Hankali Wato Mahaukaci, Amma Akwai Irin Mutanen Da Suna Nan 2sim-2sim Zakagansu Da Tsabtansu Da Komai, Basa /raujimetawiy/ Yin Duka Basa Fitar Da Yawu Da Wasu Abubuwa Na Qazanta, Irin Wadannan Abun Zuwa Dasu Ne, Amma Mutum Mai Cikekken Hankali Dolen-Dolen Ne Akanshi Zuwa Sallan /raujimetawiy/ Juma'ah, Inde Babu Uzurai Kar6a66u.
- MAZAKUTA
Sallan Juma'ah Dole Akan Mutum Namiji, Domin Idan Ance Mazakuta Ana Nufin /raujimetawiy/ Mutum Namiji Cikekke Lafiyeyye Mai Azzakari, Ba Mata-Maza Ba,
Amma Su Mata Bai Wajabta Akansu Zuwa /raujimetawiy/ Sallan Juma'ah Ba.
- 'YANCI
Mutum Wanda Yake 'Da 'Yantacce Baligi Ba Bawa Ba, Zuwa Sallan Juma'ah /raujimetawiy/ Dole Ne Akanshi, Amma Mutum Wanda Yake Bawa Ko Da Baligi Ne, Indai Shugabansa Ya Hanashi Zuwa Sallan Juma'ah, Toh Ya Zauna A Gida Yayi Azahar Insa Shiyafi Masa Alkhairi /raujimetawiy/ Da Akan Yaje Sallan Juma'an, Shiyasa Akace Sallan Juma'ah Bai Wajabta Akan Bawa Ba, Saboda Ana Samun Mutum Bawa Musulmi, Amma Shugabansa /raujimetawiy/ Ba Musulmi Ba.
- MAZAUNI / IQAMATU
Mazaunin Cikin Gari, Zuwa Sallan Juma'ah Dole Ne Akanshi, Amma Matafiyi /raujimetawiy/ Baya Hawa Akanshi, Amma Koda Kana Halin Tafiya Ne, Sai Kazo Wucewa Ta Wani Gari, Tana Tada Iqama Za'a Shiga Sallan Juma'ah, Min Babi Aula Ya Kamata Ka Tsaya Kayi Sallan, /raujimetawiy/ Ko Kazo Ka Tararda Sauran Irin Minti Biyar Zuwa Goma Nanma Ya Kamata Ka Tsaya Kayi Sallanka, Balle Ma Yanzu Zamanin Motoci Da Jirage, Delay Minti Goma Nawa Yake.
- LAFIYA
Sallan Juma'ah Dole Ne Akan Mutumin Da Yake Da Lafiya, Amma Wanda /raujimetawiy/ Yake Kwance Ba Lafiya Rashin Lafiya Mai Tsanani Shi An Sauqaqa A Gareshi, Ba Sai Yaje Ba, Kamar Yadda Bayaninsa Zaizo Anan Gaba.
Bari Mu Tsaya Anan Da Izinin Allah, Kada Mu Tsawaita Rubutu, Saboda Shi /raujimetawiy/ Kanshi Babin Bamai Tsayi Bane. Zamu Taqaitawa A Hankali A Hankali.
Insha Allahu Kuma A Kashi Na 3 Kuma Sai Mu Tashi A Inda Malam Yake Cewa :
وأما أركانها فخمسة
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
01 Safar 1448 Hijrah
16 July 2026 Miladiyya
Ranar Alhamis
3pm
marubuci
@raujimetawiy
Rabiu Alhaji Umar Jimetawiy,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment