TAQAITACCEN TARIHIN RAYUWAR NNAMDI AZIKWE DA MULKINSA
LATE RT. HON. DR. NMANDI BENJAMIN AZIKWE a.k.a
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
بسم الله الرحمن الرحيم
والصلاة والسلام على أشرف أنبياء سيدنا ومولانا محمد النبي، وعلى أزواجه أمهات المؤمنين وذريته وأهل بيته الطاهرين وصحابته الأكرمين وعلينا معهم أجمعين
@@@@ @@@@ @@@@ @@@@
Ina Qara Godewa Allah Bisa Kasantuwar Musulunci Addinina, Annabi Muhammad SAW Annabi Na, Al-qur'ani Da Hadisi Littatafaina Tsarkaka, Ka'aba Ash-sharifah Alqiblata, Malikiyyah Mazhabata, Ash'ariyyah Aqidata Ta Sunnah, Sufanci Matafiyata, Qadiriyyah Dariqata, Hausa Qabilata.
Aslm
Ya 'Yan,uwana Musulmai Maza Da Mata Manya Da Qanana Da Fatan Kowa Yana Qoshin Lafiya, Marasa Lafiyanmu Na Gida Da Na Asibiti Ubangiji Allah Ya Basu Lafiya, Masu Lafiya Kuma Allah Ya Qara Musu Lafiya, Iyayenmu Da Kakanayenmu Yayyunmu Da Qannanmu, Da Suka Rigamu Gidan Gaskiya Ubangiji Allah Yaji Qansu Yayi Musu Rahma, Muma In Tamu Tazo Allah Ya Sa Mu Cika Da Imani.
Ameen Summa Ameen
*** *** *** *** *** *** *** *** ***
Dr. Nnamdi Azikwe ( Wanda Akafi Sani Da "Zik" Ko "Zik Of Africa ) Yana 'Daya Daga Cikin Manyan Ginshikan Da Suka Fafutuki Tareda Samar Da 'Yancin Kan Najeriya. Shine /raubabangida/ Shugaban Qasa Na Farko Na Najeriya Kuma Kwararren 'Dan Jarida, Dan Siyasa, Kuma Masani.
1 - Farkon Rayuwa Da Karatu
Haihuwa: An Haife Shi A Ranar 16 Ga Nuwamba, 1904 A Garin Zungeru Dake Jihar Niger Ta Yanzu. Iyayensa Biyu ’Yan Qabilar Inyamurai (Igbo) Ne Daga Garin Onitsha, Amma Saboda Mahaifinsa Yana /raubabangida/ Aikin Gwamnati A Arewa, Zik Ya Girma Yana Jin Harshen Hausa, Yarbanci, Da Kuma Ibonci.( Igbo )
Karatu : Yayi Karatunsa Na Farko A Najeriya /raubabangida/ Kafin Ya Tsallaka Qasar Amurka A Shekarar 1925. A Can Ya Halarci Jami'o'i Da Dama Ciki Harda Lincoln University Da University Of Pennsylvania, Inda Ya Qaranci Kimiyyar Siyasa ( Political Science ), Ilimin Zamantakewa ( Sociology ), Da /raubabangida/ Aikin Jarida.
2 - Fafutukar Neman ’Yancin Kai
Bayan Dawowarsa Afirka, Zik Yayi Amfani /raubabangida/ Da Aikin Jarida A Matsayin Maqami Na Yaki Da Mulkin Mallaka Na Turawa.
Ya Kafa Kamfanonin Jaridu Da Dama, Inda Mafi Shahara Itace West African Pilot Da Aka Kafa A Shekarar 1937. Wannan Jarida Ta Zaburar /raubabangida/ Da ’Yan Najeriya Da Mutanen Afirka Wajen Neman 'Yancinsu.
A fagen Siyasa, Ya Kasance Daya Daga /raubabangida/ Cikin Wadanda Suka Kafa Jam'iyyar NCNC ( National Council Of Nigeria And The Cameroons) A Shekarar 1944, Kuma Shine Ya Shugabance Ta Bayan Rasuwar Herbert Macaulay.
3 - Tarihin Mulkinsa
Dr. Nnamdi Azikiwe Ya Rike Manyan Muqaman /raubabangida/ Mulki Na Tarihi A Najeriya Kamar Haka:
Firimiyan Yankin Gabas ( 1954–1959 ): Ya Jagoranci Gwamnatin Yankin Gabashin Najeriya, Inda Ya Mayar Da Hankali Kan Bunkasa Ilimi ( Shine Ya Kafa Jami'ar University Of Nigeria, Nsukka ) Da /raubabangida/ Kuma Tattalin Arziki.
Gwamna Janar Na Najeriya ( 1960–1963 ): Lokacin Da Najeriya Ta Sami Yancin Kai A Shekarar 1960, Shine /raubabangida/ Aka Nada A Matsayin Gwamna Janar ( wakilin Sarauniyar Ingila ), Yayin Da Sir Abubakar Tafawa Balewa Ya Kasance Firayim Minista.
Shugaban Kasa Na Farko ( 1963–1966 ): Lokacin Da Najeriya Ta Zama Jamhuriya A Shekarar 1963, Azikiwe /raubabangida/ Ya Zama Shugaban Qasa Na Farko Na Najeriya. Wannan Muqami Na Shugaban Qasa A Wancan Lokacin Na Tsarin Mulkin Barlaman ( Parliamentary System ) Ya Kasance Na Kujerar Daraja Da Wakilci ( Ceremonial President ), Yayin Da Cikakken Ikon Gudanar /raubabangida/ Da Gwamnati Da Tsaro Yake Hannun Firayim Minista Tafawa Balewa.
Mulkinsa Yazo Qarshe A Ranar 15 Ga Janairu, 1966, Sakamakon Juyin Mulkin Soja Na Farko Da Akayi A Najeriya, /raubabangida/ Wanda Ya Kawo Qarshen Jamhuriya Ta Farko.
4 - Salon Siyasa Da Rasuwarsa
Azikiwe Yayi Amfani Da Salon Siyasa Na Hada Kan Qasa ( Nationalism ) Da Kuma Yarjejeniya. Koda /raubabangida/ Aka Dawo Siyasar Jamhuriya Ta Biyu ( 1979–1983 ), Ya Tsaya Takarar Shugaban Qasa A Qarqashin Jam'iyyar NPP ( Nigerian People's Party ). Ya Kasance Mai Son Sulhu /raubabangida/ Da Kaucewa Rigingimu Da Zasu Iya Tarfa Qasar Tsakiya.
Bayan Ya Janye Daga Harkokin Siyasa Na Tsawon Lokaci, Dr. Nnamdi /raubabangida/ Azikiwe Ya Rasu A Ranar 11 Ga Mayu, 1996 A Asibitin Koyarwa Na Jami'ar Najeriya Dake Enugu, Yana Da Shekaru 91 A Duniya. Har Yau Ana Kallonsa A Matsayin "Mahaifin Kasar Najeriya" ( Father Of The Nation ), Kuma Hotonsa /raubabangida/ Yana Kan Takardar Kudi Ta N500.
@raubabangida
Rabiu Alhaji Umar Babangida,
BPM PAN PHM, CON, MVM, AUYO, YOLA-N
Comments
Post a Comment