SILSILATA TA DARIQAR QADIRIYYAH
DARIQATUL QADIRIYYAH
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
A Gurguje
Da Yawan Mutane In Nace Mu Ni 'Dan Dariqa Ne Suna Mamaki, Wasu Ma Cewa Sukeyi Qarya Ne, Toh Domin /raubabangida/ Share Muku Tantama Ga Jerin Silsilata Ta Dariqa.
001 Ni Rabiu Alhaji Umar Babangida
( Na Kar6a A Wajen )
002 Sheikh Abdul-Jabbar N Kabara
( Mal. Abdul-Jabbar Dai Da Kuka Sani, Wane Yake Tsare Hannun Gwamnatin Jihar Kano, Shi Kuma Ya Kar6a Wajen )
003 Sheikh Muh'd Nasiru Kabara
004 Sheikh Muhammad Al-Mujtaba
005 Sheikh Ni'imatullahi Al-Gaith
006 Sh. Mustapha Ma'ul'ainain
007 Sh. Muhammad Al-Fadeel
008 Sh. Muhammad Al-Mamin
009 Sh. Muhammad Addali6
010 Sh. Akyar Ahl
011 Sh. Mukthar Aljin
012 Sh. Muhammad Al-Habib
013 Sh. Dalib A'al
014 Sh. Muhammad Al-Kabir
015 Sh. Yahayal Sageer
016 Sh. Ahmad Zaruq
017 Sh. Yahya Al-Hadrami
018 Sh. Aliyul Wafa'a
019 Sh. Dawud Al-Bakali
020 Sh. Ibnu Ada'a Al-Iskandari
021 Sh. Abul Abbas Al-Mursi
022 Sh. Abul Hassan Ash-Shazali
023 Sh. Abdulsalam Ibnu Mashish
024 Sh. Muhammad Al-Hatimi
025 Sh. Abu Najib Suhruwardi
026 Sh. Aliyu Ibnu Al-hity
027 Sh. Abdul-Qadir Bin Musa Jilani
( Shugaban Dariqar Qadiriyyah, Shi Kuma Ya Kar6a Wajen )
028 Sh. Abu Wafa'a Kakisu
029 Sh. Nurul-Arifin Ash-Shanbaki
030 Sh. Junaidu Assufiy
031 Sh. Assidiq
032 Sh. Ma'arufi Bn Karrabuz Al-kirki
033 Sayyid Habibul Ajami
034 Sayyid Hassanul Basariy
035 Imam Aliyu Bn Abi-Dalib R.T.A
036 Muhammad Rasulullah S.A.W
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Toh Anan Wani Zai Iya Cewa A Ina Laqqana/Talqini Ya Samo Asali A Addini.
Mai /raubabangida/ Buqatan Sani Ga Hadisai Guda Biyu A Qasa Kamar Haka.
فأن عليا كرم الله وجهه سأل النبي صلى الله عليه وسلّم يا رسول الله دلنى اقرب طريق إلى الله وأسهلها على عبده وأفضلها عنده تعالى
An Kar6o Daga Sayyiduna Aliyu Karamallahu Wajhahu, Ya Tambayi Annabi S.A.W ( Ya Ce ) Ya! Ma'aikin Allah Ka Shiryar Dani Hanya ( Dariqa ) Mafi Kusanci Zuwa Ga Allah Kuma Mafi Sauqinta Ga Bayinsa, Kuma Mafifici A Wajensa Madaukakin Sarki,
فقال النبي صلى الله عليه وسلم عليك بمداومة ذكر الله سرا وهو جهرة
Sai Annabi S.A.W Yace, Bana Horeka Da Dawwama Da Ambaton Allah ( Zikiri ) A Asirce Ko A Bayyane,
فقال علي كل الناس ذكرون فخصنى بشيىء
Sai Sayyiduna Aliyu Yace Ai ( In Haka Ne ) Dukkan Mutane Zakirai Ne ( Masu /raubabangida/ Ambaton Allah ) Ka Ke6anceni Da Wani Abu, Wanda Zan Na Fada,
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : أفصل ما قلته أنا والنبيون من قبل " لا إله إلا الله "
Sai Manzon Allah S.A.W Yace : Mafificin Abunda Na Fada Da Annabawan Da Suka Gabata ( Shine ) " La'ilaha Illallah "
ولو أن السموات والأضين فى كفة ولااله إلا الله فى كفة لرجحتهم
Da Za'a Sanya Sammai Da Qassai A Ma'auni/Mizani A Sanya La'ilaha Illallahu A Ma'auni Da ( La'ilaha Illallahu ) Ya Rinjayesu,
ولا تقوم القيامة وعلى وجه الأرض من يقول لا إله إلا الله
Alqiyama Bazata Tsaya Ba, Face A Bayan Qasa Sai An Rasa Wanda Zaice La'ilaha Illallahu,
ثم قال علي فيف اذكر
Sannan Sai Sayyiduna Aliyu Yace ( Wa Annabi ) Yaya Zanyi Zikirin,
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : غمض عينك واسمع منى لا إله إلا الله ثلاث مرات، ثم قلها ثلاث وأنا أسمع
ثم فقل ذالك يرفع الصوت
Sai Manzon Allah S.A.W Yace : Ka Rufe Idonka Ka Saurara Daga Gareni La'ilaha Illallahu Sau Uku, Sannan Kaima Ka Fada Sau Uku Nima Ina Mai Sauraronka
Sannan Ya Fadi Haka Yana Mai Daukaka Murya.
رواه الطبراني والبزر بإسناد حسن
'Dabarani Da Bazzaru Ne Suka Rawaito Shi Da Isnadi Hasanun ( Mai Kyau )
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Dangane Da Yin Talqinin Dariqa Ga Mutane Da Yawa, Ga Madogarar Sufaye.
ففن يعلى بن سداد قال حدثنى أبى سداد بن أوس رضي الله عنه
عصامة بن الصامت حاضر يصدفه قال
An Kar6o Daga Ya'alah 'Dan Saddadu Yace Abi Saddadu 'Dan Aus R.T.A Ya Bamu Labari
Usamatu 'Dan Samit Yana Wajen, Yace :
كنا عند رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال : هل فيكم غريب؟ يعنى من أهل الكتاب، فقلنا لا يا رسول الله
Mun Kasance A Wajen Manzon Allah S.A.W Sai ( Annabi ) Yace Shin A Cikinku Akwai Baqo? Abunda Yake Nufi Ahlul Kitabi ( Shin /raubabangida/ Akwai Yahudawa Ko Nasara, Ko Babu ) Sai Muka Ce A'a Ya! Ma'aikin Allah
فأمر يغلق الباب فقال : ارفعوا أيديكم وقولوا ( لا اله إلا الله )
Sai ( Annabi ) Yayi Umarni Da Rufe Qofa, ( Bayan /raubabangida/ An Rufe Qofa, Sai Ya Ce Dasu ) Ku 'Daga Hannayenku Ku Ce ( La'ilaha Illallah )
ثم قال صلى الله عليه وسلم " الحمد لله، اللهم إنك بعثنى هذه الكلمة، وأمرتنى بها، ووعدتنى عليها الجنة، وإنك لا تخلف الميعاد "
Sannan Sai Manzon Allah S.A.W Yace " Godiya Ta Tabbata Ga Allah, Allahumma Ya! Allah Kai Ka Tasheni/Aikeni Da Wannan Kalmar, Kuma Kayi Mini Alqawari Gareta Da Aljanna ( Wato Wanda Yayi Imani Da La'ilaha Illallah Ya Yarda Da Ita, Yayi Aiki /raubabangida/ Akan Qalallahu Qala Rasulu Zai Shiga Aljannah ) Lalle Kai ( Ya! Allah ) Baka Sa6a Alqawari "
ثم قال صلى الله عليه وسلم : ألا أبشرو فإن الله قد غفر لكم
Sannan Sai Manzon Allah S.A.W Yace : Ku Saurara، Ina Yi Muku Albishir Lalle Allah Duk Ya Gafarta Muku ( Toh Amma Hakan, Ba Wai Yana Nufin Duk Wanda Ya Kar6i Dariqa An Gafarta Masa, A'a Saika Zama /raubabangida/ Akan Qalallahu Qala Rasulu, Kuma Ita Kanta Dariqa Ba Dole Bane A Musulunci, Yin Dariqa A Musulunci Mustahabi Ne Ba Dole Ba )
أخرجه الإمام أحمد والطبرانى والبزار ورجاله موثوقون كما فى مجمع زوائد ج ١ - ص ١٩
Imamu Ahmad, Dabarani Da Bazzaru Ne Suka Fitar ( Rawaita ) Mazajensa Kuma Mausiqai Ne
Kamar Yadda Yake A Cikin
Majma'u Zawa'id
Juz'i Na Daya
Shafi Na 19
Wannan Shine A Gurguje
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment